Chapter 102
Chapter 102
ciki na wata daya har da sati biyu. Duk yadda nake jin rashin kwarin jiki amma sosai na yi murna. Ni da Tijjani ban san wanda yafi murna da zumudi ba. Muna isa gida na dauki waya na k'ira layin Gwaggo. Tana dauka ta ce "Yabi ya jikin dai?" Da azarbabi na ce "Hmmm Gwaggo ashe duk wannan wahalar da murkususun da nake yi ciki ne da ni!" Ta yi shiru, sai kuma ta ce "Ni kika kira ki fa'da wa hakan Yabi? Wacce irin marar kunya ce ke haka?" Na yi sakare domin ni ban ga wani laifin ba. Ita ce uwata bani da wacce ta fita a halin yanzu. Ita ce mafi kusa na tattauna dukkan farin-cikina da ita. Zan yi kokarin na boye fa'da mata damuwar da nake ciki domin na yi amanna damuwata zata tsayar mata da dukkan farin-cikinta ne. Na sanyaya murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri. Ina cikin murna ne. Kin san kwanaki a gidan nan aka fa'da mini ce wa Tijjani ya gama zubar da yaransa a titi ni bazan haihu ba. Sannan kuma ke da bakinki kika ce sai na haihu da ki zo ki ga muhallina". Ta sassauta ta ce "To ba sai ki bari na fahimta ba, ko na ji a bakin yayarku ko kuma Nazira". Na ce "To sake yin hakuri Gwaggo ai yanzu na fahimta. Idan zan yi ta biyu, bazan fa'da miki ba. Sai dai kawai a ce miki Yabi ta haihu" Ta ja tsaki ta ce "Allah dai ya baki lafiya" tare da kashe wayarta. Tijjani da yake gefe yana ta faman murmushi ya ce "Burinmu ya cika. Yanzu fa'da mini sunan nawa?" Na yi dariya na ce "Ai sai na haihu". Ya girgiza kai ya ce "Kin ce da zarar kin samu ciki zaki fa'da mini fa". Na ce "Haka ne". Ya ce "To fa'da mini na ji". Na murmusa ka'dan na ce "Abbanta". Ya kwashe da dariya ya ce "Wanne irin suna ne wannan? Duk yadda kika kwadaita mini zakuwar samuwar cikin a iya wannan sunan zan k'are? Abbanta kuma. Wace ce?" Na jingina a jikin kujerar na ce "Bebin mana." Ya sake fa'dada dariyarsa ya ce "To idan namiji ne fa?" Na ce "Ai kuwa sunan da zan fa'da maka mai wuyar samu ne indai namiji na haifo tunda na fa'da maka mai kama da kai nake so". Dadi ya kama shi ya ce "Allah ka kula mini da Asiya. Ka taya ni son ta, ka shiga dukkan kasafinta. Duk al'amarin da zai dunfaro ta, Ubangiji kada ka bar ta da iyawar ta. Na ce "Ameen" a gajiye domin wai maganar da na yi har na gaji na fara haki. Haka nake kwana da yini babu lafiya. Duk dare bama barci kwana muke muna fama. Domin gaba'daya ni dai babu sau'ki. Kwana nake magogo. Haka kuma Tijjani baya runtsawa. Tausa yake yi mini, da fifita idan babu wuta. Tin a lokacin muka fahimci zama iyaye ba karamin al'amari ba ne. Duk yadda na zaku na samu ciki sai da na fara sare wa. Murnata ta fara koma wa ciki dan tsananin wahalar da nake ciki. Al'amura suka fara yi mana tsauri a dalilin ku'di ya fara yanke mana. Haka da safe idan ya tallafa mini na yi wanka, ya shafe mini jiki da man zafi zai fita ya dan yawata. Idan an yi sa'a ya samu aiki ya samo ku'di, zai siyo mini 'dan abin kwadayi. Watarana kuma hakan zai dawo. Baya kuma nisan kiwo, ko ya fita hankalinsa na kai na. Sai na samu