Chapter 131
Chapter 131
DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Babah ta kasa ce wa komai domin ita gabad'aya ma alamarin tsoro ya shiga bata. Tana kuma mamakin rashin kunya da son kai irin na Maryo. Bata yi zaton son zuciyarta ya kai hakan ba. Ta kasa ce wa uffan saboda tsananin kaduwa da ta yi. Ita kuwa ta dinga kuka tana face majina tamkar Dada ce ta kwanta dama. Washagari ko karyawa bata yi ba ta ce zata juya. Da k'yar Babah ta roke ta akan ta bari ta karya. Rai a bace suka rabu a dalilin Babah ta tabbatar aure kam babu a tsakanin Nasiba da Tijjani. Rai a matukar bace ta isa Toro. Ta gurfana gaban Dada tana kuka tana fad'a mata karya da gaskiyar cin mutuncin da Hauwa ta yi mata. Dada ta taya ta bacin rai tare da rarrashinta tamkar yarinya karama. Tana cin alwashin sai ta ci mutumcinta tunda bata san yakamata ba. Bijirewar da Babah ta yi akan auren tare da fitowa baro baro da ta yi ta ce alamarin ba zai yiwu ba. Sai ya zama d'an zani. Domin hakan ya fusata Baba Maryo tare da cin alwashin sai Tijjani ya auri Nasiba ko zata yi yawo tsirara, ta ga karshen rashin kara da nuna banbanci. Takanas ta tafi cikin jeji can kudu da Jos. Ta samo asiri da surkullen da muradinta zai cika. *Bayan waatanni biyu* A hankali Tijjani ya fara rikice mini fiye da bara. Sai mu kwana gari ya waye bai ce mini uffan ba. Zan masa magana goma bai fi ya amsa ni sau biyu ba a gajarce. Ya daina shayin yin waya a gabana. Yanzu har an kai jallin da zai bawa twins waya su gaishe ta. Duk da dai bai tab'a kama suna ba. Sai ya ga dama yake cin abincina. Jiya ma da na zauna kusa da shi ce mini ya na tashi yana bukatar kad'aici. Murjewar da na yi, nan da nan na fara tsomare wa. Sosai ya murde irin yadda ban taba zaton zai yi ba. Na hakurkurtar da zuciyata na dinga ba shi hak'uri tare da rokon ya fad'a mini laifin da na yi masa. Yana bude baki sai ce wa ya yi "Haihuwa yake so. Tunda ba zan haihu ba, shi aure zai yi, idan zan zauna na zauna idan kuma bazan zauna ba, to bai rik'e ni ba." Na zuba masa idona da suka soye. Na ce "Tsakanin ka da Allah kana mini adalci Tijjani?" Ya hassalo ainun tare da ce wa "Ta ya ya zan yi miki adalci Asiya? To ko kawai zaki yi gaba ko zaki samu adalin?" Na sake daskare wa. Na yi maza na kame bakina domin na gane komai na iya faruwa a tsakaninmu. Amma hawaye ke tsere babu jinkiri kuncina. Ya ja tsaki ya fice ya bar ni. Yana fad'in "Me za'a yi da mace mai rainuwa da azababben kishi. A ce mace ba zata taimake ka ta rufa maka asiri, ta taya ka son abin da kake so ba. Sai sarhutu da mance alheri kawai ta iya ". Na yini cikin bacin rai. Yayin da shi kuma ya yi tafiyarsa Toro da yara bai damu da halin da ya bar ni a ciki ba. Ina kuka na d'auki waya na bugawa Baban Marina karon farko da na yi hakan tunda ya aurar da ni. Na kasa magana sai kuka nake yi masa mai tsuma zuciya. Bai katse ni ba. Sai da na gaji dan kaina na katse wayar. Baban Marina ya dawo gida cikin sanyin jiki a dalilin yadda kukan Yabi ya buge shi. Ya leka kofar Dada dan ya bata man zafin da ya siyo mata sai kawai ya ga Tijjani da Nasiba a gefen bisihiyar zogale suna zance. Dada na daki abin ta. Duk da ba yau ya saba ganinsu ba, amma yau din sai da zuciyarsa ta buga da tsananin gaske. Ya amsa gaisuwarsu cikin k'arfin hali. Ya shiga wajen Dada ya fito, ya fita. Ya zauna kan tabarma amma zufa ta rufe shi. Ya dinga jin wani iri. Duk yadda ya so jurewa kasa wa ya yi. Yana tambayar kansa yanzu Tijjani yana da rigar da za'a bashi aure ke nan?. Ya tuna irin kukan da Yabi ta kira ta yi masa dazu, ya san kuka ne na neman agaji, kuka ne mai harshen damo. Daren ranar ya yi masa tsawo ainun. Washagari ana idar da sallar asuba ya ce Salisu ya raka shi Bauchi. Tamkar jifa haka Yabi ta gansu. Zuciyarta ta karye. Domin ta hango rauni da wata irin soyayyar ta a kan fuskar mahaifinta. Tare da Tijjani suka musu iso zuwa falo. Yana amsa gaisuwarsu ya yi gyaran murya ya ce "Zuwa na yi takanas dan na fad'a miki ce wa ki yi hakuri ki zauna a dakin ki. Ki kuma sauke dukkan hakkina da kika san Ubangiji ya dora miki. Daga nan har zuwa lokacin da Allah ya kaddara muku zaman kada ki yarda ki zalunce shi. Kada kuma ki fito babu izininsa. Aure da kike ga ni darajar sa ta wuce duk zaton mai zato. Sai dai bisa adalcin Ubangiji ya kewaye shi da dokoki da kuma sharudda daban daban. Bai barmu kara zube ba. Ina rokon ki, ki k'ara hak'uri a cikin wannan tsukun da ake son kaimu k'asa da bak'inciki mai tsanani. Idan har kika yarda kika yi hak'uri, ni kuma na miki alkawarin zan jaddada damar da shari'a ta baki na zabin cigaba da zaman ko akasin hakan matukar zalunci da cin fuska ya shigo gidan auren ki". Cikin kuka da rawar murya na ce "To Babanmu". Ina fad'in haka ya mik'e tare da ce wa "Allah ya yi miki albarka. Ya fice bai ko bi takan tagwaye da suke ta rige rigen gaishe shi ba. Yaya Salisu ne kawai ya amsa musu tare da ciro ledar alawowi a aljihunsa ya damka kowa tasa ledar. K'warai Tijjani ya muzanta da yadda suka fice basu bi takansa ba. Ya bi bayansu. Ba jimawa ya shigo ya zauna. Ya ce "Baban Marina ya canja, ya yi bangaranci. To wai a kaina aka fara k'arin aure ne da za'a mini wulakanci irin haka?" *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633 Ban kalle shi bare na ba shi amsa. Maimakon shi ma ya sawa bakinsa linzami tamkar yadda na yi sai ya zarce da ce wa "Baban kasuwa ne kawai mai mace daya, shi ma nasan a dole yake zaune bai k'ara ba. Shi Baban Marina din da yake tunzuri irin haka ai uku ne da shi, shine ni zai nemi hana ni jin yadda a ke ji?" Na kalle shi da fishi sosai na ce "Ya isa haka! Ina rantse maka da Allah Tijjani zamu kwashi y'an kallo. Komai kake ji da shi na wulakanci ya tsaya iya kaina. Amma ka yi kad'an ka tabo alfarmar ubana. Ya wuce hakan Wallahi". Bansan ya aka yi ba jikinsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161