Chapter 97
Chapter 97
ya bushe k'amas. Na saka hannuna na murtsike idanuwana da tunanin gizo yake yi mini, tare da fatan ace sak'e sak'en zuciyata ne da wasi-wasi irin na shaid'an. Amma ina zahiri nake ganinsu. Tijjani zaune akan baranda yayin da Rafi'a take kan cinyoyinsa da manyan mazaunanta. Ta kwanta luf a kirjinsa, shi kuma idonsa na kan k'irjinta yana kallonsu. A zahiri iya abin da na gani ke nan amma zuciyata sai ta shiga wassafo mini cewar yanzu ma suka sanya tufafinsu. Na ki'dima ainun, amma na kasa yin kwakkwaran motsi, na tsaya cak ina kallonsu tamkar mutum mutumi K'arar faduwar wayata ne ya ankarar da shi. Ya d'ago da fuskarsa ai yana ganina ya yi wani irin zabura ya wancakalar da ita, ta hantsilo ta fa'do kan guiwowinta. A matu'kar rude ya k'araso gare ni. Ya rasa mai zai ce, sai kawai ya zube a gabana guiwa bibbiyu. Ya ru'ko hannuna na kalle shi na ce "Tijjani gizo idona yake yi, ko mafarki nake yi?". A ki'dime ya ce "Zan so a ce mafarkin kike yi Asiya". Daidai lokacin Rafi'a ta zo ta shige sum sum tamkar k'wai ya fashe mata a ciki. Na dinga jin tukukin ba'kin ciki da tashin hankali. Amma kuma idona a soye duk yadda nake son hawaye ya zubo mini abu ya ci tura. Na sunkuya na d'auki waya ta na k'wace hannuna na yi d'akina ina jin jiri na katantanwa da ni. Kai tsaye na hau cire rigar cikina domin zafin da nake ji a zuciyata har jikina yake kutso wa. Zufa sai yanko mini take yi. Na cire komai na d'aura zani. Na zauna amma ban daina jin zafin jiki ba. Na fita har lokacin yana durk'ushe a inda na bar shi. Na dauki botiki na nufi rijiya. Da azama ya tare ni, ya ce " Bana hana ki jan ruwa da kan ki ba?". Ban ce komai ba na matsa gefe ya janyo mini ruwan. Ya kinkima ya kai mini band'akin. Na shiga na yi wanka. Amma dana fito ina goge jikina da tawul, zufar na sake keto mini. Na dauki rigar barci marar nauyi na saka, bayan na saka gajeran wando ta ciki. Na d'aure kaina da dan kwali mai taushi. Kicin na fa'da na hau girki, ina yi ina hailala. Gaba'daya jina nake yi tamkar ba ni ba. Na yi matu'kar kad'uwa da abin da na ga ni a cikin gidan aurena. Ban san falalar kuka ba sai a yau, domin gaba'daya hawayen ya k'i zuba. Shi kuma ya takure, a gefe tamkar ka ce k'yat ya zura a guje. Cikin lokaci k'alilan nadama mai tsananin gaske ta bayyana a dukkan jikinsa. Ya kasa sukuni, da alamu kunya ce ta hana shi sukuni. Tunda ni dai ban bu'de baki na ce masa komai ba. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *Dandano* *DAGA Littafin BAK'AR TA'ADA* *NA SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR HALIN YAU DA SABO DA KAZA* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GICSrs9TfxG1Q6FUXiu1Qg *Ina tallata muku make up artist din Guduyo* *Aisha Lame mai kayan kwalliyar yan gayu*. *Jakadiyar oriflame, duk wani nauyin kayan oriflame tana kawo su cikin farashi mai sau'ki*. *Ba iya kayan kwalliya masu daraja ba, ita din GWANAR sarrafa pop corn ce(gugguru), ni shaida ce ta hakika*. *Sannan tana da spices kasaitatu. Masu mayar da girki ya zama