Chapter 129
Chapter 129
Ta saki maficin hannunta ta ruko hannuna ta ce "Ni ma matukar bai nisance ta ba Wallahi sai dai ya nemi wata uwar. Na yafe shi. Share hawayen ki har abada ba zaki yi kishi da ita ba. Na miki wannan alk:awarin". Ya shigo a sanyaye ya durkusa a gabanta ya ce "Ki tsananta yi mini addu'a. Ban san me yasa nake jin ina zakuwa akan lamarinta ba. Idan na je wajenta kwata kwata bana jin sukuni dan tsananin takurar da nake shiga. Ko ganin ta bana son yi. Amma da zarar na taho kuma sai na ji zuciyata tana azalzalar na koma Toro dan na ganta. Ku mini addu'a, ku mini uzziri dan girman Allah. Wallahi addu'ar da nake yi ne ma take saisaita mini al-amurana, amma abubuwan da suka sha kaina masu tsanani ne. Ku taimake ni, kune mafi kusa da ni a yanzu." "Tirkashi" Babah ta furta a fili domin ta fahimci ba haka aka bar shi ba tabbas. Ta nisa ta ce "Allah mun tuba, Allah kada kasa shaid'an ya yi galabar tsinka siriryar igiyar zumucin gidan marina da ta yi saura." Kukana ya tsaya cak a dalilin yadda na ga Babah ta tsorata da furucinsa ainun. Yayin da zuciyata ta shiga zullimi sosai. Ke nan Tijjani da gaske yana burin auren Nasiba. Wani irin k'ullutu mai ciwo ya tokare ni. A matukar sanyaye take fad'in "Zan dage da addu'a, kai ma ka dage da addu'ar da kuma danne yadda kake ji akan lamarinta. Sannan ka saka a ranka ba matar ka ba ce, domin matukar ina raye ba zaka had'a su ba, kai gabadaya ne ma ba zaka aure ta ba. Dalilin da ya hana a baka ita a farko, shine dalilin da yasa ba zaka zama mijinta ba a yanzu" Ta juyo gare ni ta tausasa harshe ta ce "ki yi hakuri kin ji Yabi. Yana cikin canka cakare. Ki tallafe shi har ya tsallake wannan siradin. Mutanan yau da yawansu mugaye ne, zuciyarsu cike take da gilli mai yawa." Na kasa ce wa komai domin na kidime, idan har Tijjani da yake kawaici a gaban Babah zai bude baki ya ce yana zakuwa akan lamarinta a gabanta to lah shakka abin da yake ji babba ne. Hawaye ya dinga tsere a fuskata. Tabbas ina cikin tashin hankali. Bana jin tsoron karawa kishi da ko wacce mace, domin na yi imani namiji baya zama da wacce baya so. Idan kishiya ta kere ka a wani fanni to kai ma da ikon Ubangiji sai ka samu fannin da zaka kere ta. Abu biyu ya dame ni. Nasiba suntumemiyar halitta ce irin matan da suke birge Bulkachuwa. Sannan mahaifiyarta kowa yasan bata barin mazanta haka, a hannunta suke, ko marigayi mijin Nasiba kullum a yunkurin mallake mata shi ta ke. Na tabbatar Tijjani ma za'a yi komai dan ta sha gabana, tunda a yanzu ma da bai aure ta ba idan ta gan ni kamar ta doke ni haka take ji. Da k'yar Babah ta shawo kaina na samu nutsuwa, na daina kuka. Sai yamma muka baro Bulkachuwa. Dan haka sai dare muka iso. Na daure na yi k'arfin zuciya ban cigaba da share shi ba. Na rungume shi da hannu biyu muka cigaba da zama lafiya. Duk dare kuma sai ya fita waje ya yi waya. Idan kuma yana gida baya amsa waya matukar bata shafi kasuwancinsa ba. Asalima kamar ya dakatar da a a kira shi idan yana gida ne. Da kaina na fahimci da gaske ya canja, wulakancin yin waya idan yana gida yanzu ya daina, asalima kaffa kaffa yake kada na tuntsire masa. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633*. Yayin da ni kuma na tsananta addu'ar Ubangiji ya tsaremu akan duk abin da ake nufi da mu na sharri. Sa'a d'aya har yau Tijjani bai bar sallar dare ba. Yana wahalar gaske ya kwanta bai tashi ya yi nafila ba. Kullum kuma a cikin addu'ar duk kaddarar da zata hau kansa ta zama mai sassauci daga Ubangiji. Na sani asiri zai kama shi, amma na yi imani zai zo da sauki tunda wadatar da ya samu bata sanya ya bar Allah ko ya koma BAK'AR TA'ADAR neman matan da ya yi a baya ba. Na kira gwaggo na fada mata komai na roki ta tsananta yi mini addu'a. Cikin rarrashi ta ce "Ina yi miki Yabi. Zan kuma ninka addu'ar da ne yi miki. Abin da zan fad'a miki shine ki barwa Allah ya yi miki zabi, ba wai ke ki yanke hukuncin idan ya aure ta kin bar shi ba. Allah ne ya halasta dan haka akwai bukatar ki nutsu, kada ki bari Ubangiji ya bar ki da dabarar ki." Da kuka na ce ",To Gwaggo". Cikin rauni ta ce "Allah ya yi miki albarka ya shiga tsakanin ki da duk abin da zai birkita miki auren ki. Da ikon Allah ba za'a kai ki k'asa ba. Kin yi sa'a kina cikin albarkar uwa da uba. Dan haka ki yi ibada tuk'uru ki kuma yi barci da minshari ba abin da zai same ki sai alheri da ke da dukkan zuriar ki Yabi". "Na gode Gwaggo". Na furta cikin rawar murya irin ta kuka. Sannu a hankali na samu sassauci na cire hankalina kan maganar Nasiba da Tijjani. Iyaka dai ban daina addu'a ba, ban daina tofawa Tijjani addu'ar tsari a cikin duk abin da zai ci ko ya sha ba. Na rungumi zaman lafiya a tsakanina da shi. Na rungumi karatuna da y'aya'na. Mussaman a yanzu da nake gaf da kammala N.C.E. Twins sun girma domin suna shirin shiga shekaru shida da haihuwa. A lokacin suna aji daya na firamari. Hanif yafi Hamim kokari domin kullum na daya yake zuwa. Amma kuma ba shi da magana. Yayin da Hamim yake zuwa tsakanin bakwai zuwa goma. Amma kuma ba wanda bai san shi ba, saboda suruntunsa, ya kuma yi sa'a ya iya turanci. Kamar wanda ya girma a cikin masu yi. Surtunsa da fadansa ya sanya a ke fafatawa da shi. Sau tari sai ya yi tsokana ko laifi a hukunta Hanif a madadinsa tunda ba'a gane su. Shi kuma Hanif ba zai ce ba shi ba ne. Ko ni ma yana mini wannan iya shegen. Dan haka na daina binsu a guje. Sai ya manta yana ta surtunsa kamar aku sannan zan rik'e shi. Duk sadda na je Toro bin mu kawai ake yi da ido ni da y'aya'na a dalilin yadda muke fita daban muke daukar ido. Wadanda kuma basa iya boye wa hassadarsu a fili sai da kawai na ji suna fad'in iyalin babban direba shugaban masu kayan gwari na Bauchi gabad'aya. Ko yaushe aka nada masa wannan mukamin? Ni da Nasiba kuwa muna gaisawa, bama gaba sai dai babu doguwar hira. Domin idan ta gan ni sai na ga tana d'ad'are wa bata da katabus duk da bata yi mini kallon raini ko na izgili. Shi yasa nima nake jarumtar mu'amalantar ta da sakakkiyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161