Chapter 136
Chapter 136
kuma halaka shi". Na numfasa tare da ajiyar zuciya mai nauyi na ce "To" Ta shiga jero mini albarka. Ta ce "Idan akwai abin da yafi albarka da yafiyar uwa na roki Ubangiji ya yi miki da ke da zuriarki. Idan har Ubangiji baya juyar da addu'ar uwa akan d'anta , to alafamar ma'aiki ba zaki wulakanta a wannan duniyar ba. Duk inda rayuwa zata kai ki, komin tsanani zaki zama cikin rufin asiri mai yawa. Da ikon Allah wani mahaluki ba zai ga gazawar ki ba Yabi". Da rawar murya na ce "Na gode Gwaggo! Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka". Na jiyo ajiyar zuciyarra alamun ta samu nutsuwa da yadda na karbi ban hak'uriinta. Ta ce "Ameen, ina tagwaye?" Na ce "suna makaranta". "To ke me kike yi yanzu?" Ta tambayar cike da soyayya mai yawa. A hankali na ce "A zaune kawai nake Gwaggo ". "Tashi ki yi nafila, ki daina bari wannan lokacin mai tsada na wuce ki, baki yi salatul duha ba. Kinsan duk abin da Ubangiji ya rantse da shi mai falala ne, mai daraja ne. Allah ya ce "Wad Duha! Lalle ki yawaita neman gafara da rahamar Allah a wannan lokacin, Ubangiji baya juyar da addu'ar da aka yi ta a wannan sa'ar sai dai jinkiri, ko ya mussnya maka fiye da abin da ka roka alheri". Na ce "To!Da budaddiyar murya. Ina jin soyayyar Gwaggo na sake tunbatsa a dukkan sassan jikina. Kwalla ta zubo mini wacce bata ciwo ba ce, ta tausayinta ne, tare da tausayin wacce duk bata girma da uwa mahaifiya ba. Tabbas soyayyar uwa ita ce mafi kololuwa a wannan duniyar. Muka yi sallama na tashi na dauro alwallah, na yi walaha. Akan sallayar barci ya sure ni, irin wanda na jima ban samu yin sa ba. Akai Babah take yi mini waya, tana tambayar lafiyata da lafiyar yara. Na dinga mamakin yadda ta sauko. Na sani tana sona. Amma a kwanakin baya gabadaya ta canja mini. Yanzu kuma ta dawo mini Babah tawa Mai kaunata. Na dinga mamakin haka, da na ga kaina zai dauki caji Sau kawai nayi Hamdala a raiana tare da rok'on Ubangiji ya sake tsare mu daga sharrin masu tofi a cikin kulle kulle. Da daddare muna kwance a dakinsa yara suna dakinsu da yake cikin falona sun yi barci. Dukkanmu kowa tunanin zuci yake yi. Ba abin da nake so irin na fice na bar gidan Tijjani. Tufka da warwara kawai nake yi. Maganganun Gwaggo sun yi matukar karya lagona. Domin a da na kudire wa raina daga ranar da ya shiga dakin Nasiba ya kwana da ita. Tabbas washegari zan bar shi, bari na har abada tunda nasan Baban Marina zai bani masauki tare da kyakkwar mu'amala a tsakaninmu. Amma yanzu Gwaggo ta mini tilas din cigaba da zama ta hanyar rarrashi da dabara. Na nisa na saki ajiyar zuciya. Daidai lokacin ya ce "Sannu Asiya! Ban kula shi ba, ya ruko ni, na yi bakam tamkar mai barci. A sanyaye ya ce "Zullimi ne yake kama ni from no where! Samar mini da nutsuwa pls. Dan Allah bude baki ki fad'a mini wata kalma da zan samu sassauci a zuciyata. Ina daf da tarwatse wa Asiya". Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Tsuntsun da ya ja ruwa". Ya sake rik'e ni ainun. Ya kasa ce wa kanzil. Ajiyar zuciya kawai yake yi. Murya babu amo ya ce "Idan na mutu Asiya dan Allah kada laifina ya shafi twins. Ni kaina bana gane kaina a wasu lokuta, kin ga da hantsi ko yamma sai na ji tamkar ana hura mini huta a kirjina. Da zarar wani aka jima kuma sai na ji duk yadda aka azalzale ni na je Toro sai kuma na ji ke nake son na dawo ma ga ni. Ko dai na haukace ne Asiya?" Da k'arfi sosai na ce "Tunda har kana banbance wasu alamuran da hamkalinka sarai. Kuma ina nan akan bakana, ba zan zauna da kai ba Bulkachuwa. Ana kawo maka Nasiba ka tabbatar na hak'ura da kai". Jikinsa ya dauki rawa. Ya ce "Bazan iya rabuwa da ke ba. Haka kuma idan ban aure ta ba, bazan tab'a samun nutsuwa ba. Ki taimake ni mana". Na ce "zaka ga taimako ganin idon ka. Na rantse maka duk wani sababin duniya ka shiryawa ganinsa. Hala dai ka manta Yabin marina ne Tijjani?". Ga mamakina bai iya taso mini da masifar sa ba. Gabadaya jikinsa ya sake sosai. Washagari na tashi da bala'i ko kallon inda yake ban yi ba. Na yarda da zancen Gwoggo. Amma bazan iya samar masa da nutsuwar da ake so ba. Ya je can ya k'arata da dibar albarkar sa, shi da masu goya masa baya. A wannan safiyar ya mini magana yafi sau goma ban kula shi ba. Na ki yin girki. Shi kuma ba shi da kuzarin da zai yi. Gabadaya ya koma Tijjanin farkon aurenmu. Ba na yanzu da yake masife ni a dalilin ina adawa da k'arin aurensa. Ya kai ya kawo a tsakanin dakinsa da nawa. Ya kasa fita bare na samu na d'an sarara. Tunda gabadaya haushinnsa nake ji mai kama da tsana. Sallah kawai yake fita. Da k'yar ya lallaba ya tafi dauko su Hanif. Da gudu suka shigo. Na yi maza na hadiye damuwar da nake ciki na shiga yi musu oyoyo tare da murmushin yak'e. Na dora musu indomie, bayan na juye musu ruwan wanka. Na kammala yi musu wanka, suka yi sallah. Sannan na juyo mana indomie muka fara ci da su. Hanif ya ce "Baban 2 sauko mu ci". Hamim ya ce "Ba shi da lafiya ai marar lafiya ba ya cin abinci" Takaici ya shake Bulkachuwa. Ya daidai ta zamansa ya ce "Hamim baka tausayina ko kad'an?. Zaka ga tsiya, daga yau Hanif zan dinga siyo wa abina tunda kai uwarka kake so kawai". Da yake mai kwadayi ne sai ya marairaice ya ce "Na daina Baban 2 sauko mu ci to." Bai sauko ba, ya koma ya zauna. Ba tare da ya sake ce wa komai ba. Muka kammala da kansa ya saka musu yunifom din islmamiya ya rakasu waje ya dawo. Ya zauna daf da ni ya ce "Asiya Tsakanin ki da mai rumfa me ya hana ki daukar ciki?" Na hassalo na ce "Saboda na gama haihuwar da kai, sai da wani". Ai kuwa ina rufe baki ya cakume ni yana kokarin murde mini baki. Na dinga zille wa, ina ture shi. Maimakon ya bar ni tunda ya ga kuka nake yi sosai, duk da bai mini komai ba, kuka nake na takaicinsa da na aurensa. Amma bawan Allah bai yarda ya kyale ni ba. Ya sure ni ya yi dakina da ni. Sai da ya yi abin da yake so. Ya tara mini gajiya ya ce "Ya kika ji? Kin hana ni abinci, amma kin dafa muku ke da y'aya'n ki, kun ci. Sai kuma na zarta ki k'arfi da kuzari." Na ja tsaki na juya masa baya, bayan na ja mayafi na lullube jikina. Da daddare ya fita ya siyo tsire mai yawa. Ya dafa shayi ya kawo falo. Ya juye naman a plate ya ce
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161