Chapter 5
Chapter 5
lebe ba sai Tijjani kyakkawan gaske. Wani irin mutum mai saurin fishi, da k'arfin zuciya. Amma mai saurin saukowa da mantuwa. Illarsa d'aya manemin mata ne, a yadda a ke fa'da. Na shaida kuma duk wata budurwa ballagaza a Toro to kuwa budurwarsa ce ko kuma suna d'asa wa, shiyasa kowa yake jan kunnen y'arsa a kansa, barin ma ni, kullum ne sai Gwaggo ta ce kada na sake na bashi fuskar da zamu dinga doguwar magana. Gaba'daya dabi'unsa na tantiran yan-iska ne, sannan k'azami ne, baya damuwa da yin wanki sai kayansa sun k'are. A hakan kuma shashan y'anmata suke sonsa, ko da yake baya yarda ya fita da dattin sosai, yana wanke wa ya jira su bushe, guga ce sai ya samu ku'di, sai ya bayar da kayan ma a wanko a gogo masa, amma da wahalar gaske ya yi guga da kansa. Duk yadda Dada take kulafacinsa, matu'kar ya shigo muna nan sai sun haura da shi, domin yafi kowa takalarmu da magana, yana yi yana lumshe ido ta yadda zai sure zuciyoyinmu. A hakan ya yi nasarar yin wuf da zuciyar Nasiba. Idan Dada ta ga yana sakin maganganu ko lumshe ido a gabanmu ta dinga bagarar da shi, ko ta tsiri aiken sa, ko kuma ta ce mu je ta sallame mu, duk yadda take sonsa to bata son doguwar magana a tsakaninmu, kazalika kuma bata son a k'i gaishe shi. Burgar da yake yiwa mata ya sanya har yanzu bai bar dauke dauke ba, komai ya gani zai dauka ya siyar ya kashe wa budurwa ku'di. Amma iya kayan Dada yake dauka. A duk sadda take yi masa fa'da kuma zai waske ya ce bashi ba ne, ko kuma sharri ta yi masa, haka kuma sai ya d'auke mata wuta, har sai ta nemo shi ta bashi ha'kuri. Bayan soyayyar da take yi masa, yana sake samun alfarma a wajenta saboda sunan SHEHU ne da shi. Kullum bakin ta akan ya nutsu ne, ya bar shiririta ya kawo matar aure, tunda ga Yaya Salisu nan da yake sa'an sa tuni ya yi aurensa har matar ta haihu, amma shi ko maganar aure baya yi saboda sharholiya da mutuwar zuciya. Duk da k'arancin shekaruna ina tambayar kaina ko waye zai iya d'aukar y'arsa ya bawa Bulkachuwa aurenta? Tabbas sai idan yarinyar ta kasance shasha ce irinsa. Na tabbatar mahaifiyar Nasiba ba zata ta'ba bari a bashi ita ba, domin kuwa kowa nasa yake so, bare idan maganar gaskiya za'a yi bai cancanci a bashi ba, domin bashi da sana'a, gashi manemin mata, shiyasa kowa yake masa kallon shasha. A duk sadda Dada take yi masa fa'dan shigar da yake yi ta gajerun wanduna yana yawo a gari babu kunya, ko tara suma ya gegareta daga gefe, ko kuma wani zubin ya sauya launinta bayan ya mayar da ita cibiri cibiri. "Akan kunnena na sha jin tana ce wa "Saboda bamu da mutunci a idonka shiyasa kake iya zuwa gabana a hakan ko kuma gaban kawunanka". Ba jin nauyi yake ce wa "Tunda nake yin sallah a hakan, ai kin ga bai zama aibu dan kun gan ni a hakan ba. Domin Ubangijina ma a hakan yake gani na, kin takura mini fa Tsohuwa" Nan da nan ta zabura ta ce "Imaninika ai a makogaro yake shi yasa kake hakan, amma da za'a jarrabe ka da son wata yarinyar ba zaka yarda ka je mata a hakan ba. Alfarmar Shehu sai ka samu wacce sonta zai hanaka yin wannan shakiyancin. Tunda ka ki daina wa saboda Allah da Ma'aikinsa." Dariyar iyashege yake yi ya ce "Ni da