Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

wannan al'amarin kamar yadda ka nisanta gabas da yamma." Na kasa magana, amma dai zuciyata ta yi nauyi, na kuma gamsu da gaske Yaya J yana sona da dukkan zuciyarsa. Gefe guda kuma ina gasgata tsinkayen Nazira da ta ce Baban Marina ma ba zai bashi aurena ba. Na k'udire bazan sake bari mu hadu ba, bare zuciyata ta dinga karaya a dalilin ta so mini da soyayyarsa da nake ta kokarin danne wa da dukkan iya wa ta. Washagari na tashi sukuku ba wanda ya tayar da maganar. Da yamma sai ga kwamshina ya zo, sai da ya fara zuwa wajen Baban Marina a wajen sana'arsa, ya sanar masa nan da kwanaki biyar zai zuro a yi maganar aure da saka rana gaba'daya. Shi yake fa'da mini hakan. A wannan ranar ma kayan da ya kawo mini ba k'aramin yawa ne da su ba. Tunda ga kan sutura, ga provisions tamkar wacce nake rike da kaina. Sai kuma dalleliyar waya da zoben gold wai a matsayin tukuicin amincewa da shi. Tuni Baba ya sallama ya bar ni ina rike waya. Wadanccan ma da ya rike tuni ya fito mini da abina. Dama k'ananu ne sai kawai na ce ya bawa iyayenmu mata tunda uku ne dama. Ni bansan me yake faruwa ba, ashe Yaya J bai fasa sintiri a wajen Mahaifinsa da Dada ba. Da ya kasa samun tallafinsu, sai kawai ya doshi Baban kasuwa mahaifin Maijidda. Nan ma fatattakarsa ya yi tare da alwashin idan mummunar k'addara ta afko aurenmu ya tabbata, to kuwa ya kwana da sanin sai dai ya sako masa Maijidda. Hankali ya fara tashi domin gaba'daya Yaya J ya susuce ya rasa nutsuwa har ta kai Maijidda ta dawo gida a dalilin zaman nasu babu da'di sam, ita kuma ta gaza ha'diye damuwa ta taho, da k'yar Dada ta mayar da ita. Baban Marina da kansa ya fa'da wa Dada da yan'uwansa cewar ranar asabar za'a zo neman auren Yabi, kada su yi nisa. Daga Baban Tsakiya har na Kasuwa suka gabatar da uzzirin suna da daurin aure muhimmi a wannan ranar. A wannan karon hankalin Baban Marina ba k'aramin tashi ya yi da wula'kancin da suke yi masa ba. Ya gabatar da korafinsa gaban Dada cikin kankan da kai ya ce "Ba zai yiwu na dauko wasu daga waje su marabci masu neman auren y'ata ba. Alhalin ga y'anuwana ban da ransu da lafiyarsu, har wanne daurin aure zasu je da yafi al'amarina muhimmanci Dada? Ki shiga cikin wannan maganar, ina jin tsoron kada na kasa jurewa fa." Ita da kanta ta sani ba'a kyautata masa ko ka'dan amma da yake bata iya tsawatar wa wadanccan shiyasa bata iya magana, har komai ya rincab'e. Da rashin walwala ta ce "Zamu zauna da daddare dukkanmu". Da daddare kuwa dukkansu uku suka hadu a gaban mahaifiyarsu, a sanyaye take gabatar da k'orafin da yayansu ya zo da shi. Babu kunya dukkansu suka ce suna kan matsayarsu ba yadda za'a yi suna cikin hankalinsu su jagoranci bawa mai saka d'agaggen wando aure, kema da za'a fito k'arara a fa'da miki ainihin yadda ak'idarsa take da kin k'yamace lamarin wannan mutumin. Mun yi shiru ne kawai dan kada ace hassada muke yi. Ko bamu da kirki, amma waye a jahar nan bai san yadda Mustapha Zaki ya yi k'aurin suna wajen yiwa masu akidar yin maulidi kafar ungulu ba. Duk wani masallaci indai ba na yan kungiyarsa bane sai ya durkushe shi, ke kan ki da yasan yadda kike son shehu da ya d'aure ki saboda zuciyarsa babu alheri." Dada ta kad'u kwarai da