Chapter 18
Chapter 18
ya sarrafa taki ta zama mai sassauci da afuwa". Kuka ya k'wace mini sosai ina cewa "Ameen Gwaggo". Ba komai yake sanya ni d'imuwa ba irin maganar Baban Tsakiya. Maganarsa ishara ce akan aurena da Yaya J ba zai yiwu ba. Zuciyata ta yi nauyi ainun. Na shiga rud'ani mai yawa, na sani idan har zan yi aiki da lura kamata ya yi na nisanci d'ansa tunda har yake neman maraba da ni a cikin gidanmu, ina kuma ace na zama cikin ahalinsa? Mutumin da bakinsa yake ambaton jaje da alhini ga ahalin wanda d'ansu zai kwashe ni. Bansan yadda aka yi ba na tsinci kaina da fashe wa da matsanancin kuka. Saboda fishin Baban kasuwa ya sanya Baban Tsakiya tsayawa ya mini irin wannan tozarcin da zai yi wahalar gaske na sake ganin girmansa. Na samu kaina da tambayar anya kuwa Babanmu ba dan uba ba ne a tsakaninsu? Sai nake ayyana ai ko y'ay'an Baffanni suke (cousins) bai kamata su dinga yi masa irin wannan kaskancin ba, dan kawai sun fishi wadatar abin duniya. Balle kuma girman nasaba irin ta uba guda, sai dai kuma babu haufi cikinsu daya ma'ana Dada ce ta yi nakudarsa tun gabbannin a yi tasu. Babban farin cikina d'aya, bai rasa wadatar zuciya ba, tunda duk tsananin wahala ba zai bu'de baki ya ce su taimake shi ba. Idan sun yi niyya akan kansu sun yi masa kyauta to zai kar'ba, amma idan zamu kwana mu yini bamu ci ba, ba dai ya ce wane ga halin da nake ciki ba, sai dai idan ya'yan cikinsa ne. Har ya k'wammace ya fa'da wa aminisa Alhaji Tanimu tsananin da yake ciki, ya tsananta. Matu'kar kuma zai fa'da masa to kuwa zai sauke masa buhun masara, dawa, dana gero. Sau tari kallon wadatar da ake yiwa su Baban Kasuwa yake hana masu k'arfi tallafa wa Babanmu. Sannan mutanan yau suna da dabi'ar k'in taimaka wa matu'kar ba ro'konsu ka yi ba, yayin da mafi yawa aka fi taimako da azumi, shima fake wa ake yi da sunan neman lada alhali a ku'din zakkar da Allah ya wajaba a fitar ne suke siyan kayan abinci suna rarraba wa. Oh mutanan yau mun rungumi *Bakaken Ta'adodi* daban daban. Allah ya shirye mu kawai. Muryar Inna na ji cikin sigar umarni ta ce "Ki cire Jabiru a ranki, nasan zai yi matu'kar wahalar gaske wannan al'amarin bai zama sanadin yin shamaki a tsakaninki da shi ba. Ina son ki ninka jarumtar ki, tun kafin su miki 'kwalele da shi." Kafin na bu'de baki sai ganin Baban Marina muka yi ya shigo a fusace yana fa'din "Ina Asiya?" Da rawar murya na ce "Ga ni Babanmu". Ya ce "zo ki fice ki bar mini gida tunda har zaki iya tsaya wa gar da gar ki zagi Badamasi da Iliya akan idonsu. Ai bansan zaki iya irin wannan dib'ar albarkar ba. Na dauka abin naki akwai lissafi a ciki amma tunda kina ganin idan kin yi karo tsakanin kwai da dutse zai miki daidai sai ki je ki yi a wani gidan, amma ba a nan ba. Ban haifi d'an da zai zagi dan-uwana akan idonsa na bar shi ba. Na sha fa'da miki babu ruwan ki da shiga tsakanina da y'anuwana. Amma sam kin k'i ji" Cikin kuka na ce "Ka yi ha'kuri Babanmu! Ba yadda aka fa'da maka al'amarin ya kasance ba. Ban zage su ba, har abada kuma ba zan zage su ba, kada ka kore ni a gidanka, zai iya zama sanadin tabarbare war al'amura masu yawa, ka mini dukkan hukuncin