Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ta hau hidimar kai masa abinci, a raina sai kiyastawa nake yi ina ma ina da hali na dinga soya masa miya mai d'auke da naman kaji ko na shanu zuk'u zuk'u a ciki. Din ya dinga ci da abinci. Na fito na gan shi zaune a rumfa akan tabarma jikinsa duk ya yi futu futu, ga alamun gajiya mai yawa a tare da shi. Tausayinsa ya tsirga mini, cikin rauni na ce "Sannu Baba, sannu da kokari". Ya dan sassauta ya ce "Sannun ka dai Yabi Asiya". Na dan murmusa domin shi ka'dai ne yake ha'da mini sunan guda biyu. Tunda ya fahimci ina bacin rai idan ba'a ce mini Yabi ba, sai ya kankare kirana da gayan Asiya. Na wuce shi na fa'da d'akin Mama wajen Nazira. Na tarar itama shirya wa take yi. Tare muka fito muka risina muna cewa "mun tafi Baba". Ya amsa da cewa "A dawo lafiya, ku kula da kanku". Muka shiga sashin Baban Tsakiya muka fito da su Firdausi da Saratu. Amma wani irin abu ya tsirga mini mai nauyin gaske, ba dan komai ba illah ganin da na yi Baban Tsakiya yana cin dafadukan shinkafa gefe kuma kunshin balangu ne, ga pure water mai sanyi a gefensa cikin yar bak'ar leda da alamu shi ya shigo da su. A banzan ce ya amsa gaisuwarmu tamkar ma bai ganemu ba. Na tuna gabzar da muka baro Baban Marina yana ci zufa tana yanko masa. A hankali na ce "Àllah ga Yabi! Ka buda mata hanyoyin arziki ta jiyar da iyayenta da'din duniya". Kafin muje k'ofar Baban kasuwa muka yi kicibus da Maijidda, ta fito. Na ji da'din hakan domin shi kam ma tsiyatakunsa sun fi na Baban Tsakiya yawa. Gaba'daya muka d'unguma k'ofar Dada dan yi mata sallama da kuma biya wa Nasiba. D'aya bayan d'aya muke gaisuwar tamkar masu neman tabarraki, kuma dole sai an kama sunanta idan ba hakan ba sai ta dauke kai tabbacin bata karbi gaisuwar ba. Abin da zai biyo baya kuwa ba mai sau'ki ba ne. **** An idar da sallar isha dukkan mun hallara a k'ofar Dada. Sai jiranta muke ta kammala nafilfilinta ta d'ora mana karatu, domin karatun nata ba k'aramin nisha'di yake sanya mu ba. Ta idar ta dinga jan dogon carbinta wanda kafin ka kammala jan k'afa d'aya ma lokaci ne mai yawa. Amma haka muka jira ta kammala. A fili ta cika addu'arta da salatil fatih. Dada tsohuwa ce da bata samu ilimi sosai ba, amma Ubangiji ya cika zuciyarta da son addini, ta rabauta da yawan yin istigifari, matsalarta guda tana da son zuciya, matu'kar zaka bata abin duniya to zata juya gaskiya ta koma karya. Hakan kuma ya yi tasiri a zukatan ahalinta, domin kuwa a tsakaninmu ma mun k'ullaci yadda take fifita Nasiba akanmu, ta yadda ta fimu gata da iko a gidanmu. Kowa yasan Dada tafi son jikokinta da y'ay'anta mata suka haifa, mussaman su Nasiba sannan Bulkachuwa. Saratu ta ce "Dada muna dakon karatun ne, jiya kin ce addu'ar tsari da makarai da miyagu zaki d'ora mana." Ta dan yi tari ka'dan ta ce "Hakkun Saratu". Ta numfasa ta ce zan biya sau uku daga nan sai ku dinga fa'da bayan na fa'da." Muka amsa da cewa "To". Ta yi Basmalah, ta yi salati ga Annabi, sannan ta nemi tabarrakin SHEHU. Na yunkura zan yi magana sai kawai na yi maza na saka hannu na kame bakina. Da karsashi ta ce *"Wa makaru, wa makaru, Wallahu kairan makirina".