Chapter 32
Chapter 32
ya zame mini sanadin shiriya da bud'ewar arziki." Ya mike ya tafi yana sake godiya sosai. Ajiyar zuciya kawai Baban Marina yake yi, na lura ba k'aramin ki'dima ya shiga akan al'amarin ba. Murya babu amo ya ce "Yabi idan kina son Alhaji ki ce masa ya turo wakilansa, idan kuma ba kya sonsa to ki fa'da mini zan sallame shi". Na yi k'asa da kaina na kasa amsa masa, daga haka kuma sai ya fita, na bishi da ido amma tunanin a yadda jikin Baba ya mutu murus akan al'amarin Bulkachuwa da ace Adda Nazira ba ta yi aure ba, Babanmu na iya juya wa nak'asunsa baya, ya bashi auren ta. A fili na furta "Alhamdulillah da Allah ya sanya ta yi auren ta ta barranta da auren tantiri ma'abocin *BAKAKEN TA'ADODI*. Haka kawai sai zuciyata ta buga da tsananin gaske, a dalilin ayyana wa da na yi, wata'kila fa idan ban tsayar da miji ba, Baba yana iya cewa ya bashi ni. Nan da nan na tsirtar da yawu saboda kyankyaminsa da ya taso mini. Gashi dai zabgegen saurayi ne dogo cak mai murdadden jiki tamkar ya fito cikin Kyawawan Tirkawa(Turkish). Amma kwata kwata baya burge ni duk da farar fatarsa da bak'ar sumarsa, da suke rudar y'anmata. Asalima Y'ar tsama muke yi, sassaucin rikicinmu a dalilin kwamshina ne, domin sosai yake yi masa alheri. Ya karbi takardunsa, samun aikin ne dai shiru, amma ana saka rai tunda kwamshina baya wasa kuma mutuminsa ne. Tuni Yaya Salisu ya samu aiki a asibitin Toro a matsayin accountant na asibitin tunda dama bangaren ya karanta. Yaya Rabi'u da Bulkachuwa ne shiru amma akwai kyakkawan zaton suma zai samo musu. Wananan dalilin ne ya sanya ya daina tsokanata ta hanyar muzanta ni. *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* A fili na furta "dutse a tsakanina da Bulkachuwa ya Rabb". Ina wankin ina jaddada wa kaina matu'kar Yaya J bai yi yun'kuri mai k'arfi ba, to nan da lokaci kankani zan bawa kwamishina dama ya fito tun zuciyar Baba bata ayyana masa wani al'amarin da zai iya kassara ni, ya dauwamar da ni a cikin ba'kin ciki mai tsananin gaske ba. Na kammala wankina. Mama ta fito ta ce "Yabi anjima zan aike ki gidan Nazira". A ladafce cikin murna na ce "To" Domin kuwa ha'din baki muka yi da Naziran, saboda na yi ta tambayar Baba zani gidanta yana hana wa, basan me yasa yake hana ni zuwa ba, amma bai ta'ba yin k'orafin zuwa koyon sana'ar da nake fita ba kullum. Duk kuwa da ce wa ake yi shargalle nake yi da sunan koyon sana'a. Shiyasa Nazira ta ce wa Mama ta bani kwanuka na kai mata kar aba wa marar wayo ya yi b'arinsu su yi lamba. Tunda idan ita ce ta aike ni Baban ba zai hana ba, ba kuma zai tambayi aiken menene ba. Dan haka a gurguje na shirya na tafi. Muna zaune ina bata labarin yadda muka yi da J. Ta galla mini harara ta ce "um um uhum. Ashe dai Yabin bata san ciwon kanta ba. Har wane ne Jabir kuma? Idonta ya ciko ta ce "Allah ka sanya sai bayan raina zaki zama matarsa!. Jikina ya sabe da rawa na ce " Addda Nazi! Cikin gigita domin ban ta'ba ganin fishi mai yawa a tare da ita irin hakan ba, ita din mai ha'kuri ce, mai kuma sanyin hali ce tamkar dai ba daga tsatson Mama ta duro ba. Murya na rawa na ce "mene ne na wannan mugun fatan Nazira?" Idonta