nake da y'anmata kamar jamfa a Jos suna bina dan na so su, shine har son wata zai canja ni? Lah! Ba dai Bulkachuwa ba". Da wani kuma a Cikinmu ko a cikin samarin gidan matu'kar ba Yaya Anwar ba ne zai saka musu baki, a take Dada zata nuna wa mutum shine bare a tsakaninsu. Tana kuma sake kambaba shi da kawar masa da kai saboda alfarmar mai sunansa ne, domin ko ta yi masa sababi, sai ta yi ta tuba tana kamun kafa da mai asalin sunan akan a saka mata jikanta cikin shirayayyu. Hatta shi kansa dariya take bashi akan yadda take tuba idan ta saki harshe a kansa. Amma wani ikon Allah jarumi ne na gaske. Idan na ce jarumi ina nufin zai tsaya ya fafata da kowa akan hakkinsa, matu'kar kuma ya sanya kansa zai yi abu, to duk tsananin wahalar abin sai ya ga abin da ya turewa buzu nad'i. Baya ga hakan kuma tausayi ne da shi, duk zafinsa inda zai ga kana kuka to zaka ga ya bar yi maka tijara. Sai dai kallon marowa ci nake yi masa na gaske, ni dai ban ta'ba ganin ya yi kyauta ba. Ko garinsu ya je ya dawo, duk abin da zai samo ba dai ya kawo gidanmu ba. Amma kullum a cikin karbe wa jama'a nasu yake, mussaman Dada da ko ta hana shi a k'arshe take kasa juriyar ganinsa cikin rashin sukuni, sai kawai ta bashi. Mazan gidan kuwa basa bashi duk irin yadda zai karyar da kai yana fa'din bashi da lafiya, tunda suka gane matu'kar ku'di ya shiga hannunsa y'anmata banza yake kashe wa, sai kowa ya kulle bakin aljihunsa dama kuma masu k'aramar niyya ne. Sai dai gara shi ma suna bashi, amma da a ce wani ne cikin y'an k'ofarmu baza su bayar ba, daman kuma bamu isa mu ce a bamu ba. Haziki ne na sosai, kwarai da gaske yake ja, amma lalacewar da ya yi ya sanya da k'yar ya iya kammala Diploma a kwalejin Tatari Ali data ke cikin Bauchi. Ya riga su Yaya Salisu samun gurbin karatu a jami'ar amma yak'i mayar da hankalinsa akan karatun har sai da aka kore shi. Hankalin mahaifinsa ya yi tashin gauron zabi, domin zaryar da ya dinga yi tsakanin Bulkachuwa zuwa Toro ba ka'dan ba ce. Haka ya sake samo masa yin diploma akan shaanin tsaro da tafiyar da gwamnati wanda da k'yar ya kammala dan ma shekaru biyu ne. A hakan kuma sakamakon ya yi kyau, domin ya wuce fallasa. Duk da hakan Babansu bai bar shi ba, sai da ya sake samo masa gurbin karatun digiri a jamiar jahar Bauchi ta garin Itas-gad'au. Inda zai karanci ilimin halayyar dan Adam. Wannan kam da taimkon Ubangiji ya kammala domin ba ya zuwa sai an kusa fara jarrabawa, sannan bai fasa al'amari da y'an mata ba. Shekaru biyu da rasuwar mahaifinsa kenan. A kuma wannan shekarar ya tafi bautar k'asa, da shekara ta dawo ya kammala. Yanzu zaman kashe wando kawai yake yi. Sai dai yana yar buga bugarsa domin kusan kullum sai ya je Bauchi. Haka ya dinga satar jiki yana siyar da kadarorin da ya mallaka. Abin kaico kuma ba komai ya yi da kudin ba sai sharholiya da burga a mata. Wani k'aton fili a Bauchi kawai ya tsira da shi, shima dan an zuba masa matakan tsaro ne. Yau da wata sana'a yake da ku'din ko kuma wani gini yake fa'da'da wa da an samu sau'kin bacin ran da ake ciki. Ya zauna kusa da Nazira da take kusa da karshen tabarmar.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161