Skip to content

Chapter 90

Chapter 90

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

wanka kan gawayin. Na bu'de na ga ya yi zafi ainun. Na dauko babban flask din da nake zuba ruwan zafi na cika shi. Na ajiye sannan na juye ragowar na shiga wankan. Sai da na shirya na ha'da Mana abincin na kai ina cewa "Yau dai ka zama Yabi, na dawo na tarar ka yi komai sannu da kokari". Ya sake yi mini wani irin kallon da ban gane ma'anarsa ba. Duk da dai yanzu ya canja amma ba musguna mini yake ba, kawai walwala da sukuninsa ne suka ragu, sannan yana yawan yi mini abubuwan da suke kona mini rai ta hanyar shata layi da abin hannuna. Na kalle shi na ce "Sauko mu ci to". Ya girgiza kai ya ce"ci, ni ba yanzu zan ci ba". Na marairaice na ce"To zo ka dinga bani a baki na gaji sosai Wallahi". Ya sake kafe ni da kallon da yafi wadanda ya yi mini. Bai kuma ce komai ba. Na rasa gane manufar hakan sai kawai na fashe masa da kuka mai tsananin gaske. Ya taso ya zauna kusa da ni ya ce "Me na yi miki zaki yi mini irin wannan kukan?" Da kuka sosai na ce "To akan me zaka dinga yi mini kallon tuhuma? Akan me ba zaka zo mu ci abinci tare ba? Na riga da na gane ka tunda ka fahimci na fara sonka shikenan ka nade kafar wando fara yi mini wula'kanci kala kala". Ya matso jikina sosai ya kwantar da ni a kirjinsa ya ce "Da gaske kina sona Asiya?" Na ture shi na zum'bura baki na juyar da fuska gefe. Na kasa bu'de baki na ce uffan. Ya saki gauron numfashi ya ce "Shikenan na daina yi miki wula'kanci, duk da nasan ba na yi din". Da kansa ya zuba mana abincin. Lokaci zuwa lokaci kuma zai debo ya bani a baki. Ko ruwa da ya bula ledar bai sha ba, bakina ya nufa da shi. Na zuke tas na bar masa leda a hannu. Sai wani ya bu'de. Da yake ina siyar da pure water, saboda masu zuwa lalle kawia na tsiri siyar wa kuma sai nake yin ciniki sosai. Na yi gyatsa "Na yi hamdala. Gaba'daya sai jikina ya mutu murus gajiya ta taso mini, ba abin da nake so irin na kwanta na yi barci. Ga shi maghariba ta kawo kai. Na kalli agogo na ga za'a kai minitina arba'in da biyar kafin a kira sallah. Na mik'e na kwashe kwanukan, na hau zaga tsakar gida dan abincin da na ci ya dai- daita. Na koma falon na kwanta a kujera na yi daidai iskar fanka na kad'a ni. Ya taso ya fara bin gabbobina yana dannawa sannu a hankali nake jin da'di a jikina. Ban ankara ba sai kawai ya sure ni yana cewa "mu je daki na wartsake miki gajiyar gaba'daya. Na fara shure shure shi kuma ya ri'ke ni gam. Fadi nake yi "No bazan yarda ka dora mini wata gajiyar ba gaskiya". A kunne ya ce "Amma kinsan na ce idan kina yin gardama komin kankantar ta cikin ba shiga zai yi ba". Nan da nan kuwa na yi muk'us domin har zuciyata so nake na ganni da ciki, so nake na ganni da baby a hannuna kamar yadda nake ganin su Ubaida. Har aka fara kiran sallar Bai samu nutsuwa ba. Kan dole ya tsallake ya bar ni. A gurguje ya yi wanka ya nufi masallaci. Ni kaina a dole na sake wanka na sauke farali. Yau da wuri muka kwanta domin ana idar da sallar isha da ya shigo ya rufe gidan, ni dama a kwance ya tarar da ni. Sai da ya karasa abin da bai ida ba sannan muka yi wanka, muka kwanta wajen tara da rabi. Washagari lafiya muka rabu, da zai fita na ce "Idan fita ta kama ni zan fita. Bai ce komai ba, ni kuma ban yi zaton bai amince ba. Da yake na dora cewar na fara Home service akan status dina. Sai kuwa na dinga samun k'ira akan ana bu'kata ta a wuri kaza. Na za'bi gida biyu, na bawa guda biyu hakuri akan wasu sun rigasu. Na kammala gyaran gidan tsab. Na fice. Wannan ranar har dare sannan na koma gida. A k'ofar gidan na tarar da shi, cikin wani irin yanayi. Yana ganina ya zabura ya mik'e. Ni kuma ganin a waje muke yasa na zarta shi na shige. Sai kawai na tarar da k'ofar tamu da sabon kwad'o. Na jinkirta amma bai shigo ba. Na gaji da tsayuwar jiransa. Na fara hassala ya gan ni amma ya kasa shigowa, yasan kuma ya canja kwad'o. Na gaji na fita na tarar da shi yana zaune tamkar dutse ko motsi ba ya yi. Na ce "K'ofar a rufe take fa". Ko kala bai ce ba. Na sake fusata. Na ce "Ka zo ka bu'de mini". Nan ma tamkar da Dutse nake magana. Allah yasa ma babu kowa a wajen. Zuciyata ta hauro matu'ka da gaske. Duk fa'din tashin da nake yi dan asirinsa ya rufu shi bai ga hakan ba. Murya na rawa na ce "Ni kake yiwa wula'kanci haka?" A fusace ya ce "Wace ce ke? Gida ne bana bu'katar ki a cikinsa ba, ba sai ki koma inda kika fito ba, kin ga kin yi maganin wula'kancina, nima na huta da rainin da kike yi mini". Jikina ya yi matu'kar sanyi, hawaye ya b'alle mini. Murya na rawa na ce yanzu a daren kake so na tafi gida?" Shima murya na rawa ya ce "Ai ni a daren kika dawo mini gida. Dan haka ki koma inda kika fito ko ki je inda zaki, ai dai babu sisin ki wajen kama gidan har yanzu, bare ki yi mini sabon isgilanci". Na fara kuka na ce "Na rantse da Allah Tijjani kai bahago ne na k'arshe. Duk tunanina mu ha'du mu rufawa kanmu asiri wani bai ji ko ba'a gane halin da muke ciki ba, amma gaba'daya ka murde ka canja, ka ki da'din azanci. Dan Allah ka fahimce ni, nifa ba jin da'din yadda kake yi nake ji ba". A tunzure ya ce "Yo dama ni ina da abin da zan jiyar da ke da'di ne?" Na yi sakare ina kallonsa gaba'daya ya juye ya koma wani azababben mutum. A hankali na ce "To zo ka bu'de mini, tunda dare ya yi." Ya girgiza kai ya ce "bana son ganin ki a cikinsa." Na juya na ce "Shike nan na gode". Na fara tafiya ni kad'ai ga shi wajen ba kowa, tsoro ya kama ni, da na ji kamar ana bina. Sai da muka iso wajen hasken solar na juya sai na ga shi ne yake bin bayana. Na tsaya na ce "To mene ne kuma, ba dai ka kore ni ba?" Da sanyin murya ya ce "Bakin titi zan raka ki, kada karnu ka su biki". A tunzure na ce "Allah yasa ma kuraye su kama ni, su cinye ni! Bai ce komai ba, har muka isa inda zan bi na yi gida. Na kalle shi na ce "Yanzu me kake so na fa'dawa Baban Marina?" Kai tsaye ya ce "ki fa'da masa gaskiyar abin da ya faru kawai". Na

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161