Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

da muke yi ne mu da Gwaggo". Kwanaki suna ta shude wa har muka yi jarabawar zangon karatu na uku. Muna tafe kowa da sakamakonsa a hannunsa, Nasiba da su Firdausi sai murna suke yi a dalilin sakamakonsu ya yi kyau. Nazira ma babu laifi domin ta sha biyu ta zo. Amma ni kam sakamakona ba zai nunu ba domin kuwa ta arba'in da takwas na zo a cikin mu hamsin da bakwai. Kowa ya nuna sakamakonsa a tsakaninmu. Amma ni na boye nawa kamar yadda na saba. Muna tafe Maijidda sai fa'di take "Akan me za ki dinga ganin results dinmu amma ke ba zaki yarda a ga na ki ba?" Na gallah mata harara na ce "Saboda mahaifina bai fara gani ba, ba kuwa wanda yafi cancantar ya fara gani sai shi". Ta tunzura ta ce "Kins an Allah yau sai na ga ni, ai na sani ta karshen aji kike yi. Ban da class master din ajin naku saurayinki ne ai demotion ne ya kamace ki Asiya". Na fusata kwarai da gaske na ce "Tabdi jam! Yabi kika je fa wa wannan maganar?" Ba shakka ta ce "An fa'da miki Asiya. Kin dauka ina jin tsoron ki ne? Idan ba jakar aji kika dauka ba to miko mini sakamakon ki kamar yadda na baki nawa kika ga ni". Na girgiza kai da tare da yin k'wafa mai tsananin gaske. Nazira kuwa sai fa'di take "ba ruwanki da al'amarin Yabi fa Maijidda". Ta ce "Na shiga komai zata yi, ta yi ina daidai da ita". Ban ce komai ba sai da muka isa zauren Gidanmu ba zato na shake Maijidda da dukkan k'arfina, ina kai mata duka ko ta ina. Kafin ta yi yun'kurin ramawa na jibge ta sosai, sannan kuma muka ci gaba da gwabza wa. Aka rasa mai rabamu domin duk wacce ta ta'ba ni kanta fa'dan zai koma sun san haka dabi'ata take. Nazira sau fa'di take Yabi sake ta, amma bata ri'ke ni ba, domin ta san ce wa zan yi bata taya ni fa'da, ta taimake ni ba tunda bata kishina, akan me zata ri'ke ni? Na turmushe ta ke nan na debo k'asa ina shirin cika mata bakin da ya yi mini izgilanci sai ga Bulkachuwa ya shigo. Ya hau fa'din ke Asiya Toro wanne irin abu kike yi haka ne?" Ganin na fara kokarin danna mata a baki ya sanya shi iso wa garemu, bai jira komai ba ya saka hannunwan sa ya cira ni cak kamar y'ar tsana ya yi wurgi da ni. Na yi sa'a na dire akan sayyadata. Da yake a hassale nake sai na durfafe shi ina cewa "To kai ma din ai ba tsoronka nake ji ba, ka zo ka zaune mana a gida ka uzzira mana haba.?" Na kalli yadda ya harzuka amma ko gezau ban yi ba, duk da ban fi iya cikinsa ba. Ya kalli Nazira ya ce "Me ya ha'da su?" Ta tsara masa yadda aka yi ba ragi babu kari. Ya juya ga Maijidda da take hawaye ga jini a hancinta tabbacin habo ne ya goce. Ya ce "Dube ki gansamemiya da ke amma wannan y'ar tsakon ta lallasaki haka, wanne irin mutuwar zuciya ce ta same ki?" Na galla masa harara tare da murguda baki na ce "To ni komin girman gardi ma ba zai hana na zubar masa da jini ba, bare kuma mace yar-uwata". Ya nuna kansa ya ce "Asiya Toro ni kike tunanin zaki buga?". Na ce "Ba dan ha'da jiki da kai sai ballagazaye ba, ba abin da zai hana na zage mu gwabza y'ar k'ashi Wallahi". Ya nuna ni da yatsa ya ce "Asiya Billahillazi zan sumar