Skip to content

Chapter 145

Chapter 145

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

Ina ganin nasara a kudirina. Matukar yana gidan ita zan saka ta yi masa girki, ta dafa masa zobo. Wani lokacin ya yi godiya ya kwashi girki. Wani lokacin ya ce "Tunda na zama matar yayansa na ture girme mini da ya yi, nake mu'amalantarsa a matsayin k'anina. Ban da haka me yake hana ni na yi masa hidima da kaina sai na saka yarinya ta yi masa." Na yi dariya na ce "Yaya Aliyu ko a lahira wani na cin arzkin wani ai" Ba'a d'auki lokaci mai yawa ba ya fara fad'awa tarkonmu. Domin idan ya zo bai ganta ba, ya dinga tambayar me ya hana ta zuwa. Ko ba hutu suke yi ba, da sauran tambayoyi. Da na fahimci hakan kuwa sai na dakatar da zuwan nata. Domin so nake ya taka ya neme ta a inda take ba wai sai ya ganta dan ya zo ba. Ilai kuwa wanne tudu wanne gangare ya silala yake zuwa daga haka har suka had'a kansu. Tunda aka garkame Tijjani ban yi farin ciki har zuciyata ba sai akan wannan al'amarin. Domin dai Na tabbatar Aliyu mutumin kirki ne. Sannan Babah uwace ta gari bayan haka Ikilima zata auri mai rufin asiri. Zamu sake zargowa k'ofarmu wani hasken. Bugu da kari y'aya'nmu zasu kasance cikinsu guda. Tunda shi da Tijjani daya ne, haka ni da ita. Da maganar ta fasu a gidan Marina a lokacin da iyayensa suka je nema amsa aurenta. Ba abin da ba'a ce ba. Bak'in ciki muraran har ce wa aka yi ai k'aramin likita ne, wasu kuwa cewa suka yi ba ma likita ba ne. Malamin tsafta ne. Shi dai Baban Marina ya ce ya basu. Mu kuma dukkanin y'aya'n sa muka goyi bayan al'amarin. Aka saka aure idan ta kammala makaratan da wata daya, watanni biyar masu zuwa. ** Alhaji Auta yana zaune al'amarin duniya ya sake damalmale masa. Gabadaya kasuwa ta juya masa baya fiye da bara. Fatan da yake yi akan kamfani ya kyamaci filin Tijjani saboda an kama shi da laifi bai ci ba. Har asiri yake nema akan su saki filin amma shiru. Su kuwa kamfani sunce riba suke nema. A wajen suke samun gamsuwa, babu ruwansu da laifin Tijjani. Idna lokacin da zasu biya ya yi, zasu tuntubi iyalinsa. Ya rasa inda zai saka ransa. Jiya aoa kama babban dansa a cikin sahun y'an kidnaffing. Dazu kuma k'aramin dansa aka kama shi da yana yuwa yarinya yar shekaru uku lalata a cikin gidansa. Gabadaya kwanciyar hankali da nutsuwa ta yi masa tutsu. Ya rame, ya zama tamkar mai ciwon sida, tsufa ya keto masa na ban mamaki. Yana kishingide amma damuwa ta yi masa k'awanya. Wai shine naira dubu take yi masa wahalar rik'e wa?. Zullimi ya kama shi, idan akwai Bakar Taadar da ya yi ta dame shi bata wuce had'a kai da aka yi da shi wajen yiwa dan amininsa kazafin da yake kulle tsawon shekara guda ba. Ya yi shiru yana tuna irin yadda Tijjani yake zuwa yana gaishe shi cikin girmamawa. Akai akai yake yi masa alheri a matsayinsa na aminin ubansa kuma ubangidansa a kasuwa. Amma shaid'an da hassada suka saka ya jagoranci zaluncin da aka yi masa. Kuka shabe shabe da hawaye. Ya rasa ta inda zai warware wannan k'ullin da suka yi. Kan dole ya kira diaya abokin sharrin nasa, wanda yaro ne a kansa dan ba zai girme wa Bulkachuwa ba. Ya dauka murya a shak'e ya ce "Alhaji kana mini waya da ta wuce kaidar hankali gaskiyar magana