* Na amsa karatun nata ina ganin kuskuren ciki ka'dan ne. Muna saurare har ta biya sau uku kamar yadda ta fa'da. Sannan muka koma tana yi, muna amsawa har kuma ta ce mu yi da kanmu. Muka dinga yi har muka rike dama kuma mun biya ayar a islamiyya. Ina son na yi mata gyara amma ina jin tsoron abin da zai biyo baya. Ganin mun ri'ke sai ta ce "To zan baku addu'ar farin jinin samari, ku yawaita yinta atafe kuke, ko a zaune ko kuma a kwance". Muka yi shiru dan nuna kunya. Ta numfasa ta ce *"Ya tifa risubuha ragadan".* Muka k'yal-k'yalale da dariya, na kasa daurewa na ce *"Min kulli.."* kafin na karasa ta ce "Lah! Ai iya inda na tsaya, zaku dakata, duk wacce ta yi karambanin cika ayar to ta kuka da kanta. Domin maza kala kala zasu yi ta bin ta har mazan dabbobi sai sun bi'de ta da sunan soyayya saboda karfin addu'ar, kunsan Annabi Isibu aka saukar wa ayar." Muka kasa cewa uffan domin kowa dariya ce a bakinsa yake gimtse wa". Ta kalli Nazira, Saratu, da Nasiba ta ce ku dimance ta babu kakkautawa kune masu nauyin jini, ke Yabi ba sai kin yi ba, ku kuma ragowan saffa saffa zaku dinga yi tunda kuna samun mane ma." Nasiba ta bata rai ta ce "wanne irin nauyin jini kike magana Dada? Duka duka fa shekarunmu sha shida ne wasu ma basu cika ba, ban da dai ana auren wuri a gidan nan ina ma muka isa a samu a sahun y'anmata a wannan zamanin?". Dada ta ce "A wajena kun wuce y'anmata ma kun zama iyayen mata, tunda ba wacce bata yin wanki duk watan duniya, ni kam kullum sai na yi tuba sama da sau dari uku, tare da addu'ar Allah ya cika mini burina wajen sallar layya ace ko wacce maneminta ya tsaya duk sai mu tattara mu rabu da ku salin alin. Amma a duk sadda na hango zugar ku gabana faduwa yake yi, inta shiga firgicin yadda sallolimmu suke goriya a madakata basa isa gaban Zati". Cikin dariya na ce "Wai a ina kike koyon wadannan karatun naki irin na makafi ne?". Haka kawai na fa'da ta rusa ihun da ya janyo hankalin ahalin gidanmu, mu kuwa gaba'daya muka zuba mata ido muna mamakinta, yayin da jikina ya yi mugun sanyi, zuciyata ta shiga kaiwa da komowa cikin fargaba mai yawa. Cikin kankanin lokaci dukkan iyayenmu maza sun bayyana, wasu daga cikin matan gidan suma sai iso wa suke yi cikin zullumi duk da dai ta kan yi irin haka sa'i, sa'i. Tana kukan tana fa'din "Yabi ce, Yabi ta zage ni, ta mini gorin mijina makaho ne". Mamaki ya sake kama mu, domin sai a ranar muka san kakanmu Alh Garba wai ashe ya makance a karshe karshen rayuwarsa, duk cikinmu ma ba wadda ta san shi bare har a yi mata gori, sannan dama ana gorin ciwo ne?" Haka Baban kasuwa da yake jin shine a saman kowa, ya hau cin mutuncina yana fa'din ba zai yiwu kullum sai na tozarta uwarsu ba. Zai dauki mummuna mataki a kaina ya ga take takena so nake na gagari kowa, to shi ba zai zame masa komai ba akan mahaifiyarsa ya kore ni daga gidan, ko kuma ya dauke Dada su bar mini gidan, idan ya so iyayena su shata jan layi da shi. Baban Marina kuwa cikin sanyi yake fa'din "Haba Iliya yaushe zan haifi y'ar da zata shiga tsakaninmu, komai zaka yi mata ai ka isa ne". Baban Tsakiya ya ce "A a ai yaran yanzu basu da kunya balle mutunci baka ganin yadda ta saka uwarmu kuka to mu kuma idan

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161