Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,243 words 0 views Progress saved
Download Book

fa sai da kuka tsaya da yaron nan dan gidan Sarkin k'ofa ko?". Na yi murmushi na ce "Ai dai baka ji me na ce masa ba". Na fa'da cikin shagwaba shagwaba. Ya sake yin kasa da murya ya ce "Ban ji ba, amma yanzu fa'da mini na ji". Na yi k'asa da kaina na ce "Na fa'da masa cewar ni bana sonsa akwai wani bawan Allan da ya riga shi yin wuf da zuciyar Yabin Marina". Ina kallonsa ya dan murmusa ya ce "Waye wannan bawan Allan?" Na dago amma ban kalle shi ba a dalilin hasken kwai na kanmu. Na juyar da fuska na ce "Yaya J mana". A wannan karon murmushi mai sauti ya yi. Ya nisa ya ce "Yauwa Yabin J, kin biya ni. Amma idan kina son ki burge ni, ki daina ma sauraronsa ba shi kawai ba, kowanne namiji ma. Sannan ki daina fa'da dazu ma sai da kika yi dambe da Saratu. Kin ta'ba gani na ina dambe?" Na girgiza kai tare da cewa "Ha'kuri ne ya yi maka yawa, ni kuwa bani da shi, domin duk wacce ta ta'ba ni ba zan k'yale ba" Ya girgiza kai ya ce "Ha'kuri fa falala ne da shi Yabi". Na girgiza kai na ce "To ka dinga yi mini addu'a na shiga sahun masu ha'kurin domin kuwa ni duk wanda ya ta'ba ni idan ban rama ba sai nake ganin na zama sullutu". Ya murmusa sosai domin ba mai dabi'ar k'yal-k'yala dariya ba ne. Ya zuba mini ido ya ce "Wai Goggo ce ta haife ki, al'amarin Ubangiji da girma yake. Waton idan kika rama baki zama sullutu ba?". Da hanzari na ce "Ras Yaya J domin dai kai din shaida ne na yadda ake kaffa kaffa da ni, da duk kayana". Ya zuba mini ido ya ce "Allah ka sanyawa Yabi ha'kuri da juriya, a mayar mini ita ta zama mai shanye dukkan kalubale da ha'kuri da kuma kawaici". Na ce "Gaskiya Yaya J kada mu yi haka da kai, roka mini na zama yar gwagwarmaya mana, sai kawai ka roka mini na zama mai ha'kuri komai aka yi mini sai dai na yi kuka, ko ya yi ta cina a zuciyata, watarana sai dai kawai a budi ido aga Yabi ta ha'du da jinya ko ta mace ma gaba'daya. To ni ba zan zama hakan ba". Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kinsan darajar ha'kuri kuwa Asiya?" Na kalle shi domin bai cika fa'din zahirin sunana ba, tunda ya fahimci ina son inkiyata ta Yabi shi kenan ya wajabta ma kansa fa'da mini duk da dai yafi son Asiya. Domin an sha dakuwa da ni akan ce mini Asiya, ina ganin duk wanda ba zai ce mini Yabi ba, to hassada yake yi mini, tunda an yi dawafi da ni a ciki, an yi tsayuwar arfa da ni, an yi jifan shaidan da ni, an yi sa'ayi da ni to mene ne na tauye mini Hajjin?" Ban bashi amsa ba ya ce "W anda Ubangiji ya masa baiwar ha'kuri to ina tabbatar miki an ba shi arzikin duniya da lahira, ba kuma abin da ba zai cimma ba a rayuwarsa, daure ki zama jaruma amma ba jarumtar rashin ha'kuri ba". Na girgiza kai ina murmushi domin dai ban gamsu ba. Har yau da na fara mallakar hankalina ban ga ribar ha'kurin da mahaifiyata take yi ba. Ban ga ribar kawaici da ha'kurin da mahaifinmu yake yiwa zumunci ba. Ban ga ribar ha'kurin da Yaya Ummi take da mijinta da uwargidanta ba. Tunda har yau ita ce a wahale, kuskure ka'dan zata yi ya mata tijara a tsakar gida a gaban kowa