Chapter 68
Chapter 68
ba sai da tara ta gota. Sannan da ya shigo ina jinsa da Rafia a zaure da alamu ita ma unguwa ta je a lokacin ta dawo. Da k'arfi ta ce "Ka gaida amarya kwana biyu bana zama ne shi yasa ban shigo ba". Ban ji me ya ce mata, tunda bai daga tasa muryar ba. Wani irin abu mai tsananin gaske ya tokare ni. Shaidan ya shiga zuciyata ya ayyana mini tare suka dawo. Shashanci suka je suka yi abunsu. Hawaye ya b'alle mini. Ya tarar da ni ina matsar k'walla. A rikice ya zauna kusa da ni ya ru'ko ni. Na fizge cikin kuka sosai na ce "Ka je kun gama iskancin kun dawo shine zaka ri'ke ni?" Ya zauna ya ri'ke kansa. Ya kasa ce wa komai. Amma ba k'aramin kidima ya shiga ba. *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. ✍️ *BAKAR TA'ADA* *47&48* *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* Tsawon lokaci ina kuka shi kuma ya kasa ce wa komai. Da k'yar ya nisa ya ce "Asiya Toro son ki ya zame mini jarabta mai girma. Daga ranar da aka ambata mini za'a bani ke daga ranar ban sake samun y'ancin zuciyata akan lamarin ki ba. Me yasa zaki yi mini irin wannan mummunan zaton?" Ya fa'da cikin b'acin rai matsananci dan har wani haki yake yi. Na cigaba da kuka ban kula shi ba. Ya damk'e ni sosai cikin tsawa ya ce "Ina miki kallon yarinya k'arama kina mini kallon biri boko. Gaba'daya shekarun ki nawa ne a duniya. Ina tausayin k'ank'antar ki, amma ke abin da kika sani ya zarce na manyan y'anmata masu shekaru ashirin da biyar. Kin ture dukkan ka'idojin shari'a, kina ta musguna mini. Babu ragayya a tsakaninmu. Ai ko ban ci darajar aure ba ya kamata na ci na jini. Wallahi na yi zaton ko wani kika ji ya jefe ni da wannan al'amarin sai inda k'arfin ki ya k'are. Amma har da ke a cikin jerin wadanda suke mini yarfe dan na tozarta na yi ba'kin ciki.! Ya numfasa yana maida numfashi tamkar mai mura. Jikina sai bari yake yi a dalilin na shiga zullumin irin damk'e ni da ya yi. Nasan dalilin da ya sanya kike iya kallon idona kike jingina mini wannan Bak'ar TA'ADA. Saboda ban nemi hakkina ba. Ashe tunda ke ba yarinya ba ce kamar yadda nake miki kallo kuskure na yi, da na dauke kai. Tunda kin san kishi kin kuma iya har a kaina da ba sona kike yi ba shike nan, magana ta k'are zan d'ora miki girman da zai sanya ki dinga jin nauyin fa'da mini duk abin da ya zo bakin ki." Na yi muk'us ban da b'ari ba abin da jikina yake yi. Ya sake ni, ya fita. Ai ina ganin ya fita, na zabura na rufe k'ofar da sakata. Na yi shiru ina ta zare ido domin har lokacin zuciya ta bugawa take yi da tsananin gaske. Can na ji yana kwankwasa k'ofar. Na yi bakam a zuwan barci nake yi. Bai tsananta ba, ya juya ya tafi. Da asuba ban yarda na fita ba duk yadda fitsari ya matse ni, sai da na ji fitarsa masallaci sannan na yarda na bu'de k'ofar. Har ya je gidan burodi ya dawo barci bai dauke ni ba. Kamar daga sama na ji muryar Baban Marina a tsakar gidan. Zuciyata ta tsinke sosai. Gumi ya dinga yanko mini. Gaba'daya na tsorata na tabbatar Tijjani ne ya kai k'arata. A sanyaye na bu'de k'ofar, na taya Tijjani marabtarsa. A falo muka sauke shi. Ya amsa gaisuwa ta da walwala na d'an samu kuzari. Domin na lura babu bacin rai a tare da shi. Ganin hakan ya k'arfafa mini guiwa na mike na bu'de firij na d'auko ragowan k'wai uku da ya ragu. Na soya masa a gurguje tunda nasan da burodi. Kafin na gama shirya kofina a tray har shayin ya kusa juyawa. Na dauka na kai gaban Baban. Ina dawowa kuwa shayin har ya tafaso na juye a flask na kai masa. Cikin soyayyar da na kwana biyu ban ga ni ba a dalilin fishin da ya yi da ni akan auren Tijjani. Ya ce "Sannu Yabi. Allah ya yi miki albarka. Na ji da'din yadda na tarar da ku, kuna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Allah ya dauwamar da aurenku, ya baibayeku da albarka ta inda kuka zata da ta inda baku zata ba. Wanzuwar aurenku na cikin burina a wannan duniyar. Ki zauna lafiya, ki yi ha'kuri da kawaici irin na uwarki." Kaina na k'asa amma hawaye nake yi. Tabbas idan da Tijjani zai bu'de baki ya yi masa bayanin yadda muke zaune da bai yi wannan farin-cikin ba. Da bai sanya mini albarka irin hakan ba. Tijjani ya ha'da masa shayi ya ce "Bismillah Baba ka ci abincin Asiya". Da murmushi ya ce "Na riga da na karya, amma tunda Ubangiji ya nufe ni da zuwa gidanku zan ci abin da kuka ba ni. Ina fatan Ubangiji ya buda maka k'ofofin ciyar da iyali cikin sau'ki Tijjani". Nan da nan ya masa da "Ameen Baba". Yana kurb'an shayin Tijjani na yankar biredin yana cusa masa k'wai a ciki, yana mik'a masa. Ba wani sosai ya ci ba. Amma ya shanye shayin. Ya yi hamdala ya ci gaba da sanya albarka cikin marari. Ya ce "Tijjani ina fatan dai lafiya kuke zaune babu damuwa?" Jikina ya d'auki rawa. Amma ga mamakina sai ya ce "Lafiya k'alau muke zaune Baba. Ai Asiya har bayan idonka tana kiyaye tare da girmama umarninka". Da'di ya k'ara kama shi. Ya ce "Alhamdulillah! Allah ka so Asiya, ka sanya soyayyarta da tausayinta a zuciyar mijinta. Shi kuma ka bashi lafiya da jarumta da arziki mai gudana. Àllah ka zaunar da su lafiya, ka basu zuri'a dayyiba." Daga haka ya mik'e ya gyara rigarsa ya ce "Nurun ala nurun a dukkan rayuwar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161