Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

yanayin da na cire komai a raina nake iyakacin bakin kokarina wajen mayar da hankali a karatuna, sai dai ba wani fahimta nake sosai ba. Na dai yi sa'a zan iya karatu da rubutu. Na gama fahimtar ni din basirata a wajen kirkirar abin ado ne, misali idan na samu kan mace mai gashi zan b'ata lokaci na yarfa mata kitson da kowa sai ya ce "wow". Haka kuma duk gunjin gashi sai na kitse shi, zana adon lalle kuwa tamkar wanda aka bu'de mini ido. To yanzu da nake sake koyon kwalliyar da ake ya yi, ban jima da fara koyo ba amma har hannuna ya fara fa'da wa. Dan haka na daina takura wa kaina sai dai ina ta kokari dan na samu na ci jarabawar kammala sakandire. Ranar asabar tun safe nake ta murnar zan je gidan Nazira, tunda muka zo duniya bamu ta'ba rabuwa na lokaci mai yawa haka ba. Mutum uku kawai na yarda zan yi wa kitso, duk masu zuwa lalle kuwa ha'kuri nake basu, sai d'aya da take unguwar Nazira, layinsu d'aya domin Naziran ce ta turo mini ita. Dan haka na saka mata lallen a gurguje na barta da nufin ta same ni gidan Naziran na yi mata kitso a can. Da murna nake komai domin Allah ya sani ina son Nazira, ina samun farin-ciki idan ina tare da ita. Har Malaminmu na tarar yana dakon iso wa ta, ga abinci an shirya mini tamkar wata babbar bak'uwa ta mussaman. Spaghetti ce da miyar kifi, saboda ita ce favorite dina. Ga kuma zobo ya sha ha'di an fasa masa k'ank'ara, gefe kuma babbar kula ce shake da pure water da aka jefa masa k'ank'ara yini guda aka yi mini tanadinsa. Da farin-ciki yake taya amaryarsa marabta ta. Ta rungume ni tana k'walla da mitar ashe zan iya yin watsi da ita na tsawon wannan lokacin? Da dariya na ce "Babanmu ne ya ce "Ba zan dinga yi miki sintiri a gida ba". Malam Yunus ya ce "Ba wani sintiri idan kin so ma ki tattaro kayanki ni bazan gaza ba". Na yi dariya ina fa'din "Na gode da karamci, Allah ya sanya alheri". Ya fice ya barmu tare da cewa "Ameen Asiya". Tunda muka zauna hira muke yi, ba a gama wani zancen ba za'a sake, a kama wani. Na bata labarin yadda muka yi da Dada akan Malam Nata'ala. Ta dinga dariya tana tintsira wa tamkar ta samu tab'i. K'wallar dariya a idonta ta ce "Lallai ma tsohuwar nan, ke ce za'a bawa wannan tsohon?" Na taya ta dariya tare da cewa "To ba namiji ba ne? Kuma ai ta ga ya dace da ni ne, tunda ana kore mini duk wanda ya zo da niyyar aure na". Ta yi shiru ta ce "Kawai lokacin yin auren ne da saura, amma ba dai Alaramma ba." Muka shiga hirar duniya, muka ci abinci, muna santi a fili na ce "Na ji da'din ganinki Addah Nazi, Allah ya kara miki kwanciyar hankali, ya kawo zuri'a dayyiba". Ta ce "Ameen Yabi! Yanzu addu'ata mafi yawa taki ce Àllah ya kawo miki miji na gari". Na yi shiru. Ta ce"Baki amsa ba?". Idona ya cika dam da ruwa na ce "Baban Tsakiya ya lashi takobin duk wanda ya zo sai ya b'ata ni, ya fa'di munanan dabi'una kin ga kuwa aure ai zai yi mini wuya tunda kanin mahaifina ne yake fa'din munanan kalami a kaina." Ta yi shiru sai kuma ta ce ",Ba abin da yafi k'arfin addu'a Yabi! Fa'da kawai yake yi ba zai yi hakan