na ke fad'a maka. Nima nema nake idan zan samu, ka fitine ni da bani bani gaskiya". Da zullimi ya ce "Ba rokon zan yi ba Haladu! Maganar Tijjani zan yi maka. Gaskiya na yi abin da ya sha mini kai. A harzuke ya ce "To ni me zan yi maka? Ina ce Kai ka kawo shawarar, Kai ka kitsa yadda za'a yi? Ni kawai na karba a hannunsa tare da bawa haro ya ba shi. Hatta lambar wayar da aka kira shi, kai ka siya tun kuma a ranar ka taune shi. Kai ka yiwa Yan sandar hanya shunensa tare da bada lambar motarsa. Kaine zaka yi dakon zunubin ka. Idan ka yi kuskuren saka ni a ciki kuwa Wallahi sai na bata maka suna a idon duniya. Sannan sai na lahanta ka." Kuka wiwi ta k'wace wa Alhaji Auta tamkar mace. Ta ya ya zai kubutar da Tijjani? *** Yini na yi ina yiwa wata hamshakiyar Hajiya kunshi ita da mukarrabanta. Da zata tafi ta ajiye mini kudi a envelope. Ga mamakina da na bude dubu hamsin na gani a ciki. Duk da sunzo da yawa sosai. Amma tabbas kudina bai kai haka ba. Rub'anya mini ta yi. Ban sani ba ko dan na yi jarumtar yi musu jollof din taliya mai dad'i ne. Na kuma baibaye su da pure water mai sayi tunda Ina siyarwa. Na lura ta ji dad'in yadda na yi musu, sannan ta yaba da kunshin da na yarfawa kakkaurar k'afarta fara tas. Cikin hira nake fad'a mata na iya kwalliya ma sai dai nafi bada k'arfi a lalle da kitso. Kwanaki biyu da tafiyar ta sai ga waya ta k'ira ni akan wani satin zan je gidan gwamnati na yiwa mai dakin gwamna kunshi zata je bikin d'iyar gwamnan Jigawa. Jikina ya sab'e da rawa. Ni Yabi zan je government house a sanadin sana'a ta? A fili na ce "Alhamdulillah! Ubangiji ka bani damar da zan yi amafani da ita na fito da Baban 2. Allah ka yi alkawarin taimakon wanda aka zalunce shi. Ubangiji ka shiga lamarin Tijjani." Na zauna kusa da Babah ina fad'a mata. Ta yi farinciki sosai. Na ce "Idan mun je ganinsa zan fad'a masa, idan bai amince ba zan hak'ura, tunda nasan baya son na dinga zuwa gidajen mutane". Ta zuba mini ido ta ce "Allah ya yi miki albarka, Ubangiji ya kawo mana karshen ibtilain nan. Allah ya dawo da mijin ki, zaman zai yi miki yawa babu miji a tare da ke." Sai kawai ta fashe da kuka sosai. Da rawar murya nake bata hak'uri. Ina ce wa "Zan iya Babah! Zan jira shi, da ikon Allah zai dawo a kusa ma". ** Muna ta shirin tafiya dubo Baban 2 a dalilin a irin wannan ranar ta asabar din k'arshen ko wanne wata muke zuwa duba shi, tare da kai masa kayan shopping tamkar na dan makarantar kwana. Ni nake had'a masa wannan kayan. Kudin lallena da kitso suna tafiya ne a hidimarsa da ta gidanmu domin Yaya Aliyu ne yake rik'e da mu. Daidai da pencir ban san na siyawa su Hanif ba. A yadda na taso a irin gidanmu da babu tausayi da tallafawa na k'asa ban yi zaton Aliyu zai yiwa Bulkachuwa irin wannan zumuncin ba. Na sani hidimar kayan abincinmu da baya mantawa akwai alfarmar mahaifiyarsu a tare da mu. Amma yadda baya mance wa da y'aya'n Tijjani na gamsu ko Babah bata tare da mu zai yi iyakacin kokarinsa. Da na fahimci basu mayar da hankali wajen kai wa Tijjani kayan ciye ciye ba. Ni kuwa sai na mayar da hankali, domin shopping nake yi masa mai sunan shopping. Hatta kifin gwangwani ina

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161