Chapter 153
Chapter 153
gurbinka! Dakina a bushe, babu kayan shayi irin naka. Babu sabulai da turaruka irin naka. Ta hau kuka sosai. Jikinsa ya yi sanyi. Ya ce su Baban Kasuwa basa siya miki ne?" Ta ce "suna siya amma har sai sun k'are, kai kuwa kafin su k'are ka kawo wasu. Sabulai da turare masu kyau ba masu s'aukin kudi ba. Amma yanzu fa?" Ya ce "Ammar da Jabir basa yi miki ne Dada?" Ta kyabe baki ta ce "Jabiru kam ai yanzu fama yake yi da kansa. Har ya gama samun damarsa kuwa ban wani more shi ba. Kasan sun k'ullace ni akan ku. Wai nafi sonku. Iyayensa kawai yake yiwa. To yanzu an yi mutuwar kasko, kowa ma ya rasa. Shi kuwa Ammar yana yi mini bazan masa k'aharu ba". Amma sai ta waiwaya ta sassauta murya ta ce "Da uwarsa muke raba daidai. Idan ba'a hannuna ya bani kudi ba kuwa, basa zuwa mini". Ya yi shiru, tausayinta ya kama shi ainun. Abin da ya fahimta Baban Marina da mahaifiyarsa sun fi dukkan y'aya'nta yi mata biyayya da kyautatawa a gareta. Sune kuma wadanda ta rayu tana nuna musu rashin soyayya. Komai sune a baya. Amma kuma shi da kansa ya tabbatar Dada tafi sonsa akan kowa cikin jikokinta. Domin Ammar bai samu sukunin yi mata raddi da fito na fito da ita ba. Da ace shine yake da nutsuwarsa da bai san yadda zata ririta shi ba. Ya tuna sadda zai sadada ya kwashe mata yan kobbonta da kayan amafaninta ya siyar. Bata yi masa fada a gaban jama'a. Bari take sai dare ya raba kowa ya kwanta sannan ta shiga dakinsa su yi sababi, tana yi kuma tana ce wa murya kasa k'asa mai sunan manya kada a gane halin da muke ciki. Shi kuwa sai ya bude muryarsa ya ce "Aji mana tunda sharri zaki k'ala mini saboda kin washe ni. Duk yawan jama'ar gidan nan m, babu mai yi miki sata sai Tijjani! Nan da nan zata bar maganar ta ce "Alfarmar shehu zaka bari. Darajar sunan da ka ambata na yafe maka, Allah ya shirya mini kai, ya tsare ka daga hau da sharrin zamani". Ya nisa ya sake murmusawa ya ce "Ki yi hakuri zan fad'awa Aliyu ya dinga yi miki. Ki kuma cigaba da yi mini addu'a Dada. Sannan ki yafe mini ta'adin da na yi miki a shekarun baya. Da azama ta ce "Wallahi na manta komai. Kuma menene baka yi mini ba da ka samu dama? Aliyu kuwa ai shima a k'ullace yake da ni. Ya sha fad'a mini ina nunawa uwarku butanci. Wanda sharri ne kawai, to wa zai haifi d'a ya ce baya sonsa saboda Allah? Jiya kuwa a gidanka ya ce "Yasan nafi sonka a kansa. Sannan kasan matarsa d'iyar Alhaji ce, su kuwa gabadayansu sun kwashe kayansu a gaban ma'aiki akan sha'anina. Yabi ce kawai take mini sassauci, itama dan tasan ni da kai ba dai mutum ba. Duk tsiyatakunta, duk yadda ka jarabtu a kanta, ba zaka k'i jin kaina ba, ba zaka k'i ni ba! Ta fad'a cikin sigar tausayi. Ya saki gauron numfashi ya ce "Ki yi hakuri Dada. Za'a gyara. Yanzu ki daina damuwa. Sannan kada ki koma Toro. Ki zauna anan BAUCHI ki dan huta. Idan jama'a sun tafi zansa a kawo miki kaji Babah ta gyara miki, ki dinga cin abin ki. Idan sun kusa karewa za'a sake soya miki wasu. Sannan yanzu a hanya za'a siya miki kayan shayin ki, ki ajiye a wajen ki. Naki ne ke kad'ai kada Yabi