tamkar ba ita ce mai k'uruciya ba. Dan haka na k'udire a raina ba wanda zai nemi ta'ba ni, na k'yale shi, zan yi komai dan na tabbatar ban bari na zama gajeriyar katanga mai da'din k'etara ba. Yanayina ya tabbatar masa ban yarda zan iya yin hakan ba. Ya girgiza kai ya ce "Ai shikenan sai dai zan cigaba da yi miki addu'ar dace wa da babban arzikin duniya wato Ha'kuri". Na yi dariya na ce "Dama addu'ar na zama hamshakiyar y'ar kasuwa kake yi mini, ta yadda kasuwacina zai d'auke mini hankali daga dukkan wani rashin ha'kurina da kake ga ni". Da sauri ya ce "Ina yi miki Yabina! Da ikon Ubangiji komai kika kasa sai kin sayar, kullum sai na roka miki Ubangiji ya baki dauwamammiyar sana'a da zaki tsufa kina cin gajiyarta". Da'di ya kama ni, domin Yaya J ne kawai ya fahimci irin yadda nake son na zama shahararrriyar y'ar kasuwa. Ya miko mini tsarabar Jos leda biyu da ya ajiye a bayan k'yauren shiga shashinmu. Na karb'a ina godiya sosai. Na tabbatar Atile ce da kuma turare, tunda sune abu mafi soyuwa a mini kyautarsu. Fahimtar hakan da ya yi, sai ya dimanci yi mini tsarabarsu. Shine ya fara koya mini amfani da turaren Far-away. Daga haka muka yi sallamah. Kai tsaye dakin uwata na nufa ban koma wajen Dada ba. *Akwai kayayyakin gyara mace sosai irin na kasar Chad.* *Akwai maganin sanyi sadidan* *Ku tuntube ni a wannan lambar* *08032773332.* ✍️ *BAK'AR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)*. *Marubuciyar* *Halin Yau* *Sabo da kaza* •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYERS* https://www.wattpad.com/1381521145? utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_published&wp_page= create_on_publish&wp_uname=SurayyaIbrahim1&wp_originator=2c15XL0D2bIzHhiZQM1Ufz9MWP lKieRkWxJuGH2P9gX0b9XHQk5Jym8fxiz%2BPI0TAhOUhwh2GWl2lunKDNI2ObmS%2B%2FfL1BUVY3%2Ft %2BNKg%2B0D0iEZNLOPdWH9AZxOaGd51 https://arewabooks.com/book?id=64e93a53984f91b3605ae432 *Ina makaranta labaran Books ɗin Ayshat Ɗansabo lemu, marubuciyar TAIMIYYAH DA NUFIN ALLAH kai har ma da sauran daɗaɗan littafanta? Marubuciyar na muku albishir da cewa sabon littafinta mai suna ƘADDARAR ZOYA ya fara sauka da zafinsa,labarin ƘADDARAR ZOYA labari ne da ya faru a gaske ba ƙageggen labari bane.Don haka kar ku bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta,labarin zai zo muku akan 500 Whatsapp group sai VIP group on Telegram 1k.Ku tuntuɓi marubuciyar akan lambarta 08167768704 domin samun free pages na labarin kai tsaye, kafin ku kai ga yin payment.Kar ku manta it's a true life story,don haka ku hanzarta shiga cikin tafiyar da babu ✍🏻 danasanin bin alƙaminsa.... * 5&6. A zaune na tarar da ita tana kullin siga, da yake tana auno rabin kwano tana k'ullawa, idan an zo siyan koko ana siya. Ikilima tana gefenta tana faman barci. Na ajiye ledar a gabanta. Ta kalle ni ta ce "Yabi na sha fa'da miki, jikina na bani sha'aninku da Jabiru ba mai yiwuwa ba ne, ba sa'an auren ki ba ne, gara ki tsaya akan Abdulrashid zai fi mana sau'ki da kwanciyar hankali". Na yi shiru, amma zuciyata sai tsalle take yi. Babban tashin hankalina a

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161