Skip to content

Chapter 122

Chapter 122

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

da na ba shi a zamanmu. Ya sani bai manta ba, ba kuma zai mance ba. Ni kuma na yi lamo a jikinsa na shige ya rufe ni ruf. Ina jin kalamansa suna warware dukkan damuwata. Ina sake gasgata yana sona, so na hakika. Domin ya shayar da ni kalolin kauna masu tsayawa a rai da gangar jiki gabadaya. Ya kaurara murya ya ce "Ki mini alkawarin baza ki sake barin gidan nan babu izinina ba. Ki mini alkawarin komin runtsi ba zaki juya mini baya, Asiya ki mini alkawarin zaki gasgata ni ko da kowa bai yarda da ni ba. Idan har kin tsaya mini zan yi ta samun cigaba a rayuwata. Amma idan kika juya mini baya ina tabbatar miki komai zai lalace mini ya cakalkale watak'ila ma na shiga rayuwar da tafi wanda na yi a baya muni!" Ya karasa cikin matsanancin damuwa da karaya. Tausayin sa ya baibaye ni. Na nisa na ce "Idan har ka mini alkawarin zaka kame daga kule kulen mata, zaka kiyaye dukkan iyakokin shari'a to mene ne ba zan yi maka ba Baban 2?" Ya sake tsanta rungumar da ya yi mini. Yana fad'in "Na gode sosai Asiyata". Sai kawai na ji hawayensa na sauka a kan goshina. Na shiga rudani mai yawa domin a tsawon lokacin da na shafe tare da shi ban tab'a ganin kukansa ba hana rantsuwa lokacin rikicin Rafi'a. Na ga k'walla a idonsa amma hawaye bai zuba ba . Murya na rawa na ce "mene ne?" Shi ma da rawar murya ya ce "Haka kawai nake ganin kamar duniyata ta zo karshe. Karbar filina da kamfani ya yi, yana neman zame mini fitina. To idan ke ma zaki dinga yi mini irin wannan fishin akan sabanin ra'ayi, ki dinga zargina akan abin da baki ga ni ba. Na tabbatar wata rana za'a wayi gari ne bakin cikin duniya ya mayar da ni gawa". Murya babu amo na ce "Da ikon Ubangiji hakan ba zata faru ba. Ba zan sake yi maka irin haka ba. Ka yi hakuri ". Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa, domin shi din mai son na ba shi hak'uri ne ainun. Ya sake ce wa "na sake rokon ki?" Zuciyata na bugawa ainun na ce "Ina jin ka." Ya ce "Dan Allah ki yi dukkan iyawar ki, kada ki bari yaran nan su tagayyara idan har mutuwa ta yi gaggawa ta sure ni". Ai bansan yadda aka yi ba, kuka ya goce mini mai tayar da hankali domin k'warai ya gigita ni. Maimakon ya kwantar mini da hankali sai ya sake ce wa "Na sani idan na mutu dole zaki yi aure Asiya. Domin a yanzu ne ma kika yi shekaru ashirin. Amma dan Allah, dan darajar ma'aiki ban da Jabir, ban da shi little!". Ya fada da wani irin yanayi na tashin hankali sosai. Kukan da na ke yi ya tsaya cak a dalilin tashin hankalin da ya jefa ni ya wuce kukan hawaye ko na baki. Sai kukan zuci da na gangar jiki. Zufa ta dinga yanko mini tamkar na yi tsere. Na kasa ko da motsi. Tsawon lokaci muna ta fama da sake saken zuciya da fargaba. Murya babu amo na ce "wannan ne tukuicin dawowar da na yi ko Baban 2? Haka kawai ka tayar mini da hankali. Kana nufin mutuwa zaka yi ka bar ni da k'ananun y'aya'n ka Tijjani?" Ya ce "Jikina da zuciyata ke raya mini hakan, amma ai bani da tabbacin hakan domin gaibu ne. Fatana dai ki cigaba da zama jajirtacciya ko bayan babu ni. Akwai mata da yawa da suka sadaukar da kuruciyarsu da jin dadinsu dan inganta goben y'aya'nsu. Ki kula da su, ki saka idon a kan tarbiyarsu, idan Ubangiji ya baki tsawon rai sai suma su raine ki, su ji kan ki". Na sake kece wa da kuka tare da ce wa "Kada ka mini haka Baban 2. Dan Allah ina son na rayu da kai. Ina son twins su girma a tsakanin uwa da uba, bana son na rasa ka. Kai nake fatan ya zame mini miji har a aljanna. Idan mutuwar zata dauke ni, to kawai ta hada ta dauke mu tare." Da sauri ya ce "A a In sha Allah ke zaki rayu, ki zame wa y'aya'nmu bangon jingina. Me yasa ba ki gano girman kalubalen da zasu fuskanta a dalilin rashin uwa da uba ba?." Cikin kuka sosai na ce "Allah ka jinkirta mana rayuwarmu gabadaya". Ganin hankalina ya tashi ainun, sai ya kawar da maganar ya shiga rarrashina da tarairaya ta. Amma gabadaya hankalina bai kwanta ba. Na riga da na ankara matuka da gaske. Washagari haka na tashi sukuku babu kuzari bare walwala. Ya yi shirin tafiya kasuwar Ilela. Zuciyata ta dinga ayyana mini na hana shi fita domin sai nake ganin tamkar ba zai dawo ba. Ai kuwa na fasa masa kukan ba zai fita ba. Duk yadda dinga rarrashina amma ban yarda na amince zai fita ba. Kan dole ya zauna ya fasa fitar. Ya sassauta murya ya ce "Idan Ubangiji ya so ikon sa sai na mutu a kan katifata lafiya lau ba tare da ciwon komai ba." Ina hawaye na ce "Masifa da jafa'in kake jawo mini Tijjani Allah ya yafe maka kawai. Allah yasa kai ne zaka ga gawa ta. In kuwa ba haka ba tabbas sai ka yi mini sababin hawan jinin da zai nannad'e ni na kasa moruwa". Ya numfasa bai ce komai ba, fitar da bai yi ba ke nan. Yaranmu suna ta kai komon farincikin ganina a tare da su. Mu kuma muna cikin wani irin yanayi mai wahalar wa. Kwanaki biyu na rik'e Tijjani a gida. Masallaci kawai nake barinsa ya je. Mukullin motar na boye na hana shi. Na kafe sai ya canja sana'a. Da wa'azi da nasiha da lallashi ya shawo kaina ta hanyar cusa mini tauhidi tare da gasgata hukuncin Ubangiji baya sauyawa. Kawai na dinga fahimtar maganganunsa tare da zama jaruma, mai fuskantar dukkan kalubalen rayuwa da k'arfin zuciya, sai kuma na dage da addu'ar duk runtsi Ubangiji ya tsare mini imani ya kuma shirya mini zuria. Na yarda da nasiharsa. Na ba shi mukullin motar sa. Ranar da ya fara fita, na k'ira wayarsa tafi sau goma, ina tambayar sa inda yake. Kwanaki suka yi ta shud'e wa ba abin da ya samu Tijjani. Sai na fara warware wa. Zullimin da nake ciki ya yi sauki. Yayin da shi kuma yake ta samun nasibi. Domin a yanzu ya bar kasuwa. Amma yana sarar kayan miya ya kai kasuwannin k'auyuka. Idan zai juyo sai ya saro abin da yake sauki a garin ya zo ya siyar a cikin gari. Kafin azahar ya dawo gida. Sai ya sake fito da dabarar kai da karbo sako(Delivery). Sosai yake samun alheri da harkar. Ya fara tafiya Jos ya kai kayan miya da sakonnin jama'a, idan zai dawo ya sake karbo sakonni ya kuma saro dankalin turawa da su atile. Nan da nan sai al'amarin ya karbe shi. Muka canja mu da y'aya'nmu a dalilin wadatar da yake samu. Na fara murje wa, ina haske, suturu suka yawaita mini. Mussaman material din Umm Nihla mazauniyar Malaysia. Bana gajiya da siyan yadinka ta. Saboda

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161