ba". Na hade fuska na ce "bana son haka, wanne irin zance kike yi? Kema kin san gaskiya, zai yi abin da yafi haka in dai Alle Badamasi ne" Dariya ta subuce wa Nazira ainun, tana yi tana nuna ni da yatsa tare da ce wa "Ho Yabi". Tsawon lokaci muna hira tana ta bani labarin aure. Na dube ta na ce "Ya ya maganar da ake fa'da na ha'duwar farko, ya take kaya wa?" Ta galla mini harara ta nuna kanta ta ce "Ni kika yi wa wannan tambayar?" Na k'yal-k'yale da dariya ina fa'din "Adda Nazi manya. Yo wa nake da ita da zan tambaya, kawai fa'da mini Malama". Ta leka ta ga ko Iki na jinmu, sai ta ga game take yi a wayarta a falo, mu kuma muna uwar daki. Ta ce "Kawo kunnenki ki ji". Da rawar jiki na mika mata, ai kuwa ta gantsara mini cizo. Na saki kara a ki'dime. Ita kuma ta ci magani tana fa'din "Maganin mai son jin almarin da bai shafe shi ba, maganin mai son jin abin da Allah ya sakaye shi, maganin mai son ya ji sirrin da Annabi ya tsine wa mai bayyana shi". Ai kuwa na fara hawaye ina shesshe ka. Nan da nan ta hau shafa kafa'data tana fa'din "Yi ha'kuri mana Yabina a hankali fa na yi miki, menene zaki zubar da hawayenki?" Na zum'bura baki ina fa'din "Mun bata gaskiya! Kuma dan kin zama babba ce ai dai kinsan fa'da na." Ta yi murmushi ta ce "Ni ban girma ba." Muka yi dariya gaba'daya. Sai lokacin wacce na bari a gida da k'unshi, ta biyo ni, akan na yi mata kitso. Muka fara, yayin da Ikilima ta hau wanke wanke ita kuma Nazira ta hau gyara wajen da muka yi dabdala. Da zan taho ta hado ni da kayan kwalliya masu yawa har Ina fa'din ta kwashe mini kayan ai. Da sabuwar doguwar riga da ko sata bata yi ba, da sabon takalmi. Na kalleta na ce "Ki rage kayan sun yi yawa Adda Nazi". Ta ce "Idan ina da fiye da hakan baki zan yi Yabi". Na jijjiga kai na kasa cewa komai na yi gaba na bar Iki tana dauko mini. Muna tafe ni da Iklima muna hirarmu na ce "Idan kin gaji dai, ki bani na karbi kayan." Ta ce "zan iya Adda Yabi". Muna tafe wani Alhaji sai binmu yake a hankali a cikin dankareriyar motarsa. Duk hon dinsa ban yarda mun tsaya ba. Har muka je gida, bai fasa ba. Muka shige gida, ya yi parking. Dai-dai lokacin Bulkachuwa ya danno kai. Na shige na bar Iki tana lekensa. Ba wani jima wa ta shigo da sauri tana fa'din "Adda Yabi wai ke ya biyo. Yaya Bulkachuwa ya fa'da masa babu maganar wani a kanki, ya bashi ku'di, ya kuma aiko shi wajen ki". Tana rufe baki sai ko ya shigo, daga tsaye ya gaida Gwaggo da Inna yana fa'din "Asiya Toro zo mana". Na yi kamar bazan kula shi ba, sai da Gwaggo ta ce "Yabi wai Yayanki ba magana yake yi miki ba ne? Ni fa bana son wannan wula'kancin na ki". Na mike ina fa'din "Shi ai Tijjani kayan haushinsa yawa ne da shi." Ya yi dariya ya ce "Ashe duk yadda na yi ba'kin jini a wajen Jabir akan ki ban wanke laifina na baya ba?" Muka dan fita wajen k'ofa. Ya sassauta ya ce "Kin ga Àllah ya dubi takaicin da aka cusa miki Asiya Toro! Kin zargo babban kifi. Wannan mutumin son ki yake yi da aure, kwamshinan harkokin addini ne na jahar nan, sannan babban dan kasuwa

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161