taf cike da hawaye ta ce "Da kin fahimci yadda na k'yamci al'amarin, da baki zo gabana da wannan maganar mai bak'i tamkar zunubi ba. Ban iya fishi ba, shi yasa nake kaffa kaffa da duk abin da zai ha'da ni rikici da jama'a, domin ni kaina ina tsoron fishina ina kuma yawaita neman tsarin Allah da shi. Amma zan fa'da miki, matu'kar kina son ganin fishina da barranta kaina daga al'amarinki to ki cigaba da yi mini wannan maganar da nake fatan ajalina ya riske ni kafin ta wanzu". Sai ta fashe da kuka sosai. Cikin kuma kukan take cewa "Yanzu duk ba'kin cikin da aka cusa wa ubanmu, duk yadda aka wula'kanta ki, dan ke ce asararriya har ki kalli dan Baban Tsakiya da sunan soyayya irin ta aure? Na rantse miki da Allah idan ace Jabir ne ka'dai namiji a duniya gara ki tabbata babu aure, ko ni na mutu ki maye wa mijina madadina da dai Yaya Jabir ya same ki. A haukanki Baban Tsakiya zai bar shi ne? Ko kuwa kwantaccen tunaninki ya fa'da miki Baban Kasuwa zai bashi aurenki alhalin tasa y'ar ce matarsa? Kaico da wannan maganar da kika nufo ni da ita. Nima cikin kuka na ce ",Takura mini ya yi shine na yi masa gatse dan ya shafa mini lafiya." Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da fa'din "Amma shine kike rawar jikin fa'da mini, idan ba kya so me ya sanya zaki yi mararin sanar mini?" Ta nisa ta zarce da fa'din "Idan zaki ha'kura da shi ki hakura Yabi. Domin Jabir ba mijinki bane, na tabbatar duk sanyayyar zuciyar Baban Marina ba zai ta'ba bawa Jabir aurenki ba, ban da dai ma mai k'arfin halin jure damuwa ne da kuma kawaici da tuni bai ha'du da ciwon shanyewar barin jiki ba a dalilin abin da yan'uwansa suka yi masa. Ashe duk zafin ranki, da kishinmu da kike yi a banza ne a kuma fatar baki ce? Wallahi matu'kar zaki nemi zama ahalin gidan Baban Tsakiya ki tabbatar kin fita daga namu ahalin Yabi" Ta tashi ta bar ni tana kuka sosai. Jikina ya mutu wato ba k'aramin gaba ba ce ta shiga dangimu ba kenan? Duk ha'kuri da kawaicin Nazira ita ce take fadin tsauraran kalmomi akan zumunta irin haka? To idan har Nazira mai sau'kin hali da k'ullaci zata yi hakan to ina ga Yaya Ummi shakikiyata kuma mai ra'ayin rikau?. Domin ita hatta zumuncina da Nazira adawa take yi da shi tana ganin ita ce tafi kusa da ni, ita ta cancanci mu yi irin wannan soyayyar, ta kasa fahimtar tazara mai yawa ce a tsakanina da ita, Nazira kuwa tare muka taso tamkar tagwaye, kuma Ubangiji ya jefa mana soyayyar juna duk da k'unbiya k'unbiya irin ta iyaye mata da kishi yake haifar wa. Bare kuma mazan Gidanmu. Yaya Rabi'u shine sa'an Yaya J tare suka taso, bayan jini da ya ha'dasu, abokanta suke yi sosai, amma Yaya Rabi'u da kansa bayan an yiwa J aure da Maijidda na ji yana fa'dar bai k'i wani a duniya har cikin zuciyarsa irin Baffanninmu ba, yana kuma fatan kada a k'addara auren zumunci a tsakanin y'an k'ofarmu da tasu ila yaumil k'iyamati. A sanyaye na bita uwar d'akinta na dinga rarrashinta da k'yar na shawo kanta ta ha'diye kukan nata tamkar yarinya y'ar k'arama haka ta koma mini. Wannan yinin bai yi wani armashi ba tunda zuciyarta ta riga ta baci. Har na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161