gaske. Domin babban b'acin ranta a nemi ta'ba mata mutuncin ra'ayinta. Ita din mai mai zazzafar akida ce akan hakan. Ta fara tafa hannu tana cewa "Ashe hakane? Allah na gode maka da ka kubutar da jinina fa'da wa hannun wanda zai yi mata sanadin rashin samun rabo ranar gobe". Sai ta hau kuka tana sake godiya ga Allah da Annabi. Jikin Baban Marina ya yi matu'kar yin sanyi ta yadda yan'uwansa suka shammace shi, suka gabatar da hujjar da ba mai kankareta a zuciyar Mahaifiyarsu. Ya tabbatar sun dade da kitsa maganar dan sun tabbatar auren ya rushe gaba'daya, kuma wannan hanya ita ce mafi sau'ki da zasu ja hankali gyatumarsu ta lalata komai. A zuciyarsa ya dinga ayyana shin wanne irin zamani muke ciki wanda dan-uwanka ma baya son ya ganka a inuwa? Me ya tare musu ne? Shi ka'dai ne yake fuskantar irin wannan tsananin ko kuwa a ko wacce zuria ce? "Allah kai ne mai zamani, a kawo mana mafita, da sassauci" ya fa'da a ransa. Ya sake kallonsu, yana ganin sun hade sun bar shi daban, sai dai a zahiri ne suke shiri a bad'ini kuwa ba wani taimakon juna a tsakaninsu, tunda kowa iya y'ay'an da ya haifa ne dolensa. Sannan kowannensu boye wa dan-uwansa wadatarsa yake yi. Ya sauke gauron numfashi kafin ya yi magana ya ji Dada tana fa'din "matu'kar ina da iko akan ka ba za'a bashi aure ba, idan kuwa ka kafe sai dai na barka da Ubangijin gizagizai ya bi mini kadina a wajenka". A ki'dime ya ce "Har abada maganar ta mutu, Allah ya yanke mata wahala ya fito mata da wani mafi alheri wanda za'a yi alfahari da shi". Dada ta goge idonta tana fa'din "Ameen". Baban Tsakiya kuwa ya ce "ai y'ar fariya ce , ba zata tsaya a matsayinta ba, dama ya ta kasance? bare yanzu da wannan tsohon banzan ya sake kambaba burinta. Ai idan ba tashi aka yi akan ta ba, sai ta tsofe tana gabanmu tana zuba d'ibar albarka, ko yanzu tana ganin sakamakon hatsabibanci, tunda duk kintsatsse ba zai zo wajenta ba. Har yau ta k'i barin Jabir ya fuskanci matarsa sosai, da sun fara zama lafiya idan har ya yi tozali da Yabi zai gigice. Gashi kuma Maijidda matarsa ce, tunda cikine da ita, idan ba'a bashi aurenta da ake ta munafurci ba, ta ya ya ake so wannan rabon ya bayyana?" Baban kasuwa ya ce " Ai ha'kuri Muna cikinsa, amma sai ace mune da laifi, ban da sha'anin jini tasirinsa yawa ne da shi ai wata shari'a sai a lahira kawai." Dada ta ce "To ni kam ba zaku bar gun nan ba sai an samo wanda za'a ba shi auren Yabi. Domin na fuskanci matsalar gidan nan tana 'damfare da ita." Baban Tsakiya ya sake cafe wa da cewa "Kinsan dai ni da Iliya bamu da mutuncin da zamu yi irin wannan ikon da ita, wannan maganarki ce da ubanta." Cikin rawar murya irin ta sare wa da lamari Baban Marina ya ce "Yau muna watan Safar ko Dada? To matu'kar rayuwata ta kai, watan jibi na gaban maulidi ke nan, zan aurar da ita. Domin ina da wadanda zan basu aurenta su kar'ba, sannan ita ma Ubangiji ya hore mini ita zata ta yi mini biyayya. Ubangiji kuma zai duba manufar kowa a nan ya cusa wa wanda zan ba shi auren ya kar'ba da dukkan zuciyarsa". Dada ta ce "Allah ya tabbatar ya nuna mana lokacin, amma ba za'a tashi ba sai ka fadi wanene, d'an wacce haular ce? Gudun kada a sake kitso da kwarkwata." Baban Tsakiya

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161