na alfarma* *07036662633*. *INA SANAR MUKU ZAMU BUGA LITTAFIN KANA NAKA ZUWA HARD COPY*. *MASU BU'KATAR MALLAKAR NASU SU TUNTU'BE NI, KO SU TUNTU'BI MARUBUCIYA JANAFTY*. *BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*. Na gama komai na kai falo kamar yadda na saba. Shi kuma ya zama mutum mutumi. Na fito na ce "Ga abinci ko sai ka dawo daga masallaci?" Ya zuba mini ido ya rasa abin fa'da. Ya tashi ya ce "Da sauran lokaci ai." Na zuba mana kamar yadda na I'm. Amma gaba'daya mun kasa ci sai faman juya shi muke yi. Gara ni na ci loma biyu na ji mak'oshina ya cushe na ajiye. Shi kuwa yama kasa kai wa ba'kin nasa. Ya gaji ya kalle ni ya ce Dan Allah Yabi ki yi ha'kuri, ki yafe mini". Ba ja in ja na ce "To". Daga haka kuma ban sake ce wa komai ba. Ya yi maganganu na ban ha'kuri da nuna nadama masu yawa amma ban ko kalle shi ba. Aka kira sallah ban yarda na bu'de baki mun yi magana kamar yadda yake fata. Ya yi alwala ya tafi masallaci. Har muka haramar kwanciya ban bu'de baki na ce k'ala ba. Duk jaye-jayen maganarsa kuwa. Da muka kwanta ya fara lalubata ban hana shi ba, amma ko kwakkwaran motsi ban yi ba. Ya yi duk abin da zai yi dan na motsa ko na mayar masa martani amma tamkar an shuka dusa. Ya gaji ya koma ya kwanta yana fa'din "Innalillahi wa ilaihir rajiun" . Ya ru'ko ni da rawar murya ya ce "Yabi ki yiwa Allah, ki bu'de baki mu yi magana". Yana rufe baki na ce"To". "Asiya ki yi ha'kuri, ki yafe mini, dan Allah, dan Annabi, ki yafe mini". Na yi shiru. Ya sake ce wa Bansan me ya same ni ba Yabi. Dan Allah ki mini uzziri ki yi ha'kuri ki gafar ce ni". Nan ma na ce "To". Ya yi iya ban hakuri, amma ban yarda na ce komai ba. Da gari ya waye da wuri ya dawo daga masallaci ya hau hidimar gyaran gida. Ya yi abin karya wa. Har d'aki ya kawo mini amma ina ci sau daya ban sake kai wa na biyu ba, na ce na koshi. Ya yi shiru ya rasa yadda zai yi. Bai fita ko ina ba. Yini aka yi ana zuwa lalle amma ban iya yiwa ko mutum daya ba. Sai ha'kuri nake basu tare da uzzirin cewa bani da lafiya ne. Hakan da ya ga ni ya sake rib'anya tashin hankalinsa. Domin yasan yadda nake matu'kar son sana'ata. Bana son abin da zai hana ni yin lalle ko kitso. Amma da bakina nake sallamar mutane yasan al'amarin da yake zuciyata ba k'ank'ani ba ne. Kwanaki uku muna cikin wannan halin. Daga ni har shi, mun yi matu'kar rame wa tunda bama iya cin abinci ga rashin nutsuwar zuciya. Ya yi juyin duniya mu yi magana na ki, domin har yau ban yarda na yi masa korafi ba. Komai kuma zai ce sai na amsa da "To". Kullum safiya zan gaishe shi, zan kuma amsa sallamar sa idan ya shigo. Daga hakan kuma bazan sake yarda na ce komai ba. Rashin yin lallen har zuwa lokacin ya fara ta'bamu tunda shi ma baya iya fita, ko ya fitan ma baya nisan kiwo zai dawo. Ranar da aka yi kwanaki biyar da faruwar al'amarin, ya zauna ya bani hakuri tamkar yawun bakinsa zai k'afe. Har da k'wallarsa. Amma ban ce komai ba, sai ma murmushi mai ciwo da na yi na ce masa "To me
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161