Chapter 50
Chapter 50
ya rab'i jikina irin haka. Da muryar kuka na ce "kada ka kuma ta'ba ni. Bana son ka, bana ko son ganin ka". Ya rasa yadda zai yi da ni. Ya zauna a gefena cikin rashin abin yi. Tsawon lokaci ina shesshekar kuka. A hankali ya ce "Ko na samo miki katon baho sai ki yi wankan anan idan kin gama sai na dauke na gyara wajen". Yadda ya yi maganar sai na ji wani irin abu mai kama da tausayinsa yana neman kama ni. Na sassauta kukan nawa. Amma ban kula shi ba, bare na tanka masa. Ya sake lank'awasa harshe ya ce "Ki yi ha'kuri Asiya! A yanzu bani da halin irin gidan da kike mafarkin samu. Ban ta'ba jin takaicin ta'adin dukiyata da na dinga yi ba irin yau. Amma ina ro'kon arziki ki yi mini ha'kuri . Da ikon Allah zan yi aiki tukuru dan na cika miki burin ki. Na miki al'kawarin matu'kar rayuwata da taki ta kai lokacin da zan yi miki ginin da zai dace da ke, to ke zan bawa zabin yadda za'a fasalta ginin". Na ja tsaki na ce "Duk kana nufin ina nan tare da kai, ina kuma dakon ganin wasikar jaki irin taka?" Idonsa ya kad'a ya ce "Ni na sani Allah zai taimake ni, dan haka ba wasikar jaki nake yi ba". Na ja bakina na tsuke. Ya dinga magiya tamkar zai fashe da kuka akan na je na yi wanka. Da k'yar na yarda na tashi sai dai ban yarda na tube kayana akan idonsa ba. Sai da ya fita. Sannan na cire. Na dauko sabon zanina gyauto guda. Na daura na saka hijabi. Na bu'de akwatin da na shirya kayana a ciki. Na ciro soson wanka da sabulu da burush, hadi da makilin. Na ajiye tawul akan gadon. Na fito na tarar da shi zaune akan baranda duk jikinsa ya saki babu kuzari a tare da shi tamkar ba Bulkachuwa wanda baya barin ta kwana ba. Yana ganin na fito ya mik'e ya dauki botikin da yake gabansa cike da ruwa. Ya nufi band'akin. Na dakata ya fito, ya kalle ni ya ce "yanzu na janyo miki a rijiya da dumi tunda garin da zafi." Ta tafasa ban ce ba. Na shiga na turo kofar na sanya sakata. Ina wanka ina ayyana, ina ma a cikin daki bayin yake? Dan karami amma ko ina tayals ne. Na fahimci sabon gini ne mune muka fara zama a ciki. Sosai na yi wanka. Sai da na alwala da kuma brush sannan na fito. Na shiga daki na tarar da tsintsiya a hannunsa tabbacin shara ya yi mini. Ga gadon ya gyara tamkar gyaran mace. Daga kasa kuma kwanukan abinci ne. Ko kallonsa ban yi ba, bare na yaba masa ta hanyar cewa sannu ko na gode. Ya kalle ni ya ce "Bari na baki wuri ki shirya". Ya juya ya fice. A hankali nake shafa mai tamkar mai ciwo sannan na goga powder. Na shirya cikin sabuwar atamfa ta Buyers Batik. Doguwar riga ce amma dinkin ya yi kyau domin a Jos aka dinko mini. Gata shudiya ce sosai aka yi mata yarfen ja. Tsaya fa'din yadda farar fata ta haska atamfar bata lokaci ne. Na goga rol on din Nivea a raina sai tsaki nake yi ina fa'din da an bar ni da kwamishina ko Yaya Jabir da tuni roll on din oriflame zan dinga tu'amalli da shi dama sauran product dinsu gaba'daya. Tunda su zance a zubo mini a lefena. Na fesa turaren Far-away, na shafawa lebena jan baki mai jan duhu. Gefe na ajiye jan mayafi Wanda ya dace da atamafar. Da yake yanzu a hutar