Skip to content

Chapter 106

Chapter 106

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

soyayyarsa na kekketa ni fiye da ko wanne lokaci. Wata'kila kuma kasancewar sa uban y'ay'an da nake jin kaunarsu har a cikin b'argona yana da alak'a da sake jin ninkin soyayyar sa. Na murmusa na masa ameen a zuciyata. Ya mik'awa Yaya Ummi wanda yake hannunsa ya karbi d'aya yaron da ya kammala sha yanzu a hannun malamar. Cikin nutsuwa ta kalle shi ta ce "Mr Tijjani kada Kaka ta rikita ka." Ta shiga fado masa muhimmancin fara bawa yaro nonon uwa a farkon awanninsa a duniya. Ta sake ce wa "Tunda mu musulmai ne mun yi sa'a kuma muna d'abbaka sunnar manzo. Da zarar uwa ko uba sun tauna dabino sun guntsawa yaronsu a baki bayan sun yi Bismillah. Ba abin da zai fi dace wa da lafiyarsa illah wannan nono da mutanan jiya suka tafi a fahimtar ce wa cuta ce. Babban sirrika ne da Ubangiji ya zuba a ciki". Ya gyada kai cike da gamsuwa. Ya yi mata godiya sosai tare da bata ha'kuri akan maganganun Dada. Ta murmusa ta ce "Ai babu komai nima kafin na fito sai da muka haura da tawa kakar. Sai ana yi musu uzziri. Da zarar sun kai shekarun girma irin haka, sai an sake yin hakuri da sha'aninsu ana mayar da komai zasu ce a matsayin girma ne. Shi kuwa tsufa ba k'aramin nauyi ne da shi ba. Domin Allah da kansa sai da ya yi ta jan kunnenmu a cikin kura'aninsa mai girma akan idan iyayenmu suka kai shekarun girma kada mu fa'da musu munanan kalamai, komai zasu yi mana, kada mu ce musu uffan, balle a yi sa'insa da su". Ya sake ce wa "Haka ne. Na gode sosai". ✍️. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633*. *Masu fitarwa bazance muku komai ba. Kowa ya yi mai kyau kansa.* *Wacce ta karanta mini labarin nan bata biya ba tabbas ina binta bashi*. *Masu jiran na kammala su had'a mini document, kada ku yi hakan, na ro'ke ki a littafaina na baya amma still baku ji ba.* *Bana son a had'a mini document* *Bana son a had'a mini document* *Wacce kuwa ta hada na kai ta k'ara wajen Ubangiji*. Ta tattara kayanta ta fice ta bamu waje. Ya matso ya zauna a gefen gadon da nake kai. Ya zuba mini ido tare da ce wa "Sannu little. Ban zaci zaki iya haihuwa da kanki ba. Mussaman da na ga Ubaida da Nasiba masu garin jiki sun gaza haihuwar da kansu". A hankali na ce "Haihuwa ikon Allah ke sawa a yi ta lafiya ban da haka kam da iyayenmu basu taramu da yawa haka ba". Ummi da take gefe ta murmusa ta ce "Yabi an je kusa da lahira an dawo." Ya ce "Ummi ai ni da kaina na tausaya mata, haihuwar yara biyu tashi guda, sannan ki gansu manya tamkar ba tagwaye ba? Wani ikon Allah bamu yi zaton yan biyu ba ne, Ubangiji ya boye su ko sikanin din da aka yi bai nuna ba." "Ikon Allah ya fi ga hakan ai" Yaya Ummi ta fa'da a hankali. Ya sake kallona ya ce "Asiya kin ga yaran nan kuwa, kina ganin yadda Ubangiji ya mana kyautar da ba kowa yake yiwa irinta tashi guda ba?" A hankali na ce "Ai ban gansu ba, ba'a bani na ga ni ba, kunya kuma ta hana ni na tambaya". Ya yi hanzarin sake matso wa kusa da ni tare da d'ora mini yaron akan cinya a hankali. Cikin nutsuwa