Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

Downloaded From https://tknovels.com.ng *BAK'AR TA'ADA* *NA* *Surayya Dahiru Gwaram* *(Mrs M.I. Nashe)* *Marubuciyar Halin yau da Sabo da kaza*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *Rok'on addu'arku*! *A irin wannan ranar ta 09 ga wata 09 shekarar 2000. Ubangiji ya karbi ran mahaifiyata. Dan haka ina baran addu'arku dan nema mata raham da gafarar Allah daga bakunanku masu albarka dan Allah*. *Haka nan ina mika sak'on ta'aziya ta ga dukkan musulmai bisa babban rashin da muka yi na bijimin malaminmu kuma uba*. *Sheikh Abubakar Giro Argugun* *Allah ya jikan magabatanmu gabad'aya kwata.* *JAN KUNNE* *KADA A TA'BA MINI LABARIN NAN, KO KARANTA SHI A KOWACCE IRIN KAFA TA SADARWA BA TARE DA IZININA A RUBUCE BA*. *IDAN KUMA AKA YI KARAMBANIN TABAWA, ZA'A FUSKANCI TUHUMA DAGA LAUYANA BAR MUSTAPHA ISA GWARAM*. *GARGADI*. *WANNAN LABARIN KIRKIRARREN LABARI NE* *BA SHI DA ALAKA DA KO WANNE MAHALUKI*. *IDAN KIN CI KARO DA RAYUWAR DA TA YI KAMANCECENIYA DA TA KI, KO WANINKI, TO ARASHI NE*. *DOMIN MANUFAR MARUBUCI ISAR DA SAKO DA HANNUNKA MAI SANDA A CIKIN ZAMANTAKEWARMU*. *LITTAFAN SURAYYA BASA NUFIN HABAICI KO SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA.* *NA GODE*. *GODIYA GA* *SADIK ABUBAKAR* *NA GODE MADALLAH*. *GAISUWAR GIRMA GA IYAYENA KUMA MARUBUTA* *HAJ SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI ZARIA*. *HAJ HAFSAT C SODANGI*. *HAJ MARYAM KABIR MASHI*. *HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM*. *YABO GA* *K'AWATA JAMILA JANAFTY* *IDAN DA WANDA NA GAMSU DA TULIN SOYAYYARTA GA RUBUTUNA DA CIGABANSA TO KE CE* *DUK WATA KALMA TA YI KA'DAN TA FAYYACE GIRMAN SHA'ANINKI A WAJENA* *INA FATAN UBANGIJI YA SHIGA AL'AMARIN KI, YA BAKI MIJI NA GARI*. *GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA MARUBUTA* *Sumayayyah Takori* *Binta Umar Abbale* *Fadilah lamido*. *Hassana D'anlarbawa* *Zainab MAZAWAJE* *Lubna Sufyan* *Nazifa Nashe* *Ayusha Muhd* *Nana Diso*. *Kulsum Baffah*. *Safiyya Um Abdul* *Umm Asghar*. *Aisha Dansabo* *Aisha jos* *Zee Kumurya* *Da dukkan y'an kungiyarmu ta lafazi*. *FATAN ALHERI GA IYAYEN D'AKINA*. *HAJ HALIMA D'ALHA SHEHU* *HAJ RABI SANI* *HAJIYA HALIMATUS SA'ADIYA* *HAJIYA HADIZA FARI*. *HAJIYA ZAINAB ABDULWAHAB* *ALLAH YA HA'DA Y'AY'ENKU DA MUTANAN DA ZASU MUSU KARAMCI FIYE DA YADDA KUKE MINI, INA MATU'KAR GODE MUKU*. *TUKUICIN LABARIN SUKUTUM GA* *AISHA MUHD LAME* *ALLAH KA SO AISHA, KA FARANTA MATA, KA BIYA MATA BU'KATUN TA NA DUNIYA, KA BATA BABBAN RABO A LAHIRA*. *IDAN AKWAI WANDA JINI BAI HA'DAMU BA, NA KE DAKACEN INA MA JINI YA RATSA TSAKANINMU TO AISHA LAME CE MAI KAYAN Y'AN GAYU TA ORIFLAME* *SURAYYA DEE TA GODE, TA YABA MIKI, UBANGIJI YA TAYA NI GODE MIKI*. *Doka mi lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha Babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*. *1&2*. *SHIMFI'DA*. Sunana Asiya Sani Toro. Amma mafi yawa da Yabi ake kira na a dalilin mahaifiyata ta yi aikin Hajj da ni a cikinta. Mama ce kawai bata kira na da hakan sai Asiya saboda tana adawa da Yabi tunda ana nufin nima Hajiya ce. Gidanmu babban gida ne a garin na Toro domin ko yaro k'arami ka tambayi gidan Marina zai nuna maka. A dalilin asalin kakanmu da ya zo daga Kano ya fara kafa wannan sana'ar a garin. Fiye da shekaru saba'in kenan, amma har yau ba'a juya wa sana'ar baya ba, duk da dai an zamanantar da ita, ba kuma cikin gidan ake yin ta ba