da mata bata lokaci wajen daura dankwali ana ta yin huluna. Nima hular aka yi mini. Ai kuwa na kafata a kaina na isa gaban madubi ina daidita zamanta. Ni da kaina na dinga fa'din "Fatabarakallahu ahsanul khalik'in. Sosai na yiwa kaina kyau. Maimakon na zauna sai na tsinci kaina da son yin walaha tunda na yi alwallah kafin na fito a band'akin. Na idar na tsaya ina kallon dakin. Madaidaici ne sannan kayan gadona suma matsakaita ne masu sau'kin ku'di. Amma sun yi kyau babu laifi. Labulayen sun fi komai dqukar hankalina, ledar tsakar dakin ma mai kyaun aka saka mini wacce za'a kwana biyu bata fatattake ba. Na bude akwatin na dauko wayata na kunna. Na koma bakin gadon na kishingida ina dakon ta gama daidaita. Ina cikin dube dube ya shigo shima tamkar alamara ya sanya shudiyar shadda irin shud'in atamfar jikina. Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Domin komin k'in da nake yi masa tun fil'azal nasan yana cikin yan ka'dan da Ubangiji ya yi masa kyaun fuska da kuma ciakken zati. Da walwala ya ce "Amarya kin sha kyau. Nan gaba fa idan zuciyoyinmu suka zama aminai ba karamin gidan farin ciki zamu gina ba. Tun yanzu zabin zuciyoyinmu ya zo d:aya. Mun sanya kaya iri daya ba tare da mun shawarci juna ba". Na zabura na cire hular na bu'de akwati ina laluben wasu kayan. Da sauri ya karaso kusa da ni. Ya ce "Dan Allah! Ba dan ni ba. Dan alfarmar Annabi ki bar kayan ki, sun miki kyau ainun. Ina ta fa'da miki baki zaki ta yi yau. Ni fita ma zan yi". Magiyar da ya yi ta sace mini guiwa na fasa canjawar. Ya bu'de flask din abinci ya ce "Wannan doya ce da kwai Salisu ne ya aiko mana. Ya bu'de d'ayan kuma masa ce itin tamu ta mutanan Bauchi da kuli kuli. Ya ce wannan kuma daga gida aka kawo ga kuma kunu". Yana nuna mini jug din. Ya sake cewa "Na tafasa miki shayi na dauko miki?" Ina kallonsa amma ko motsi ban yi ba bare na tanka shi. Bai yi fishi ba, ya mike ya dauko flask din shayi wanda nawa ne a cikin kaya ya dauko. Ya koma ya dauko kofina da kayan hada shayin a leda wanda alamu suka nuna siyowa ya yi. Ya zauna ya ce "Sauko to mu karya". Na sake sharewa. A hankali ya ce "Da ace kin ji nasihar da aka yi ta yi Miki, iya ta jiya kacal da kin raga mini, domin dai ko ya ya nake ni din Ubangiji ya za'ba miki ya zame miki miji. Shi kuwa miji komin kashinsa ai daraja ne da shi." Na yi kamar ban ji ba, na cigaba da danne danne wayata. Ya karya, ya kwashe kwanukan da ya yi amfani da su. Ya dawo ya ce "Zan fita Asiya. Zamu je yiwa iyayenmu ban gajiya. Nasan ba zaki yini da kewa ba yau". Ya sake cewa sai "Na dawo". Daga hakan ya juya ko uffan bai sake cewa ba. Sai tashin mashin dinsa na jiyo. Yana fita na sauko na karya. Na kai ragowar kicin. Na tsinci kaina da son karewa gidan kallo. D'akuna biyu ne a jere akan baranda. Sai kuwa guda daya daga can gefe kusa da bandaki. Sai kicin a dayan gefen. Gini ne ba laifi gashi ya sha fenti. Kan barandar ma tayals ne. Haka kicin dinma. A fili na ce "ko me ya hana a saka tayal a dakin? Na kalli yadda aka k'awata mini
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161