ta yi miki k'auron nata". Ta yi maza ta ce "A a itama tana yi mini alheri, sannan tunda aka sakaye ka soyayya ta sake kulluwa a tsakaninmu, kullum muka hadu sai mun yi kuka. Kasan yanzu ta yi hankali. Gara na fad'i gaskiya ko ba haka ba". Ya yi dariya ya ce "Ho Dada ta Yabi. Tsoron ta kike ji ne yanzu?" Ta rausayar da kai ta ce "Uum kaidin mata mai yawa ne. Yanzun nan idan ta murde kai ma sai ka juya mini baya a kanta. Barta dai tunda ta nutsu, kuma tana mini ya kamata. A lallaba a tafi a haka, domin na riga na yi imani da kiararin da na ji ubanta yana yi mata. Na ce wa ita kad'ai gayya ce a gidan Marina. Ko kasan kaf zuri'ata babu mai ruwan kudi a hannunsa irin Yabi? Yadda na gasgata karamar Shehu haka na gasgata kudinta na halali ne. Ka ga yadda ta mayar da dakin uwarta ne? To ragowar matan uban ma duk ta yiwa dakunansu kwaskwarima lokacin auren Ubaida. Idan ka ga bajintar da ta yi a auren kuwa sai ka rik'e baki. Matar gwamna har tawaga ta turo su wakilce ta a bikin. Kofarsu tafi ko ina haske da kyawu yanzu, kuma duk ita ce. Ko kai ma irin yadda kake yiwa ubanta ai saboda ita ne. Yabi, Yabi duniya ce? K'aramar halitta sai babban al'amari". Ya kwashe da dariya ainun. Ta ce "Allah kuwa. Mata ai yanzu sun ri'ka. Idan basa yin ka to mijinsu ma ba zai maka kallon rahama ba". Ya sake yin dariya ya ce "Duk zan fad'a mata ne". Ta kyabe baki tare da ce wa "To hudawa cikinka wuka da kanka. Ta jima kafin ta dingisa ta tarar da su a mota suka tafi. ** *Watanni uku a gaba* Zuwa lokacin Husna ta yi gubibi da ita. Shayarwa na matukar ciko da Yabi . Saboda kirjinta suna cika, ita kam tana cikin mata kad'an da goyo yake karbarsu. Bata da matsalar komai sai ta rashin miji. Har zuwa lokacin Dada na tare da su. Ba zato ba tsammani Aliyu ya zo ya kwashe su aka yi musu passport. Sai da passport ya fito yake fad'a musu kudin hayar filling Tijjani ne. Shine kuma ya ce Yabi da Dada su tafi su yi Umrah su yi masa addu'a." Ai kafin ya rufe baki Dada ta zabge da kuka tare da ce wa "Ashe zan koma gabar ni Binta? Hauwa kin iya haihuwa! Shehu ya haifu. Allah ka yiwa Shehu abin da mai zato bai yi zatonsa ba ". Sai kuma ta rushe da kuka wurjajan. Aliyu ya ce "Ganin hakan ya sanya na biyawa tawa uwar sai ku tafi tare" Nan ma Dada ce ta yi fit ta ce "Wayyo Ali Allah ya yi albarka, yasa kai ma ayi maka tagwaye." Ya ce "Ai tuni ya bani Dada. Wadannan da suke gittawa ta gabanki ba nawa ba ne? Ko kuwa dan a gidan Marina kowa d'an da ya haifa ne nasa shiyasa kike ganin sai na haifi wasu tagwayen?" Da yake babu wata shak'uwa a tsakaninsu, asalima tsoro tsoronsa take ji. A sanyaye ta ce "A a kuskure ne, da mantuwa Ali. Yanzu dai ba zamu yi fad'a ba, bayan ka zo mana da babban albishirin da babu irinsa. Allah ya saka da alheri, ya yi muku albarka gabad'aya". Ya ce "Ameen". Babah itama ta yi masa godiya da fatan alheri da bunk'asar arziki. Yabi tana bude baki ta ce "Na dad'e ina son na tura Baban Marina Umrah. Na dad'e ina fatan na yi masa ba zata. Ta ce zan tattara abin da nake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161