saboda warinta. Gidanmu babban gida ne k'warai da gaske. Idan na ce babban gida ina nufin mai d'auke da ahali daban daban masu yawa. Ko a k'ofar mahaifinmu Alh Sani (Baban Marina) da shi ne babba mata uku ne. Hajiya Habiba ita ce uwargidan mahaifinmu, mace mai k'ifadi da kutunguila. Duk wani rikicin da yake k'ofarmu, dama cikin gidan tana da sa hannu, ta tsani ta ga ko wanne irin cigaban d'an wata sai nata yaran kawai. Sannan komai cikin dabara da girma ta ke yinsa, ba kowa ne ya fahimci irin makircin da take k'ullawa ba. Sai mu da mu ke rayuwa da ita kullu yaumin. Ta kanka ne komai, ta yadda komai ta shimfi'da akan haka za'a tafi, sai dai ranar da ta samu bacin rana Baba ya bijire mata. Ya'yanta biyar. Yaya Musa, Yaya Hadiza, Yaya Salamatu, Yaya Indo sai autarta da ta haifa bayan ta shafe shekaru masu yawa Nazira, wacce ita ce sa'a ta ta girme ni da wata uku. Sai Mahaifiyata Hajiya Àsma'u wacce muke kira da Goggo. Ba dan tana mahaifiyata ba, amma mace ce mai sanyin hali da matsanancin ha'kuri. Idan na ce ha'kuri, ina nufin ha'kuri gangariya, irin ha'kurin nan da mai yinsa kan saka a alummar da suke kewaye da shi su halaka saboda hakkinsa da za suyi ta d'auka. Yaranta takwas cif. Yaya Salisu, Yaya Rabi'u, Yaya Ummi, Yaya Adnan, Yaya Ali, sai ni Yabi, duk dai bani nake bin Yaya Ali ba, akwai wani ya rasu ne, sai Anas da kuma autarmu Ikilima. Wannan yawan yara da mahaifiyata ta tara a d'akinta, kuma maza, ya sanya Mama ta tisa ta a gaba da masifa da tuggu, kusan kowa a gidan ya tsani mahaifiyarmu, ba kowa ne yake mua'amala da ita ba. Duk gidan bakinsu daya ne a kanta. Duk kuma Mama ce ta b'ata ta, take adawa da duk wanda zata ga ya mu'amalan ce ta Shi yasa hatta mu yaranta bamu da wani kwarjini har a wajen Dada kakarmu da ita ma tana cikin gidan bangarenta daban. Sai Hajiya Sahura muna k'iranta da Innah. Yaranta biyar Na farkon ma mun dan girme masa ka'dan Ubaid, Ubaida sai Abida, Hajara, Ismail da autarmu gaba'daya Saliha. Duk yadda Mama ta so wajen raba zumunta a tsakaninmu bai yi tasiri a tsanina da Nazira ba. Duk yadda bata kula ni, bata sakar mini fuska hakan bai hana ni yin dabdala a dakinta ba a dalilin Nazira. Bare ita kuma da dakin Goggonmu take kwana.. Sau dubu gara Inna akan Mama. Domin dai ba yadda za'a yi Inna ta ha'da wa Goggo sharri, ko ta tsokane ta da gangan, amma bata wani girmama ta a dalilin Mama ta dabarbarce ta, ta hana ta yin mu'amala da Goggo ta hanyar fa'da mata Goggo ce da gida, duk yaranta maza ne, idan Alhaji ya mutu duk su din y'an kallo ne. Da na fara mallakar hankalina sai nake tambayar kaina wai mene ne mahaifinmu ya mallaka da har ake fatan ya mutu? A da kam ya yi arziki k'warai da gaske, domin duk girman Gidanmu shi ya zaga ye ya gine shi, sannan mafi yawa na cikin zuri'arsu shine ya biya musu suka sauke farali. Amma tun shekarar da aka haife ni ya ha'du da y'an damfara suka yi masa sanadin karayar arziki, har yanzu da muke da shekaru goma sha biyar bai farfad'o ba. Yan'uwansa kuma kowa ya zuba masa ido ya zama abin tausayi. Amma a hakan Mama take fa'din Goggonmu ce zata ja komai. Wannan kenan. Sai k'ofar Alh Badamasi(Baban Tsakiya). Matansa biyu da yara sha biyu. Na uwargidan Hajiya guda bakwai . Babban d'anta Yaya Jabir, Zakiya, Jamila, Hauwa, Firdausi, Aisha sai k'aramarsu , Basira. Nan Firdausi ce warinmu. Sai amaryar Momi tana da yara biyar, Nasiru, Naziru, Sararu, Rumanatu

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161