Skip to content

Chapter 134

Chapter 134

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

To albishirinki yar uwa!* *UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1 *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633*. Bamu yi mamakin furucinsa ba domin tamkar dan kama haka Hamim ya ke da magana. Ga kafirin wayo tamkar ya shekara goma. A sanyaye Tijjani ya jasu jikinsa dukkansu. Yana gode wa Yabi a zuciyarsa da ta rufe masa k'ofar da y'aya'nsa zasu tsane shi. Domin ya riga ya gane Hamim, ba abin da yake so a duniya sama da Yabi. Hanif ne ba shi da alkibla, bai san wa ya fi so a tsakaninsa da ita ba. Sosai ya tisa mu gaba a da tarairaiya. Rabon da ya yi mini hakan na manta. Gara yara yana ta tasu ni ce dai babu dad'i a tsananinmu. Da wuri ya sa suka kwanta. Suna yin barci kuwa ya ja ni dakinsa. Bamu samu kanmu ba sai tsakiyar dare. Mun tabbatar mun yi kewar junanmu. Haduwar kuma ta yi awon gaba da wani kason bacin ran da ke zukatanmu. Barci na shirin daukemu ya yi azama ya ce "Mu tashi mu kai kukanmu gun Allah. Ya taimake mu ya kawo mana mafita ya kuma yi mana maganin duk abin da zai farrak'amu". Duk yadda na gaji tikis. Haka na daure na yi wanka, na bishi sallar da ya tayar muka dinga yi har sai da lokacin asuba ya yi. Kwanakin da suka biyo baya na samu sassauci domin ya yi matukar rage kyara ta. Sannan ya daina fita ya shafe lokaci yna waya a waje. Watak'ila yana yi ne kafin ya shigo. ** Tunda Babah ta koma Bulkachuwa ta shiga damuwar halin da ta baro d'an uwanta, mahaifin Yabi. Sannan ta shiga alhinin yadda ake ta shirin bikin Tijjani da a Nasiba babu nadamar komai a gidan Marina. Ta kasa gane kanta sai kawai ta durfafi addu'a tare da fatan Ubangiji ya warware dukkan abin da babu alheri. Kwanaki biyu kullum sai ta yi mafarkin wai randar Dada ta sanyi akwai maciji mai dafi a ciki. Kwanaki biyu a jere tana wannan farkin babu tsagaitawa. Tun bata tunawa har ya fara shiga ranta mussaman da take ganin macijin na yunkurin fitowa ya hallaka Dada. Ta kasa katabus ta fara kokwanto akan lamarin. Yayin da ya rage saura sati uku biki. Baban Marina ya mik'e ya fara samun sauki a dalilin yadda Yabi ta kwantar da hankalinta. Takanas ta zo har Toro ta bashi tabbacin zata jure matukar ba Tijjani ne ya sake ta ba, to zata yi dukkan iyawarta ta tsallake dukkan kalubalen da yake gabanta. Murya na rawa ta ce ",Ya kamata ka huta Baba. Ya kamata ka samu nutsuwa, sannan mune zamu yi gwagwarmaya mu tsaywa kanmu. Ranar da babu kai kuma waye zai tare mini fad'a ko ya tsaya mini? Bini da addu'a kawai, na karbi wannan kaddarar da dukkan zuciyata, Allah yasa abokiyar arziki ce". Ya d'ora hannunsa a kaina ya ce "Ina alfahari da haihuwar ki Yabi. Ina samun nutsuwa saboda Ubangiji ya azurta ni da haihuwar ki. Da ikon Allah duk abin da kika saka a gaba na alheri sai kin ga fatahi a cikinsa. Allah ya shirya miki yaranki, Allah ya hore miki mijinki. Ya miki shamaki da dukkan abin da zai cutar da ke, ko ya gigita miki kwanciyar hankalinki". Cikin jarumta na ce "Ameen na gode Baba". ** Mafarkin maciji a randar Dada sai idan bata kwnata barci ba. Kan dole ta shirya ta tafi Toro, a lokacin sati biyu ya rage daurin aurensu Nasiba. Sai didima ake yi tare da kambaba lamarin. Masu adawa da Yabi suna fad'in "Duk d'aya ne to wa za'a ki a tsakaninsu? Tare da fake wa da ce wa rabon aure ai kisa yake yi, gara a yi, kowa rabon ta zata samu". A wannan tsukun na gasgata k'arfin jini domin hatta su Yaya Indo da suke mana yan'ubanci na gaske sun kaurace wa shiga shirgin auren ko taya masu adawa kanzagi da nuna kowa nasa ne a tsakaninmu. Kafatalin y'an k'ofarmu sun kame daga shiga cikin maganar auren gabadaya. Sun janye jikinsu sai isu isu. Ai kuwa mutanan gidan suka yi ca wajen sakin maganganun tare da ce wa "Kamar gaske. Su a tsakaninsu ma suke son ganin wani a uku shine yanzu zasu nuna mana an tab'asu? Suka dinga furzar da maganganun da su Yaya Indo suke fad'a akanmu a baya. Yaya Ummi kuwa ta k'i yarda da yadda ake son a sake gwara kansu. Tunda yawanci a kanta suke gulmar sai kuwa ni da na ke cikin rufin asiri. Suke taya masu yamididin duk abin da aka gani a jikina ni nake yiwa kaina. Da kuma ce wa duk k'afafar da nake yi bana gaban Tijjani domin har yau bai bar iskancin kule kulen mata ba. Na ka'du k'warai da Nazira take mayar mini wadannan maganganun da ake ta fitowa da su tare da ce wa a bakin su Yaya Indo aka fara ji. Amma yanzu sun fitittke wai suna kishin kanwarsu sai ka ce gaske. *** Babah sai dube dube take yi a tsakanin randunar Dada amma bata ga komai ba. Ta kasa samun nutsuwa. Rashin ganin macijin, ga shi bata daina ganisa a mafarkinta ba. A yanzu al'amarin ma yafi ta'azzara ko barcin rana ta yi sai ta ga ni. Tana zaune a gefen randar Aliyu ya k'ira ta a waya wanda a yanzu likita ne a F.M.C Azare. Cikin rauni ya ce "Babah kina yawaita addu'a kuwa? Tunda kika fad'a mini auren Yaya Tijjani da yarinyar nan ban sake samun nutsuwa ba. Anya kuwa! Ke ce da kanki kika mara bayan irin wannan kwamacalar a zuria guda? Duk matan duniya a rasa wacce zai aura sai wannan abar da aka tozarta ki saboda ita?" Ta kasa ce wa komai a dalilin yadda take jin an danne zuciyarta. Ga kuma sanyin da yake bin zuciyarta da gangar jikinta gabad'aya. Ya numfasa ya ce "Ki tsananta addu'ar tsari. Ina yawan mafarkin wani abu kamar tulu ya danne ki. Sannan a k'ofar Dada nake ganin abun. Na kasa gane mene ne shi." Jikinta ya sab'e da rawa. A rarrabe ta ce "ko randa ka ke ga ni?" Kai tsaye ya ce "Abu dai da ake zuba ruwa. Amma ba randa ba ce". Ta ce "Ai kuwa nima kullum sai na ga ni duk yadda aka yi akwsi wani abu a randar nan." Ta katse wayar, ta zabura ta mike ta dauko tabarya. Ta yi a'uziya, tare da ce wa "Innahu Sulaimanu wa Innahu Bismillahir rahamanin Rahim". Ta kuwa fasa gindimemiyar randar da tashi ta yi ta ganta a wajen. Dada ta fashe da kuka tana ce wa "Hauwa kika fasa mini randa ta. Kinsan ke ma kanki tare da aba ta kika gan ni. Kwanaki

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161