Chapter 52
Chapter 52
na jiranta. Da k'yar muka rabu. Cikin lallashi take ta nanata "Ki zauna lafiya, ki kwantar da hankalinki da na iyayenmu dan Allah. Kin ga dai an riga an yi auren nan. Allah ya taimake ki, ya hore miki shi. Nan da wata daya ki cigaba da sana'ar ki, domin mace mai neman na kanta ta huce takaicin babu". Ta bata rai ta ce "kinsan dai ba'kin cikin da na kwankwada a dalilin bani da yar'uwar da aka aurar da muke daki daya. Yanzu murna nake yi kema an aurar da ke na samu abokiyar ha'di. Komai ya taso miki ni ce a hakku saura ki ce zaki bayar da ni a wajensu ta hanyar nunawa duk daya muke ni da su a wajen ki. Gasu nan su hudu ne dakinsu daya." Nima na bata rai na ce "To idan hakane ita kuma Ubaida dawa zata hada kai kenan? Ko so kike ita ma ta fuskanci tsananin da kika fuskanta? Ni fa dukkan y'ay'an Babanmu ina sonsu da dukkan zuciyata". Ta zaburo mini ta ce "Ban ce kada ki so su ba, amma ai wata kusan tafi wata". Na yi dariya na ce "To kawai ki ha'da ni da Nazira da kuma Ubaida ki jamu a jikinki, ki dai-daita su da ni. Shikenan Kinga kin samu k'anne uku aurarru tashi guda. Da sannu suma manyan sai su dawo cikinmu mu zama madaurin tsintsiya". Ta yi gaba tana fa'din "To uwar Iyah! Ta ya ya zan ha'da shakikiyata da dan uba su zama duka daya ne?" Na k'yal-k'yale da dariya tare da fa'din "Yaushe zaki dawo?". Ta ce "sai an kwana biyu". Na zauna ina nazarin Yaya Ummi mutumiyar kirki ce, amma rashin adalcin da manyanmu suke yi mata da kuma yadda kishiyarta ta jefa yan'ubanci a tsakanin y'ay'ansu ya sanya ta k'yamaci dan uba. Na yi mata uzziri domin ita da yaranta suna fuskantar zazzafan yan'ubanci. Ina fatan watarana duka y'ay'an Babanmu mu zama abu guda, ina matu'kar son mu gane girman nasaba irin ta uba daya. *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* *** Bai dawo ba, sai da ya sallaci Isha. A falo ya tarar da ni, na yi wanka na zira doguwar riga cotton mai zuwa da mayafi babba. Na shafa turaren oudi(concentrate). Ya kalle ni ya ce "Ranki ya da'de Asiyata". Na galla masa harara na ce "Ba taka ba ce". Ya murmusa ya ce "Ta Ummi ce shikenan?" Na yi shiru domin so nake na fa'da masa abin da zai bak'anta masa rai. Amma tunda ya saki maganar bari na k'yale shi sai idan ya sake katobarar cewa ni tasa ce zan tabbatar masa ba tasa ba ce, ba kuma zan zama tasan ba. Ya ajiye ledar hannunsa ya fita. Sai gashi ya dawo da kananun bowls da kuma fork biyu. Ya zauna kusa da ni. Ya bude ledar kamshin hadadden balangu ta buge ni. Ya juyo mini dauri guda ya turo mini gabana. Tare da robar yogurt madaidaiciya mai sanyi, da kuma robar ruwa shima mai sanyi. Sannan ya juyo nasa daurin. A hankali ya ce "Bismillah Amarya". Ban kula shi ba. Na gama yaukina na dauka na fara ci. Sosai naman ya yi mini da'di, sannan kuma mai laushi ne. Na cinye tas na bu'de yogurt na fara sha. Rabona da abinci tun karyawar safe. Duk da an kawo mini daga gida amma ban iya ci ba. Ganin na cinye yasa ya turo mini nasa ya ce "Kara Asiya". Na yi kamar ban ji ba. A sanyaye ya ce "Ba kyau a yi magana mutum ya yi kamar bai ji ba". Nan ma tamkar ba na wajen. Ya yi k'wafa alamun ya k'ulu. Ganin hakan ya sanya na tashi na bar shi na yi dakina ko kwanon da na ci ban kawar ba, bare na kawar da nasa. Ina shiga kuma na sanyawa dakin sakata. Na cire mayafin rigar na haye gado na yi kwanciya ta. Tunda na kwanta ban farka ba, sai da asuba shima kwakwasa mini kofa ya yi. Kafin na fito tuni ya bu'de gida ya wuce masallaci. Yau kam har na gama barcina na tashi k'arfe goma. Da na bu'de kofa na fito a zaune na same shi akan barandar. Babu alamun gaggawa a tare da shi. Yana ganina ya mike da sauri yana fa'din "Bari na janyo miki, na roba da sanyi, na rijiyar kuwa dumi ne da shi. Ya bu'de bandaki ya dauko botiki ta nufi rijiyar. Na bishi da kallo. Mamaki nake yi dama Tijjani zai iya yin laushi haka? Duk wula'kancin da nake yi ba ya fasa yi mini hidima. Na sake bin kayan jikinsa da kallo. Alamu sun nuna ya yi wanka. Sabon yadi ne a jikinsa amma ba alamun karin guga. Na tabbatar yadda tela ya ba shi hakan ya saka su. Na ja tsaki sosai. Dai-dai lokacin kuma ya zo daf da ni. Ya ce "Asiya Toro wata rana za'a wayi gari a ga kin zama tsaka fa". Ban kula shi ba, bare na tanka ya samu sanadin da zai jani da surutu. Ya wuce ya kai mini bayin. Na shiga na yi wankana na fito. Yauma atamfa na dauko koriya Shar. Doguwar riga ce da ta manne a jikina. Na gyara sosai. Na gyara d'akin, na zauna. Ya yi sallamah na amsa a dole. Ya ce "Na shigo?" Na ja tsaki, na kame bakina na tsuke. Jim ka'dan ya shigo. Na daga kai na kalle shi. Fuska a daure na ce "Na baka izinin shigowa ne?" Da walwala ya ce "Tunda baki zabura kin ce kada ka shigo mini ba, ai nasan kin kammala adana yan kananun abubuwan da kike yi mini k'yashin ganinsu". Ba'kin ciki ya turnike ni. Na murguda baki na ce "A a kiyasai ne k'arewar kankantar". Ya zauna bakin gado ya ce "Ban da samun guri irin na ki Asiya. Ta ya ya zaki dinga rufe mini kofa, kina hayewa gadon da ba'a siya miki ba sai saboda ni, ni kuma ki bar ni da kwanan kasa. Kwana nake yi ina artabu da sauro. Amma ke babu ruwan ki, ba kya gudun maleriya ta yi mini illah?". Na ki kula shi, bansan me yasa yake bani haushi ba, baya burge ni ko ka'dan. Ya sake yin k'asa da murya ya ce "Ki yi kokarin kyautata lahirarki Asiya. Babu ruwan alkalami da cewar ba kya sona. Matu'kar ina kwana da ba'kin ciki ki sani kina cikin fishin Ubangiji". Na rasa me zance masa domin dai ya sako wanda ban isa na fa'di bak'ar magana a kansa ba. Kan tilas na share ban ce komai ba. Ya tashi tsaye ya ce ki taso ki karya ga abin kari can a falo. Bauchi zan je. In
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161