Chapter 86
Chapter 86
na yi kukana. Ina ayyana wai ni Tijjani yake yiwa wannan wula'kancin haka siddan dan ya fahimci na fara sonsa. Na fara zargin akwai abin da yake yi a waje da ya sanya yake iya kawar da kansa a kaina. Gaba'daya na rasa sukuni. Na yi wani iri. Ranar da muka yi kwana hudu a cikin wannan halin. Gaba'daya ya juye mini, tamkar ba shine mai rawar jiki da tsoron ganin fishina ba. Tamkar ba shine mai kulafacina kamar me ba. Ranar da wuri ya shigo. Na yi wanka na sanya riga da wando silky. Wando iya guiwa rigar ma iya tsayinta kenan wando kawai ta rufe. Na taje gashina da yake a tsefe na mulke shi da man gashi na kwakwa da asalain man alaiyadi. Na dauko turarena na mai maiko na oudi na murtsike hannayena da jikina har ma da gashin. Na sake dauko turaren active woman da Tijjani ya canja mini na bi jikina na feshe. Na saka hula marar nauyi kalar kayan barcin nawa. Na fita na same shi yana kallon labaran NTA Bauchi. Na zauna ya dago ya kalle ni. Domin na tabbatar kamshina ya kai masa caffa mai yawa. Na sassauta na ce "Wai mun b'ata ne?" Cikin nutsuwa ya ce "Da yaushe?" Na yi sakare ina kallonsa. Na numfasa na ce"Ai tambayar ka na yi." Ya girgiza kai ya ce "To ke mun b'ata ne?" Na rasa me zan ce masa ma. Na nisa na ce "Nasan bamu b'ata ba. Amma na ga ka sauya ne". Ya daure fuska ya ce "Tun yaushe na canja d'in?" Na ce "Tun kwanaki hudu, tun ranar da ka kai ni gida". Ya yi shiru tsawon lokaci kafin ya bu'de baki ya ce "Kuma sai yau kike bu'katar sanin dalilin sauyin nawa saboda baki d'auke ni a bakin komai ba?" Ga mamakina sai na shiga rud'u na ce "To ai kai ne zaka fa'da mini." Ya girgiza kai ya ce "Babu damuwa ki cigaba da zaman jiran na fa'da miki". Idona ya ciko da k'walla. Na zuba masa ido sosai na nuna kaina da yatsana na ce "Ni kake wula'kantawa saboda kawai ka shiga ka fita kasa na saba da kai ko?. Ai shike nan na gode". Daga hakan na kifa kaina a hannun kujerar na fashe da kuka mai tsananin gaske. Ya taso da azama ya zauna kusa da ni. Ya ru'ko ni na fizge tare da ce wa "Ba ruwanka da ni, komai kake yi na barwa Allah. Ka cigaba da yi mini wula'kanci komai lokaci ne ai, watarana ba zaka yi ba". Ya sake tarairayo ni jikinsa yana kamo weak points dina. Jikina ya fara tsuma. Amma na sake k'wace wa na mike, cikin muryar kuka na ce "Bana so Tijjani, ka bari na fa'da maka". Na fice na yi d'akina ina kuka sosai. Sai da ya yi wanka sannan ya shigo d'akin har lokacin kuma ina dukunkune ina kuka sosai. Sai da ya yi shafa'i da wutiri sannan ya tarar da ni a gadon. Bai kwanta ba. Ya zauna ya kaurara murya ya ce "Asiya tashi mu yi magana." Na share shi, na k'i na nuna ma na ji shi. Ya saka hannunsa biyu ya d'aga ni ya zaunar da ni. Na sake yun'kurin koma wa na kwanta dan na nuna masa ba ni da lokacinsa, sai kawai na ji ya bu'de murya sosai ya ce "Wallahi idan kika kwanta idan ranki sun kai dubu ki tabbatar sai na bisu d'aya bayan d'aya na b'ata su." Jin ya rantse sai na zauna din. Amma na tattaro dukkan fishi na yab'a a fuskata. Ya jima yana kallon yadda nake tunbatsa. Shima ya d'aure tasa fuskar ya ce "Ki saurare ni da kunnen basira Asiya Toro". Jin ya fadi wannan sunan na sake hassala ainun. Ya furzar da iskar baki ya ce "Ranar da muka je gida kin wula'kanta ni, kin tozarta ni! Watannin baya na fa'da miki, ba zai yiwu a gabana ki wula'kanta iyayenmu ba. Idan kin ture girmansu na k'annen mahaifinki ne, to ki sani baki isa ki ture nasabarsu da ni ba. Ina kuma da hak'kin ki mutunta iyayena. Dole ne, wajibi ne Asiya ki mutunta mini dangin uwata matu'kar kina son mu zauna lafiya. Ba zai yiwu ina aurenki kuma in zuba miki ido ki dinga yin rashin mutunci ba. Bilhiillazi wannan ne karon k'arshe da zaki ga wani cikin iyayenmu ki k'i gaishesu, ko ki yi musu gaisuwar je ka na yi ka". Na fara kuka ina ce wa "To ina ruwanka ne kam. Kai baka ga irin k'iyayyar da suke yi mini ba? Saboda baka kishina, saboda kai sun yarda gyatumarka yar'uwarsu ce shiyasa kake ganin bekena. Duk abubuwan da suke yiwa ubanmu baku da kaico. Ai ka sani ba sai na fa'da ba, ko auren nan nawa sun yi sanadinsa ne dan kawai suna ganin bazan cigaba ba. Amma da sun tabbatar zan samu nutsuwa a cikinsa a sai sun rugurguza shi. Yanzu ma kuwa nasan akwai lokacin da zai zo da zasu rabamu tunda zuciyarsu mai k'yashi ce." Ya buge mini baki ya ce "Kada ki kuskura ki fa'di maganar banza a kansu a gabana. Dole fa ki mutunta su a matsayin surakanki tunda ke kin yanke nasabar da ta hada ku". Cikin gigita na ce "To ka sake ni, bana son yin surukuta da su. Kai ma bana sonka Tijjani". Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* Jikinsa ya yi sanyi domin ya ga matsanancin fishi a tare da ni. Ya numfasa ya ce "Na sani ai ba kya sona Asiya. Ban manta ba, amma na sakankace a d'an zaman da muka yi, zaki iya mini kawaici da alkunya akan abin da kika san zai musguna mini tunda kin sani sarai an jarrabe ni akan son ki. Amma yanzu na gane da gaske ba kya sona tunda akan idona kika k'i gaida Baban Tsakiya cikin mutunci duk da kashedin da nake yi miki da ido. Sannan kika gaida Jabir cikin falli har kina kiransa Yaya alhalin kin kankare zumuntar da ubansa." Na yi shiru domin kam jikina ya yi tub'us. Ya cigaba da ce wa "Saboda shi kina sonsa, kuma yafi ni ku'di shi yasa kike ce masa Yaya ni kuma ki gatsa Tijjani gatsal duk da na girme shi kuma ni ne mijin ki. Asiya ba zamu tab'a daidaita wa da ke ba alhalin kin ri'ke BAK'AK'EN TA'ADODI. Yanzu duk k'uruciyar ki ai k'iris ya rage ki yi sha bakwai. Kin san kuma hukuncin wacce ta bu'de baki ta ce mijinta ya sake ta ba tare da gamshasshen dalili ba. Sannan kina da ra'ayin ruk'au na k'ullaci. Hakan kuma ba siffar mace ta gari ba ce.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161