da zaka gamsu. Ka taimaki kanka, ka kuma tserar da ni fa'da wa halaka akan wad'anda basa nufin ka da alheri". Ya jijjiga kai ya ce "Yabi ki yawaita hamdala da baki zo a cikin mutanan farko ba, lah shakka da irinku ne masu kafiya akan ra'ayinku ko da ya ci karo da gaskiya. Na ji ba zan kore ki ba, amma dole ki yi nisa da gidan nan tun ban fusata na miki baki ba, tunda ba'kin cikin da kika cusa mini a sanadin musayar yawun da kika yi da iyayenki ba mai sau'ki ba ne, akan kannena mahaifiyata take mini mugun baki. Yabi kibi a sannu fa." Na sake tsorata na ce "Àllah ya huci zuciyarka Baba, Allah ya shiga cikin al'muranka, ya iya maka da iyawarsa". Nan da nan ya sauka ya hau fa'din "ameen". Gobe ki shirya ki tafi gidan Salisu har sai na nemi ki, saura can din ma ki nemi gigita masa zaman lafiya a gidansa, dan nasan zaki gano masa laifukan da iyalinsa take yi wanda shi yake yin uzziri a cikinsu". Na yi kasa da kaina na kasa cewa komai. Washagari kuwa Gwaggo da kanta ta shirya mini kayana a ledar biba tana ta jaddada mini idan na kuskura na yi rikici da matarsa to ba tantama da ita na yi. A sanyaye na ce "Komai zan ga ni zan runtse idona babu ruwana, ko da kuwa zata tsokane ni." Wani irin salama ya shiga Gwaggo ta dinga fa'din "Yauwa Yabina Allah ya sassauta miki". Anas ne ya fara yi mini gaba da kayana. Yayin da zamu tafi da Nazira da Iki idan anjima. Nazira sai kuka take akan tafiyar da zan yi na barta. Na yi shirin zuwa gaida Dada wanda rashin zuwa wannan gaisuwar ba k'aramin abu take mayar da shi ba. Babu kuzari na ce "Nazira mu je mu gaida Dada". Ta girgiza kai tare da cewa "je ki kawai, bana jin dadi anjima na leka". Na ce "Tom na tafi, ina jin da'di tare da k'arfafa wa kaina guiwar ko na rasa soyayyar kowa a fuskar zumunci ina da yakinin ba zan rasa soyayyar Nazira ba. Tana sona fiye da zatona, haka nima nake sonta tamkar yadda nake son shakikiyata Yaya Ummi. Tun daga bayan katangar Dada nake jin tashin muryoyinta da na Ya'yanta Na karasa har cikin soron sosai na dinga jin kumfar bakin da Baba Maryo uwar Nasiba take yi akan ba zata ta'ba yarda a dauki Nasiba a bawa Tijjani ba. Kuka take yi wiwi. Tana cewa "sai dai a ga laifina a banza, amma wannan ha'din ba mai yiwu wa ba ne." Yayin da Babah ta Bulkachuwa take fa'din "Ai ban ga laifinki ba, gaskiyar magana kika fa'da. Kuma dama mutum shi yake mutunta kansa, da ya nutsu ya zama mutumin kirki ina ce a ko ina zai nemi aure a ba shi?. Yanzu kuwa da ya zama abin da ya zama a cikin danginsa ma gudunsa za'a yi bare a waje". Dada ta ce "Ya isa haka, ba cece-kuce zaku yi mini ba. Na rufe wannan maganar, na yi zaton auren nasa da ita zai kawo masa dai-daito tunda tana sonsa, idan aka yi sa'a sai ya shiryu, ruwan wankan aure ka'dai maganin wanda ko wacce suka fand'are ne. Amma tunda abin zai zama tashin hankali a bar maganar haka nan Nasiba ba matarsa ba ce." Kafin na yi wani motsi sai jin muryar Baban Tsakiya ya yi yana fa'din "Kazalika wannan yar iskar yarinyar ba matar Jabir ba ce, ko bayan raina idan aka bari ya aure ta Wallahi Allah ya isa, na fa'da a gabanku, kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161