Chapter 12
Chapter 12
lafiya da nisan kwana mai albarka. Na gode sosai". Duk muka yi shiru kowa na cikin alhini. A hakan Nazira ta fito rai a bace da gani Mama sababin yadda ta like mini ta yi mata. Kusa da ni ta zauna, cikin sanyin murya ta ce "Sannu Baba". Murya ba amo ya ce "Sannu kadai Nazira, Allah ya kara miki ha'kuri kin ji. Ki cigaba da jajirce wa a kan gaskiya ko da hakan ya ci karo da ra'ayin kowa, ku so junanku, ku binne a tsakaninku, kin fi Yabi ha'kuri, a duk sadda kika ga zata yi aikin nadama yi amfani da fikon da kika yi mata ki dakatar da ita, komin runtsi kada ki bari ta dauki hukunci cikin fishi. Ke kuma Yabi kul kika ki jin shawararta, idan ta ce yi ha'kuri, to na roki ki bar abin nan komin girmansa. Ina jaddada muku ne dan ku ri'ke su da kyau, ko babu ni idan kuka ri'ke maganganuna ba zaku ta'be ba. Allah ya yi muku albarka ya ha'da ku da maza na gari, ya raba ku da sharrin shaidan a cikin zumunta". Muka amsa da Ameen amen cikin sanyin jiki. Nazira ta mika hannu ta karb'i Maficin hannun Gwaggo ta cigaba da yi masa fifita, duk da gumin ya yi sau'ki. Har lokacin kuma bai saki hannuna ba. Ya jima kafin ya saki hannuna yana sake cewa "Na hore ki da ha'kuri Yabi! Ku zauna da yan'uwana lafiya, ku mutunta su, ku gaishe su da girmama wa". Na gyada kai yayin da Nazira ta ce "Duk yadda kake so hakan zamu yi, amma ka taimake mu ka daina sanya damuwa a ranka Baba! Fatanamu mu ganka a tsaye akan kafafuwanka, idan muna ganinka cikin walwala ba abin da zai dame mu sosai." Haka muka kwanta ni da Nazira tana ta jan kunnena na kiyayi Dada, tunda zata iya yin ha'din kitifo har ya zama sanadin da za'a samu damar cin zarafin Babanmu akan idonmu. Tun daga wannan ranar na kame bakina a gaban Dada, duk karatun da zata yi bana tankawa, haka nan ban cika zama na yi doguwar magana da ita ba. Zanje gaishe ta babu fashi, kuma sai na tabbatar mun ha'da ido sannan zan kama sunanta na gaishe ta. Na daina jan magana a tsakaninmu ne kawai. Sannan na soke zuwa hirar dare, amma matu'kar zata d'ora karatu sai ta sa an kira ni. Janye war da na yi da ita kuma sai ya dame ta, amma ta kasa bu'de baki ta yi magana. Tunda Nazira ma ba wani sake wa take yi ba, balle ta yi mata korafi. *** Karshen wata Yaya J ya dawo. Mun taso daga Islamiya muka ganshi zaune akan dandamalin kofar gidanmu. Sanye yake cikin kananun Kaya da suka yi matu'kar kar'barsa, sai kamshin turaren Dagmar yake tashi sannu a hankali. Dukkan y'anmatan suka hau rige-rigen gaishe shi, yayin da ni na sunkuyar da kai kasa alamun kunya. Na zo wucewa ta gefensa na saci kallonsa ai kuwa karaf muka hada ido, wani irin abu ya tsikare ni, kwalliya da tsabtar Yaya J ko mace ce ta kai a sata a masu tsabta, sannan kankantarsa tana sawa na ji mun dace da juna. Domin da ka'dan ya zarta ni cika ido da tsayi. Babban abin burgewa mai nutsuwa ne, sannan mai ha'kuri ne, bashi da hayaniya ko ka'dan. Da sauri na janye idon nawa, murmushi yana subuce mini wanda ban shirya yinsa ba, na tsananin shauki ne. Na wuce ba tare da na yi gaisuwar ba. Cikin raha ya ce "Nasiba