Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

bincike da nazari akan gidan yawa mai dauke da mabanbanta iyalai. *GIDANMU ne kawai kwamacala ta dabaibaye shi?* *A GIDANMU ne kawai ake yin kasafi irin na kashin dankali ma'ana na sama ya danne na kasa?* *A GIDANMU ne kawai ake mayar da babba k'arami saboda ba shi da wadata ko kuwa?* *A GIDANMU ne kawai ake ta'ba yan ubanci ko kuwa?* *Ba k'aramin caji kwakwalwata take yi ba dan neman sahihohin amsoshi wadannan tambayoyin*. *Ayi bitar da nutsuwa domin wannan karon gidan yawa zamu kutsa sosai* VIP 1K. REGULAR 500. 2384876855 SURAYYA IBRAHIM ZENITH BANK. *ASSALAMU ALAIKUM* *Masoyan rubutun Surayya Dee na gaishe ku, na kuma yaba muku* *Dafatan zaku yi hakuri, ku bi labarin sannu a hankali, har ku fahimci sakon da nake nufin isar wa.* *Ba zan ce muku komai ba. Abu d'aya nake da tabbaci ba zaku yi nadamar bibiyarsa ba.* *Kawai fatana kada ku kosa da yanayin rubutuna.* *Allah ya taimakemu, Allah ya zaunar mu lafiya da y'anuwanmu da abokan zamanmu*. *Allah ya bamu lafiya, ya bamu hakuri da k'addarar da muke fuskanta a rayuwar nan*. *Surayya Dee* ✍️. *BAK'AR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *MARUBUCIYAR HALIN YAU DA SABO DA KAZA* •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *GODIYA* *INA MATUKAR GODIYA BISA ADDU'AR DA KUKA YI WA MAMA*! *ALLAH YA KARBA, YA BADA LADA*. *HAKA NAN INA NEMAN UZZIRINKU BISA RASHIN AMSAWA. DOMIN NA KARBI SAKON MUTANE SAMA DA DARI BIYAR, TUN INA AMSAWA HAR AL'AMARIN YA GAGARI KUNDILA*. *DUK WACCE BAN AMSA BA, INA AMFANI DA WANNAN SHAFIN WAJEN GODIYA TARE DA YABAWA A GAREKU GABADAYA* *ALLAH YA JIK'AN DUKKAN MAGABATANMU*. *KUNSAN DAI YADDA AISHA LAME MAKEUP ARTIST DIN GUDUYO, TA KWARE WAJEN SANIN HAKIKANIN MAN DA ZAI DACE DA KOWACCE FATA, WALA DRY KO OILY*. *BABBAN ABIN BIRGE WA DA KAYANTA FARASHI MAI SAUKI NE DA YA ZARTA NA SAURA SALAMA* *HANZARTA KI TUNTUBE TA DAN KI GA JERIN KAYAYYAKIN ORIFLAME KALA DABAN DABAN* *SANNAN TANA DA HADADDEN GANYEN SHAYIN DA AKA YI SHI DA GANYAYYAKI MASU SAISAITA JINI DA KITSE A JIKIN DAN ADAM.* *LAME TEA YAFI SHAYI MAE MADARA*. *IDAN KUWA KIKA CI LAME POPCORN INA TABBATAR MIKI KIN YI ADABO DA SAKE CIN WANI GUGGURU MATUKAR BA LAME POPCORN BA NE*. *07036662633*. *3&4* K'aramar hukumar Toro tana cikin k'ananun hukumomin jahar Bauchi. Duk wani mai nazari yasan yadda Ubangiji ya wadata Toro da girman k'asa. Ita ce k'aramar hukuma mafi girma a dukkan fa'din tarayyar Nigeria dama Africa ta yamma gaba'daya. Garin Toro an kasa shi zuwa Gundumomi uku. Gundumar Toro, gundumar Jama'a da gundumar Lame. Sannan akwai kabilu daban daban bayan Hausawa da Fulani. A karkashin jahar Bauchi ta ke amma tafi makwbataka da jihar Filato. Shi yasa garin kewaye yake da ni'imomin kayan itatuwa da rashin zafin rana sosai. Ba dan ina y'ar garin ba, Ubangiji ya dabaibaye garin Toro da tarin faloli Alhamdulillah. Dare ne amma ba ainun ba, mafi yawa mun ha'du a kofar Kakarmu Dada ana ta hira da tatsuniya. Kannenmu kuma sai wasan d'an dunmi suke yi. Dukkanmu y'anmata mu bakwai da muke kai d'aya muna zaune akan tabarma, idan aka dauke shalele Nasiba da take kishingi'de a jikin Dada. Sannu a hankali Dada take taunar goron bakinta tana mulmulawa. Kyakkawar dattijuwa mai kyakkawan jiki. Asalin Bafulatanar Lame ce, kowa kuma yasan asalin mutanan wannan garin