Chapter 111
Chapter 111
ta ce "Sanin kina da daraja ne a wajen mijinta ya sanya ta washe ki, ban da haka kina matar wani, ta shafa miki lafiya mana, tunda tasan a musulunci mace bata auren miji biyu. Da a ce Nasiba ce ke, ai da tuni Maijidda ta kusa zama gawa, domin ba abin da zai hana mijinta fitowa neman auren ki, tunda har gobe yana son ki". Da hanzari na ce "Allah suturi bukui. Ai sai yanzu na fahimci tun asali ba wani sonsa na yi ba, shak'uwa ce da soyayyar k'uruciya. Yanzu da na saba mua'amalantar barden namiji irin Baban 2, mai zan yi da dan karamin sauron mijinta? Su je can su k'arata har abada ba zai sake burge ni ba." Dadi ya kama Adda Nazira ta fashe da dariya ta ce "Ina komawa zan fa'dawa Baban su Abid tun yanzu Yabi ta fara fa'din madallah da auren Yaya Bulkachuwa". Kunya ta dan rufar mini na ce "eh ki fa'da masa". Haka aka yi bikin aka gama lafiya. Baba Maryo da kanta wani gani gani take yi mini da ban san dalilinsa ba. Ba dama ta ga Babah ta yi mini wani abu sai ta ce "Ba hakan aka barki ba, da aka tashi kame mata Tijjani har da uwarsa aka ha'da ban da hakan irin wannan gudun zuciyrta da kike yi har ina? Yara na son zuwa wajen uwarsu kin kanekane kin rikesu kina fa'din ta je ta yi hidimar jama'a. Ke kuma kin zama mai raino'. A lokacin da take fa'din haka ina tsaye, wata irin fargaba ta kama ni, domin na hango kishina ke cinta ba ka'dan ba. Na laluba ko na yi mata laifi ne, amma ban ga na yi mata komai ba. Wata'kila zamana lafiya a gidan aurena ne yake mintsinarsu. Tunda da safen nan ma sai da Baban Tsakiya da na kasuwa suka tambaye ni, wai na fa'di irin zaman da nake yi, idan babu dama sai a ha'kura ramar da nake yi ta yi yawa. A dakin Dada a gaban kuma Babah. Na kalle su ina mamakin manufarsu. Domin ni dai jefi jefi Tijjani na matsa mini na kira na gaishe su, ina kuma yi tunda tisa ni yake yi a gaba. Amma su kam tunda na yi aure ba wanda ya ta'ba kirana ya ji lafiyata, ko ya ji ya ya na ke? Baban Marina ne kawai yake mini hakan a cikinsu. Amma abin mamaki sune da fa'din wai na rame tsabar sun saka mini ido suna kuma adawar sun jimu k'alau ni da Tijjani. Na bu'de baki cikin nutsuwa na ce "Satin jiya na yaye yara, na yi fama da zazzabi a dalilin haka. Sannan ni ba ni da matsalar komai ina cikin rufin asiri mai yawa. Allah ya saka muku da alheri bisa bawa Tijjani aurena da kuka yi. Bana fatan sauyi ko a aljannah ne". Baban Kasuwa ya ce "To ya isa zabiya! Mun ji, mun ga ne ba sai kin zarce da rashin kunyar da kika saba ba." Baban Tsakiya kuwa ya ce "Na tashi na basu waje sun sallame ni, dama sun nuna kulawa ne dan sun gane muna zaginsu a bayan idonsu akan basa kula da sha'anin yan k'ofarmu. Amma zan fara yi musu rashin kunya da iyashege." Na fito zan shige Babah da take bawa tagwaye koko da kosai. Suka fashe da kuka wannan karon kukan har da Hanif. Murya babu amo ta ce "Zo ki zauna, yunwa suke ji". Na dawo na zauna shi ke nan kuma suka yi shiru. Suka ci gaba da cin abincinsu. Muna haka Tijjani ya shigo dan haka na sid'ad'a na fice tunda suna ganinsa. Washagari muka koma, daga ni har Tijjani so muke mu tafi da yaranmu. Tunda sun yi sati biyu. Amma kowa ya kasa fa'dawa Babah da ta daure fuska bayan ta fahimci take takenmu. Sai da zamu tafi ta biyo ni har zaure tana fa'din "Zan dawo muku da su, amma sai kin warware kin murje. Kina ganin dai yadda ramar ta ki ta janyo cece kuce. Ki kwantar da hankalinki, nan da wata ma zasu dawo." Kunya ta kama ni, na shagwabe fuska na cuna baki na ce "Ni fa Babah ban damu da su ba, su zauna ma gaba'daya a wajen ki, ba ni da matsalar komai". Ina rufe baki Tijjani ya yi maza ya ce "Bilhiillazi karya take yi miki Babah." Ta gwale shi da ce wa "ko k'arya take yi, ai ta saya, kai da baka da kunya ai ka bu'de ka nuna na baku yaranku". Nan da nan ya yi shiru, ni kuma na yi dariya tare da yi masa gwalo. Da hakan muka rabu, ta koma cikin gida, mu kuma muka tafi. ✍️. *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *Tuni labarin ya fara nisa, yana kuma da dadi da darasi*. *08089965176* *07084653262* Da wuri muka shiga Bauchi. Ya taimake ni muka gyara gidan, muka yi girikin abin da zamu ci. Dai da yamma ya fita. Kwanci tashi asarar mai rai, kwanaki suka yi ta shud'ewa har muka samu sati da dawowa daga Toro. Daga ni har Tijjani bama jin da'din rashin yaranmu a tare da mu. Kewarsu muke yi sosai. Amma dukkanmu kowa ya bar abin a ransa, mun bisu da addu'a. Muna cikin hakan ba zato sai aka kira Tijjani tare da albishir din filinsa kamfanin sadarwa yake bu'kata. Zasu karbi hayar wajen na shekaru uku. Idan wa'adin ya cika, wata'kila su siya gaba'daya ma, matu'kar mutane sun karbi sabon kamfanin da hannu biyu. Farincikin da muke ciki ba ka'dan ba ne. Mussaman da Tijjani ya tabbatar mini ku'din ya isa ya sayi gidan da muke ciki da kuma mota golf da ake yin sufuri da ita. Cikin Ikon Allah kuwa bayan cike cike, da kai komo suka tura masa ku'dinsa cas ta asusunsa na banki. Hassada da bak'in-cikin a wajen masu filaye a wajen tamkar su jefa shi wuta. Hatta Alh Auta bai iya boye ba'kin cikin da ya ji ba.duk da Tijjani ya bashi kyautar dubu dari a cikin ku'din amma hakan bai sa ya gode ya ha'diye ba'kin cikinsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161