ki koya wa Asiyan Toro gaisuwa tunda ta zama bak'auya". Da dariya ta ce "Yaya Jabir kaine da fa'din Asiyan Toro yau? Babu ruwana a shirginka da Yabi". Ya k'yal-k'yale da dariya ya ce "Tsoron ta kike ji ne Nasiba? Kin fita tirinya fa, to kuma ya za'a yi ne tunda ku biyu zan ha'da na aure rana guda?". Ta yi maza ta ce "Lallai kuwa ka shiryawa darun Yabi domin har ka tafi ba zata saurare ka ba, ni kuma ba zan taya ka rarrashi ba". Ta wuce ni da sauri ta shige shashin Dada. Ni kuma na wuce shashinmu a dalilin yau Nazira ba ta samu damar zuwa ba, saboda tana fama da ciwon mara. Zuciyata har wani tukiki take yi na tsananin bacin ran kalaman Yaya J. Wai zai ha'da ni da Nasiba ya aura. Na yi tsuka na ce "Sai dai ya aureta ita ka'dai. Dama na san dunbula dunbulan kirjinta na iya tafiya da shi, ba'kin ciki ya sake turnike ni a dalilin ni ba mai cikar k'irji ba ce. Har yanzu bana saka breziya sai dai half best, domin a manne suke a kirjina yan kananu da kadan suka fi tsakuwa. Amma Nazira da Nasiba kam kirjinsu a cike yake sosai. Wataran har rayawa nake yi ko dai na fara shan ruwan baru ne ko zan yi sa'a su fito su cika mini kirji ni ma. Amma sai na kasa, mussaman da sai na ro'ko ruwan kuma sai nake ganin kamar za'a gane dalilin shan da zan yi. Da daddare ya dinga aiken na zo amma na yi mirsisi na ki fita. Washagari a zauren Dada na tarar da shi. Na sani sammakon tashi ya yi dan ya hadu da ni. Domin shi ba ma'abocin tashi sassafe bane, da zarar ya dawo daga sallar asubahi idan ya kwanta sai tara yake tashi. Nazira ta gaishe shi ta shige, yayin da na dauke kai fuska murtuk zan wuce shi. Ya yi maza ya sha gabana yana fa'din "Haba Yabin J baki san wasa ba ne? Na yi bakam tamkar dai ban fahimci da ni yake magana ba. Na yi kasa da kaina. Ya sassauta murya ya ce "Yanzu Ashe zaki iya mini irin wannan fishin Yabi?" Na dago na kalla shi na ce "Oh wai ka yi zaton ba zan iya ba? To kuwa ka dauka zan yi maka fiye da hakan domin zan iya shafe babinka gaba'daya." Ya jima yana kallona cikin ki'dima. Ya yi k'arfin halin cewa "Me ya yi zafi haka, daga wasa?" Na sake d'aure fuska na ce "Bansan wasa ba, ban iya shi ba, ban kuma ta'ba daukan al'amarinka a matsayin wasa ba, bare har na yi maka tsokanar da zaka ji ka tozarta". "Hakane, na kuma gasgata ki, yanzu ki yi ha'kuri ba zan sake miki irin hakan ba kin ji". Na jijjiga kaina tare da yin wata irin shakiyar dariya na ce "Ha'kurin ma ban iya shi ba. Ba kuma zan koyo shi a dalilin cin fuskar da aka yi mini ba. Na riga na barwa Nasiba kai, dan haka ka manta da wata Yabin Marina". Ya yi tsam cikin kaduwa wata'kila yana mamakin yadda kishi yake kutsowa tunda ga kasan zuciyata ne, kallon yarinya k'arama yake yi mini, sai dai bai san yar shekaru goma ma zata yi kishin abin da take so ba, bare ni da nake da shekaru sha sha biyar, na ke harun sha shida. Ya lankwashe murya cikin rarrashi ya ce "Ai na yi zaton ina da wata alfarma ta daban a wajen ki, ban ta'ba zaton zan yi miki laifin da zaki shafe ni a zuciyar ki ba. Yau
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161