yake ce wa "kalle shi da kyau Asiyata. Kalli ki ga yadda suke kama da ni. Kalle shi, ki masa addu'a, ki kuma gode wa Ubangiji bisa d'inbin baiwar da ya yi mana". Na zuba wa yaron ido. Ina son ga ne kammannin da Tijjani yake fa'da. Amma na kasa tantance wa, domin ni kam bana ga ne kammannin jarirai. Na tsananta kallonsa, ina jin wata irin nutsuwa da kaunar yaron na shigata sannu a hankali. Na saka hannu ina duba yatsun hannunsa da na tabbatar irin nawa ne. A hankali Tijjani ya ce "Yusuf ke nan (Baban Bulkachuwa) ki masa addu'a, shi ne babban". A fili na furta "Allah ya raya shi, ya saka shi cikin bayinsa da yake sonsu. Allah ya masa kyakkawar rayuwa. Allah ya bashi basira da azanci, ya saukaka al'amarinsa, ya kuma ba shi kyakkawan rabo a lahira". "Ameen ameen" Tijjani yake fa'da cikin wani irin yanayi. Da azama ya ce "Ummilolo kawo shi, shi ma ya samu tabararakin addu'ar uwa." Ya dauke wanda ya kira da Yusuf. Yaya Ummi ta d'ora mini na hannunta ta koma gefe. Ya gyara rikon na hannunsa ya ce "Kin ga yadda suke kama da juna ko? Tagwaye ne masu kama da juna kwabo da kwabo(Identical twins)". Na gasgata shi, domin ni kaina idan aka jere mini su bazan iya banbanta su ba a yanzu. Na zuba masa ido tamkar yadda na yiwa d'anuwan sa. A hankali Tijjani ya ce "Muhammad Sani ne wannan(Baban Marina)." Haka kawai na ji tausayi yaron ya shige ni. Kaunar sa ta shiga mamayata. Cikin rauni na ce "Allah ya raya shi, ya sanya shi cikin bayinsa da yake kar'ba daga garesu. Allah ya saukaka al'amarinsa, ya kimsa masa ilimi da azancin sarrafa harshe. Ubangiji ya sa ya dace da kyakkawan rabo a lahira". Shi da Yaya Ummi suna ta fa'din "ameen". Ya sake kusantowa gare ni. Ya ha'demu gaba'daya ya rungume. A fili ya ce "Allah ga ahalina, ka so su, ka taya ni kula da al'amarinsu, ka tsarkake mini su. Ubangiji ka basu kariyar da ni ba zan iya basu ba. Ka zame mini jagoran wajen sauke nauyinsu da ka d'ora mini. Allah ka bawa uwarsu lafiya da juriyar raino da tarbiya. Ina ro'kon ka saukar da albarka a cikin gidanmu da rayuwarmu gaba'daya". Ya dinga kaiwa kuncina da goshina sumba. Jaririn da yake hannuna ya fara mutsu mutsu da k'ananun kuka tabbacin an takure shi. Da azama Tijjani ya janye daga gare ni. Yaya Ummi ta matso da nufin d'aukar yaron. Ya ce "Ashe ba ki fita rarashin Dada ba Ummilolo? Da kika ga sun fice ai sai ke ma ki bi bayansu ki bamu waje". Ta ce "ka gama borin kunyar ka dai". Ya matse ya ce "To ba daukarsa zaki yi ba. Taimaka wa zaki yi ya sha. Da alamu yunwa yake ji sai tsotson hannu yake yi". A hankali ya na ce "A a ai ya d'an sha d'azu. Zafi Wallahi!. Cikin tausayi ya ce "Ki yi ha'kuri, zafin na d'an lokaci ne k'alilan". Kan dole na yarda na ba shi. Shi kuwa yaro sai zuka yake yi babu jinkiri da alamu sai yafi d'an uwansa tsotso. Ana hakan na hannunsa shi ma ya fara nasa sukur sukur din. Ya mike ya saba shi a kafa'da, yana dan juyawa. Daidai nan su Babah suka shigo. Ta kalle shi ta ce "Bawa Ummi shi, ka zo ka tafi. Ka zo ka yi kane kane ko kunyar iyayen pka

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161