da ke, yar iska marar mutunci kawai.". Yana rufe baki na ce "Ga ka nan babban dan-iska mai shiga fa'dan mata, yabi bayan wacce take da abin da zai lallaba ya cuce ta." Ya yo kaina yana fa'din ashe "Izgilancinki mai girma ne haka?" Ga mamakinsa sai kawai na yi shirin kai masa naushi tamkar bacaniya. Wannan dunukule hannu da saitin da na yi, ya yi matu'kar bashi dariya da tu'ajjibin k'arfi halina. Ya tsaya ya ce dambe zaki yi da ni? Na ce "Allah suturu bu'kui na yi dambe da mai daudar zunubi irin ka, kuma ni ba ballagaza ba ce, kawai zan kare kaina ne daga cutarwar ka". Ya jima bai ce komai sai ya kalle ni ya ce "shahsa da bata iya komai ba, sai fa'da da rashin kunya a aji kuwa ita ce dalkiya". Ba'kin ciki ya mamaye ni, idona ya ciko da hawayen takaici na ce "Na gode wa Allah da na yarda ina zuwa makarantar, wani ma tsabar akuyanci korarsa aka yi daga karatun nasa. Me za'a yi da mai halin bunsuru?" Ya rasa yadda zai yi da ni sai kawai ya shammace ni ya dauke jakata yi wuf ya zaro takardar sakamakon da take a farko farko. Ya juya zuwa waje ya bu'de ya ga yadda jan biro suke mamaye sakamakon. A karshe ya ga ta yadda na zo sannan ya mayar ya shigo ya kalli yadda na tumbatsa ya ce "Anya Asiya ba dusa kike ci ba kuwa? Ace har kin doshi hamsin? Gaskiya ina taya Baba ba'kin cikin asarar ku'din taran da ya wanzu yana baki". Cikin rawar murya na ce "Bulkachuwa Yadda ka tozarta ni a gaban wanda suke son na tozarta in sha Allah sai an tozarta budurwarka fiye da yadda ka mini, da ikon Ubangiji sai ka ha'du da sharrin mace, sai ka muzanta a idon duniya". Ya make kafa'da alamun ko a jikinsa tare da cewa "Yabi yanga mai kwakwalwar kifi". Ganin hakan ya sanya Maijidda ta mike tana jin karfi yana shigar ta tunda ta ji abin da take son ji. Ta mini gwalo tare da cewa "Na ji dai, dama nasan baki tsinana komai ba". Ta shige wajen Dada da saurin ta. Yayin da ragowar suke fa'din "Yi ha'kuri Yabi, ai kin nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane. Ba gashi ta tsere ba". Na jijjiga kai na ce "Ai dan ta ga Bulkachuwa ya tsaya mata ne". Yayin da shi kuma ya ce "Ba dole na tsaya mata ba, tunda ke din karfinki na aljanu ne, na tabbatar ba ke ka'dai kike fa'da ba, kina samun tallafin aljani mai kilabo da gwaigwai". Duk wajen aka fashe da dariya illah ni dana sake fusata na daga murya "Ina ce wa "Allah ka dora wa matar Bulkachuwa aljanun da zata dinga daga shi sama tana danfara shi da k'asa". Ya wuce yana fa'din "Duk bala'in aljani ba zai shigo mini gida ba, domin hafiza zan aura mai hazakar gaske a ilimin boko da na addini. Safiya da marairaice ta yi ta tofe mini gidan da azkhar, idan kin ga aljanu sun yi tasiri, sai a gidan wanda basa mayar da kai a wajen bautar Allah irin ki". Na wuce shi zuwa shashin Dada. Na tarar da Maijidda tana ta kuka yayin da Dada take sakacen hakori da tsinken zabori hankalinta a kwance. Na bu'de baki na ce "Dada sannu da gida, mun dawo". Ta amsa ba alamun damuwa a tare da ita. Na juya na tafi sai na ji kukan Maijidda ya karu tana

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161