Skip to content

Chapter 140

Chapter 140

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

cikin masu zuwa duba shi tare da jajanta masa. Gobe zan koma, sai mu tafi tare ko ya samu nutsuwa". Ta kasa amsawa. Hatta Dada ma na kashe ta da kunya gabad'aya sun rasa me zasu ce. Yanayinsu ya sa na gane suma tamkar an tursasu ne akan sha'anin Tijjani. Washagari kuwa na shirya yara na ce mun tafi Kano. Baba bai so ba, amma saboda lallaba farincikina yake yi bai hana ba. Sai ma ya ce "Ubaidun Inna ya raka ni. K'ofar Dada na dire. Na tisa Nasiba a gaba muka tafi a kan dole ba yadda zata yi. Domin na lura tsoro nake bata. Har muka isa Kano ba wata hira a tsakaninmu. Sai kuma muka hadi da tasgadon y'an sanda. Wai ba zamu gan shi ba, ana yawan yi musu zarya da sunan ganin Tijjani bayan shi mai babban laifi ne. Hanif ya fashe da kuka yana ce wa "Zamu ga Baban 2 dan Allah ". Hamim ma ya fara kuka sosai. Watak'ila tausayi suka bawa wannan babban dansandan sai kawai ya bada umarnin a fito da shi. Ga mamakina sama da mintina goma da isowar Tijjani bai kalli inda Nasiba take zaune ba. Tunda ta gaishe shi ya amsa hankalinsa na kan su Hanif da suke kan cinyarsa bai sake bi ta kanta ba. Ni da yara kawai ya ke kulawa. Na mike na ce "Bari na baku waje tunda idona yasa ka kasa yin hirar". A zabure ya ce "Zan ci mutuncin ki little! Jiya da yau ban ji azabar da nake ji ba. Akwai abin da ake yi mini wanda zalunci ne da k'eta. Alfarmar Annabi kuma Allah zai kawo mini k'arshen al'amarin tunda kwana nake ina fad'awa Ubangijin al'arshi ya warware mini wannan masifar. Ni ko wannan k'azafin da aka yi mini baya gigita ni, kamar yadda al'amarin ta yake gigita ni. Amma akwai Allah." Ba Nasiba ba, ni kaina sai da na ji babu dad'i ainun. Na yi tsuru tsuru na kasa ce wa komai. Domin na tabbatar k'arshen muzanci Tijjani ya yi shi. Amma na sake gasgata surkulle ake yi masa. Ban da haka jiya k'iri k'iri ya fad'a mini yau na kawo masa ita. Ko tunanin rikicin da zan yi masa bai yi ba, saboda an ringa an kidima shi a kanta. Na daure na rakito ta, amma bai ko kalli inda take ba, sai ya b'uge da cin mutunci. Jikina ya mutu domin nasan zata zargi na kwaso ta ne dan na saka mijina ya wulakanta ta a gabana. Tunda a hakan kafatalin gidan Marina sun tafi akan na gama da Bulkachuwa tsorona yake ji. Sai abin da na shimfi'da zai bi. Har fad'i suke idan bana son mutum to ko kallon arziki Tijjani baya masa saboda gudun zuciyata. Ta mike a kasalance ta ce "Bari na jira ku a mota Yabi". Murya babu amo na ce "To". Tana tafiya ya saki dogon tsaki mai karfi da na tabbatar zai je kunnuwanta. Na zuba masa ido ba tare da na iya ce wa komai ba. Da k'yar na ce "To da sun san zasu mayar da kai Bauchin me yasa suka kawo nan?" Ya kalle ni ya ce "Akasi aka samu. Sun tsayar da ni a farko ban tsaya ba. Shine suka harbi tayar motar ikon Allah ne yasa motar bata yi bari da ni ba". Zuciyata ta buga da tsananin gaske na ce "mene ne dalilin ka na k'in tsayawa Baban 2? Ta ya ya kana dan k'asa amma ka ce ba zaka girmama dokar k'asar ba? Ko dai kasan dama baka da gaskiya ne?" Nan da nan ya kidime ya ce "Wallahi Tallahi ina da gaskiya, bansan an saka mini wannan abin ba. Ban sani ba, ki yarda da ni Asiya!. Na saki karfaffan numfashi tare da ce wa "Rashin tsayawar ka ba k'aramin hujja zasu kafa da ita ba. Na yarda da kai". Ya nutsu ya ce "Idan har kin yarda da ni to kowa ma kada ya gasgata ni Asiya! Nasan mahaifuyata zata shaide ni, duk fitina ta bana harkar maye bare kuma a yanzu da na girma. Ba zan shiga safarar abin da nasan illah ce ga al'umma ba. Ina miki ranstuwa da girman Allah ban san mugun abu aka bani ba. Waya kawai aka mini akwai sakon kaya da zan karba a Dutsen tanshi, idan na kai Kano za'a karba a biya ni. Kinsan kuwa ina harkar sakonni(Delivery). Ban tab'a zaton za'a mini kutse a cikin sana'a ta ba. Ni yanzu babban tashin hankalina ke ce. Ban san hukuncin da za'a yanke mini ba little. Kinsan k'asar nan waka sani ne waya sanka." Idona taf da hawaye na ce "Nasan baka aika ta wannan BAK'AR TA'ADAR ba. Da ikon Allah ina tare da kai, komin tsanani". Ya murmusa ya ce "Alhamdulillah! Na samu amincin firgicin da nake ciki. Dan Allah Asiya kada ki canja, kada ki juya mini baya a cikin wannan halin canka cakare da nake ciki." Idonsa ya kad'a sosai ya kasa cigaba da magana alamun ya shiga rudani. Hanif ya ce "Baban 2 kada yi kuka zamu zauna mu taya ka zama. Ammo ta tafi ta barmu tare da kai". Hamim ya ce "No zamu je mu koyo yadda zamu kwace shi daga hannun yan sandan kawai". Na yi k'asa da kaina kawai ina hawaye domin tausayin da suka ba ni ba kad'an ba ne. Ban iya ce musu komai ba. Shine ya yi jarumtar sake rungume su tunda a akan cinyoyinsa suke. Murya na rawa ya ce "Baban 2 baya karya domin wanda ya yi karya ya zagi Allah, Wanda ya zagi Allah kuwa dan wuta ne. Dan haka am innocent, ban yi laifi ba. Sharri aka yi mini. