Skip to content

Chapter 62

Chapter 62

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

ya bada lada Dada. Amma ni bazan yi a kansa ba. Baya sona, bana sonsa. Kowa harkar gabansa yake yi." Ta dauki salati tana fa'din"Ashe har yau baku zama d'aya ba? Tisa ki yayi a gaba yake kallon ki kawai? To idan na tafi zan fara tsayawa wajen Malam Nata'ala na ji ya ya matsayin aurenku. Domin nasan duk ma'auratan da suka shafe kwanaki arba'in basu hadu ba, tabbas aure ya haranta. To ku kwanaki talatin da biyu da aurenku. Zan je na sake jin fatawar kada aje ko auren ya b'aci ba'a sani ba". Na yi shiru domin na kasa gane bayanin na ta. Ban ce komai ba, domin kuwa ban ta'ba jin makancin hakan ba. Ta numfasa ta ce "Yabi kin san duk macen da ta ki d'agawa mijin auren ta k'afa. Zata zama makamashi ne a cikin wutar jahimu?" Na yi shiru tare da b'ata fuska. Ta sake ce wa "Wannan hukuncin lahira ne. A duniya kuwa babu ita babu ganin hasken rayuwa tunda malaiku dubu maitan ne zasu yi ta kabarbari suna d'ebe mata albarka. Kin san kuwa ko limamin unguwarku ne ya tsine miki, kin yi hannun riga ke da walwalar rayuwa bare kuma ma'asumai irin malaikun Allahu". Jikina ya yi sanyi da wannan karatun na karshe. Wanda babu kuskure ko shaci fa'da a cikinsa. Amma da na tuna ai bai ta'ba nema na hana ba, ke nan bana cikin tsinuwar malaiku, sai na samu sau'kin tsoratar da na yi. Kafin ta sake magana na zabura na tashi ina ce wa "Bari na duba girikina". Na tace shinkafa, na yi k'asa da wutar na mayar. Na duba ledar da ya ajiye na ga salak da kuma ledar soyayyen kifi. A gurguje na yanka na wanke da gishiri na bar shi a kwandon tsane wa bayan na rufe. Daidai lokacin na sauke sanwar, na d'ora ta miya. Na juye a flask na fito da tukunyar na jika ta da ruwa. Na ce "Dada mu shiga ki yi kallo. Rana ta fara kusantomu. Ta ce "Zan tashi dai saboda rana, amma ba dan na yi kallon shagala ba. Na kunna na kamo mata wa'azin Malam Guruntun tana saurare can ta nisa ta ce "ya iya karatu kuwa. Amma dai wannan ba namu ba ne ko Yabi?" Cikin k'arfin hali na ce "Musulmi ai d'anuwan musulmi ne Dada. Bare wannan bijimin Malami ne. Ke dai ba ki ji abin da Allah da ma'aiki suka ce ba ne na ki?" "Ta kyabe baki ta ce"Masu daddagen wando ai tsakaninmu da su sai a lahira. Tunda suna raina karamar shehu". Dariya ta kwace mini. Na dinga yi sosai. Na canja tashar cikin sa'a kuwa sai ga sheikh Mak'ari yana bayani irin wanda ta gamsu da shi. Na gama abinci tsaf. Bamu ci ba sai da muka yi salla sannan na kawo mana. Tare ta ce na zuba mana. Muna ci tana yaba girkin nawa. Tana kuma ta yi mini maganganun da suke nuna girman da miji yake da shi. Ban ce uffan ba, sai da ta ce "Ki kwantar da hankalinki ki zauna lafiya. Nan da kwanaki ka'dan zan sake kewayo ku. Idan har kika bari kwanakin auren ki ya kai arba'in baki bari ya ri'ke hannun ki ba. Tabbas zan fa'dawa mahaifin ki. A san halin da kuke ciki. Kada ku fara zaman haranci". Na fara kuka tare da ce wa "Ba ruwan ki Dada! Kada ki ha'da ni da ubana, kada ki janyo mini fishin sa." Ga mamakina sai ta sassauta ta ce "Idan kuwa har irin haka kike gudun fishin uban ki. Kamata ya yi ki guji