sau'ki, sai kuma jikin ya sake rikice wa. Na fara gazawa. Rannan Baban Marina da ya zo duba ni, ya ga yadda na koma gaba'daya na yi yaushi. Ya bashi umarnin ya kai ni gida, ko shima ya d'an huta. Bai musa ba kuwa washagari da hantsi ya dauke ni da jakar kayana ya kai ni gida. Har da siya mini su maltina da madara da indomi da zan dan yi kwanaki ina ci. Wanda na tabbatar ya ha'da da bashi. Da k'yar na shiga muka gaisa da Dada wacce bayyana farincikin da ta yi a dalilin samuwar cikin bata lokaci ne. Ya kira Ikilima ta ri'ke ni zuwa cikin gida. Na sani kuma dan ya mutunta iyayenmu ne ya sanya bai ri'ke ni da kansa ba. Yadda Tijjani ya ha'do ni da shirgi da maganganuwana. Sai ka rantse har cikin zuciyarsa yake nufin na zo na yi goyon ciki a gida. Kwana na biyu a gida na fara samun sau'ki tamkar a gidana ciwon yake. Domin ina barci, da safe kuma ina shan koko na ci dumame. Sannan Gwaggo da kanta take daddana mini jikina. Har gasa mini jiki take yi da tawul. Ga shi duk abubuwan da nake son ci na gargajiya ina samu. Kwatsam ranar da na yi kwana uku sai ga shi ya ce shi ya gaji da rashina sai dai mu koma gida. Na tubure akan sai na ji k'warin jikina. Shima ya kafe. Kuma wai ni ce zan ce ina son komawa gidana. Nan da nan na rantse akan bazan fa'da ba. Ya jijjiga kai ya ce "Shike nan tunda babu taimako da fahimta a tsakaninmu. Ni zan fa'da wa Baban akan na gaji ina son ki koma dakinki. Dama kunya da nauyinsa ne suka sanya na kawo ki." Da yamma ya dawo akan na taimake shi mu koma gida. Ya kasa fa'dawa Baban zai tafi da ni. Na ce "Ni dai na fi son zaman nan". Nan da nan ya tunzura ya ce "Saboda bani da ku'di ko Asiya?" Na kalle shi a razane. Ya ce "Haka ne mana. Inba hakan ba wace ce ta taba zuwa gida dan bata da lafiya a gidan nan?" Na ce "Ubaida bata dawo ba?" Da hanzari ya ce "Amma duk jinyar da ta yi da ciki ai bata dawo ba. Sai da ta haihu. Ke kuwa ai ba haihuwa kika yi ba. Idan ba gazawa ta aka ga ni ba. Mene ne zai sa ayi mini wannan umarnin?" Na sake kallonsa cikin tu'ajjibi na ce "Baban Marina kake fa'dawa hakan ko kuwa wa?" A tunzure ya ce "Asiya na ke fa'dawa saboda ita ce zata ce masa ta samu sau'ki." Idona ya ciko da hawayen takaici na ce "To". Daga hakan na k'ulle bakina ban ce masa komai ba. Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Ya ce "Ya muke ciki?" Ko kallonsa ban yi ba. Ya gama zamansa ban sake kula shi ba. Da daddare ma ya dawo, ban yarda na kula shi ba. Domin idan akwai abin da yake b'ata mini rai da shi idan muna magana ya dinga sako babun shi ne. Na kuma lura idan ban taka masa birki ba, ba wanye wa k'alau zamu yi ba. Tunda yana nema ya mayar da ita sara. Washagari sassafe sai ga Babah ta Bulkachuwa ta dira a gidan. Ina daga daki na ji suna gaisawa da Baba. Ya ce " Hauwa kamar ba kwanaki ka'dan da suka shud'e kika zo duba y'arki ba. Me ya sake dawo da ke kuma yanzu? Mata kuna da son sabgar yawo. Ta ce "Ba hakan ba ne Yaya. Shi ne ya mini waya wai jikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161