Chapter 49
Chapter 49
zumuncinmu ba wai sanadin tabarbarewarsa gaba'daya ba". Duk da fuskata a rufe take amma na lura da yadda jikin Babah ya yi lakwas. Domin ta kasa bu'de baki ta ce uffan. Na dai ga tana goge fuskarta da na tabbatar hawaye ne. Tsawon lokaci ba wanda ya yi magana a tsakaninsu. Sai Baban ne ya katse shirun ta hanyar fa'din "Ki saurare ni da kyau Yabi. Aurenki ya banbanta da na dukkan y'ay'an gidan nan. Ina fatan kuma ya zama mafi da'din misali a cikinku. Ki dauka ibada zaki yi. Kinsan kuwa ibada wajibi ce ba wai ra'ayi ba. Ina ro'kon ki zauna lafiya da mijinki. Ina alfahari da ke tabbas Asiya. Amma zan sake alfahari da ke ne idan har kika taka muhimmiyar rawa wajen mayar da Tijjani yadda muke son ganinsa. Na sani babban aiki ne mai nauyi. Amma tunda an yi sa'a yana sonki to matu'kar kin kwantar da hankalinki za'a samu dai-daito. Ina fatan na ganku da iyali masu yawa kuna cikin rufin asiri. Tashi ki je, Allah ya bada sa'a ya maki albarka". Ina kallo yadda Babah ta tashi da k'yar amma bata yarda ta saki hannuna ba tunda Baban Marina ya damka mata. Ta tayar da ni ta fita da ni har lokacin kuma bata iya cewa komai ba. Har muka shiga mota, muka isa gidan tana rike da ni. Da kanta ta shigar da ni dakina bayan ta jira ni na karanta falaki da nasi da attahiyatu har zuwa inda ake yin sallamah a bakin kofa. Ita ce ta bani umarnin yin hakan wanda sai lokacin na ji ta yi magana, rawar da muryarta take yi ya sanya na gane kuka take yi sosai. Duk yadda jama'a suke shiga da fita na ganin dakin amarya bai sanya Babah ta tafi ko ta saki hannuna ba. Matan gidanmu duk wacce ta shigo ta ga Babah sai ta yi turus. Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*. *08032773332* Hatta mamah da matan Baban Tsakiya da suka rakoni tare da ita sai da suka tsokane ta suna cewa "To ko dai ba zaki bar ta a dakinta bane kamar yadda aka yiwa kowa?" Duk da hakan kuma bai sa ta bar ni ba. Har sai da Aliyu ya dauko mata Bulkachuwa cikin abokansa da suke dakon a gama watsewa su rako shi. Yadda mahaifina ya damka mata ni a hannunta, bata saki hannuna ba duk tsawon lokacin nan. Ta kamo hannunsa ta ha'da da nawa ta damk'e cikin nata. Ta ce "gata nan ubanta ya bani amanarta na kawo maka ita da kaina saboda ya nuna mini ita ce tawa ba kai ba. Na karbi amanarta, ni kuma na baka amanarta. Ka dinga tuna dalilin ha'da wannan auren. Ka zama cikin mutane masu halarci da kuma sakanta alheri da alheri. Ban ta'ba farin ciki irin na yau ba. Ka sani na ha'diyi takaici da wahalolinka daban daban. Zan mance komai na yi alfahari da kai har ma na daga maka sawuna ka shiga aljannah idan Yabi ta kubuta daga tozarcinka da gangan. Ko bana raye idan ka kyautata mata tamkar ni ka yiwa. Albarka da farin-ciki zasu kewaye ka. Ka kula da tarbiyarta, kada ka bari ta bijire wa ka'idojin shari'a. Amma ka zama mai sasauci da kawaici domin dai yarinya ce y'ar k'arama. Ina fatan auren nan ya bud'a maka k'ofofin arziki da kuma fahimtar rayuwa daidai. Àllah ya shirye ka ya shirya maka iyali. Allah ya albarkaceku gaba'daya". Ta mik'e ta bar shi a durk'ushe yayin da nake kan gado, hannunmu kuma suna sark'e. Sai da na tabbatar ta yi nisa na fincike hannuna, na ja tsaki na koma gefe. Murya a dushe ya ce "Na yafe miki Asiyata! A gabanki Babah ta ce amanarki ta bani, na tausaya miki, na kuma yi miki sassauci." Na sake jan tsaki fiye da na farko. Ya mike ya fita bayan yan tsirarrun kawayena sun fara hayaniyar ba'a sayi baki ba dare na yi. D'aya ce ma k'awata a ciki ragowar hudun duk wanda suka zo daga Kangire ne wato cousin dina na dangin Gwaggo. Sai kuwa Ihisan k'anwarsa. Ita kuma a takure take a dalilin yayanta ne angon. Ba jima wa suka zo. Suka taba barkwancinsu, sannan aka yi nasiha da addu'a. Suka gwangwaje k'awaye da ku'din sallama mai auki. Sannan suka tafi da su. Ina ganin sun fita, shi kuma ya bisu da niyyar rakiya. Na tashi na rufe kofar dakina. Da ya dawo ba yadda bai yi dan na bu'de kofar ba na ki. Ta windo ya leko ya ce "Ga leda nan ki dauka ki ci nasan da yunwa a tare da ke". Washagari ina jin ya fita sallah na yi maza na fita na doro alwallah a bandaki, takaicina daya bandaki a tsakar gida yake ba a cikin daki kamar yadda na ci buri ba. A gurguje na kammala uzziri na koma na rufe dakina. Ina idar da sallah na yi kwanciya ta. Sai tara da kadan na bu'de k'ofar dakin, domin barci na yi mai nauyi. Ina bu'de wa kuwa ya shigo da sauri. Ya ce "Kin tashi? Sannu ya kwanan bakunta?" Uffan ban ce ba. Amma wani irin bakin ciki ne ya turnike ni. A dalilin rashin bandaki a cikin daki. Na hakaito kusan duk wadanda muka taso tare ko wacce band'akinta a dakinta ne. Na tuna gidan J da na Nura, hatta Nasiba band'akinta a dakinta ne sai ni ce na samu dakuna tamkar na Islamiya tunda na ga falon ma daban ne ba'a hade suke ba". Sai kawai na fashe da kuka mai sauti sosai. Ya diririce ya ce "Daga tashi sai kuka Asiya? Tun dazu fa nake zaman jiran ki tashi ki karya. Ina son na fita muyi sallama da abokaina zasu koma garuruwansu". Ban ce masa komai ba. Illah kukan da nake yi mai tsananin cin rai da nuna k'ololuwar ba'kin cikin da mai yinsa yake ciki. Ya dinga rarrashi yana Fa'din "Ki yi ha'kuri Asiya komai zai dai-daita, daure ki tashi ki yi wanka anjima ka'dan zaki fara yin baki, duk wadanda zasu tafi yau sai sun biyo sun gan ki. Ina ganin kafin Babah ta wuce Bulkachuwa ma sai ta zo, idan ta ganki a hakan kinsan ba zata ji da'di ba." Gaba'daya ya rikice ya ce wannan ya saki, ya ce wancan. Da kuka na ce "Ni ban ta'ba hasko zan shiga gida mai bandaki a waje ba. Gaskiya an cuce ni, an gama da ni. Na saka fashewa da kukan da yafi na farko tsanani. Hankalinsa ya tashi domin a ki'dime ya tattaro ni. Na zabura na k'wace ina sake jin taikacinsa tamkar na rufe shi da duka. Jikina har bari ya dauka domin lokacin ne karon na farko da jikin namiji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161