fishin Allah fiye da hakan. Ai ba Babanku ba ne ya hukunta faruwar al'amarin ba. Allah ne da kansa. Fishin Ubangiji akan bawansa kuwa yana nufin tabarbarewar dukkan al'amuran rayuwa". Na kasa bu'de baki na ce "Bai ta'ba nuna wa yana da bu'katar hakan daga gare ni ba. Saboda yana samu a waje. Sai kawai na sake tsananta kukan da nake yi. Domin har ciki mak'oshina nake jin ba'kin cikin halin da nake ciki. Har la'asar ta kawo kai, bata fasa sakin maganganu ba. Wasu na gaskiya, wasu na barkwanci wasu kuwa masu nauyi ne. Ita kuwa ko a jikinta. Ina kuka sosai amma bata damu ba sai ce wa ta yi "Da kin san kanki ai da tuni kin mayar da shi bita zaizai. Mata irinmu masu k'aramin ruwa ai mafi yawa murza maza muke yi. Kin ga duk haiba da siffar mijin ki. Da kin kwantar da hankalinki, kina masa biyayya, kina ba shi kanki ai wataran ma sai ya shirya zai fita, idan kika ce kada ka fita ce wa zai yi to." Na cuna baki na ce "Da dai ba dan-iskan duniya ba ne". Ta kuwa zabura ta jefe ni da kofin kusa da ita. A ki'dime ta ce "Mijin ki kika zaga kai tsaye babu nadama bare shakka? Tabbas kin kafurta, kin halaka Yabi. Dole sai kin sake karban shahadar shiga musulunci. Na kasa kunshe dariya ta. Na k'yal-k'yale da dariya sosai. Ranta ya baci k'warai da gaske. Ta shiga share hawayen takaici. Murya na rawa ta ce "Ki aikata kaba'ira sannan ki yi dariya? Saboda ku yaran yau babu darhamin imani a zuciyarku?" Na ha'diye dariyar a dalilin kukan gaske take yi. Da sanyin murya na ce "Ki yi hakuri Dada." Ta ce "Na ha'kura amma, ai dole ki sabunta musuluncinki Yabi. In kuwa ba hakan ba, tabbas kin zama arniya. Cikin k'arfin hali na ce "Ba ni kalmar shahadar na sabunta din." Ta rike baki ta ce "Wace ni na shiga sahun Malamai. Ni almajira ce me neman sani. Gaban babban malami za'a kai ki ya baki shahada ki kar'ba. Ko kuma ki yi tuba a gaban mijinki ki nemi afuwa sannan ya baki kalmar ki kar'ba". Na bata rai na ce "Haba Dada tunda ba'a gabansa aka yi ba, ina dalilin sai ya ji. Tunda kin ce na sabawa Allah. Ki bari na ce Astagafirillah! Amma kada ki fa'da masa. Dukana zai yi, son girmansa yawa ne da shi". "To shikenan bazan fa'da masa ba. Amma ki tsananta intigifari Yabi". Daga haka muka yi haramar sallar la'asar. Na tattare kwanukan na share wajen kafin ta fito daga bayi. Mun jima da idar da salla sannan ya dawo. Kallonsa kawai na yi na gane bai ci abinci ba. Dada ta dinga yi masa barka da dawowa. Ya amsa yana murmushi wanda na tabbatar na yak'e ne. Ta zuba masa ido ta ce "Ya na ganka haka ne?" Ya ce "Babu komai. Sauri nake yi kada ki ce ban zo da wuri ba." Bata ba shi amsa ba ta kalle ni. A dole na ce "Sannu da dawo wa". Ya amsa da walwala sosai". Ya ce "Na kai ki yanzu, ko na watsa ruwa?" A tausashe ta ce "Yunwa kake ji, ka fara cin abinci, nasan baka shiri da yunwa". Ya yi k'asa da kansa. Bai ce komai ba. Ta ce "Yabi ki kawo masa ruwa da abinci mana". Na daure fuska matu'ka da gaske sannan na ce "Baya cin abincina ai". Ta fara fa'din "Allahu Akbar kabiran, wa subhanallahi bukuratan wa asila. Wanne irin zama kuke yi ne na kafirci ni Binta? Baya

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161