fulanin Mali ne da kiwo ya saka suka tsallako Nigeria suka yi sansani a yankin na Lame. Wani ikon Allah mafi yawa na ahalinta sun samu kyawun halittar fulanin Lame. Haka muke y'an gidanmu son kowa k'in wanda ya rasa. Wani irin kallo take mana na kurillah. Ta kasa ha'kuri ta ce "Na fa'da muku dukkanku ku zauna cikin shirin ko ta kwana. Domin kuwa ba zaku fi haka gandare wa a gabanmu ba. Dukkanku abubuwa sun cika muku k'irji. Ko wacce a cikin ku wanki take yi a gabanmu, ina kallon zamani ni Binta! Muna cikin alhini. Allah yasa intingifarin da muke nacin yi mun samu rabauta ana karban sallarmu". Dariya ta kama mafi yawanmu. Ni da nake da kaud'i na ce "Dada Ashe ba'a karban sallarku ne?" Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Ai matu'kar kana da yarinyar da ka yi saken da ta fa'di a gabanka, to kuwa babu makawa sallarka bata isa gaban zati, daga bakin k'ofa ake dakatar da ita!" Nasiba ta ce "Allah ya kawo mafita. Yanzu biya mana karatun na yau". Nan da nan ta furzar da goron bakinta dan girmama karatun da zata d'ora mana. Ta tsume ta ce "Mu karanto na jiya". Muka ha'da baki wurin rera karatu cikin sigar wake muka ce "Idan attishawa ta sauko mana, idan wani bawa a kusa da mu ya ce mana "Rai ya hadu da Gafarar Allah!" Sai mai attishawa ya ce "Ya-hadi kumalle. Idan kuwa zamu ci adda'ami. Zamu fara da ambaton Allah. Idan koshi ya zo mana sai mu ce "Sawaba ta sauka akan me nemo wa da mai dafa wa". Dada ta murmusa tabbacin ta gamsu mun ri'ke karatun nata da kyau. Ta ce "Madallah!". Cikin alfaharin muna da fikirar fahimtar karatun da take yi mana. Ta muskuta ta ce "yau karatun yiwa kai rigakafi daga shaidanu da makarai zan dora muku". Muka ha'da baki wajen fa'din "Mun gode Dadarmu, Allah ya kara miki nasibi. Annabi yasan da ke". Ta numfasa ta ce "Ameen, a kuma tsananta yi mini rokon dacewa da shiga cikin masoyan SHEHU". Na kasa jure wa na ce "Ashe Dada ba zaki bar zancen Shehu ba? Kowa ya bar Allah da ma'aiki ai ya bar hanyar tsira." Nan da Nan ta fusata ta ce "kaico da Yabi! Yabi ba zaki tsira ba, waya yake inkari da jikan Manzo? Tabbas sai gafalalle". Na ci je na sake ce wa, Annabi dai aka ce mu ri'ke ba waninsa ba Dada, iyalan gidansa suna da girma da hakkin mu so su mu kare mutuncinsu. Amma ba'a ce a kai su wani bigire da zai iya zama halaka ba. Da kansa ya ce "Zan bar muku kura'ani da sunnata wato (Hadisansa) idan kuka bisu kun tsira. Amma ku kun shure komai, kun dauko shehu kuna neman mayar da shi abin bauta?". Ai kuwa ta sake harzuka ta ce "Wahalar rayuwa akan ki Yabi! Mai gadon taurin rai da kafiya, kaicon ki, kaicon ki! Da yi mini izgilanci Asiya". Jikina ya sabe da rawa a dalilin ba irin jan kunnena da Gwaggo bata yi mini ba, akan kada na sake na janyo abin da Dada zata dinga yi mini mugun fata. Ga shi ban ji ba, na yi sanadin da take fatan na dauwama cikin wahalar rayuwa. Kafin na ce komai sai ga Tijjani wanda mafi yawa an fi k'iransa da sunan garinsu Bulkachuwa. Wani irin zabgegen saurayi. Dogon gaske har d'an rankwafa wa ya yi ka'dan. Fari ne tas, irin fulanin Bulkachuwa, a murde yake, shi ba siriri ba, kuma ko ka'dan baya cikin masu kiba. Ga dogon hanci da ya k'awata doguwar fuskarsa. Baya ga hakan manyan idanuwansa ka'dai sun isa abin burge wa. Ban ta'ba ganin namiji mai jajayen

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161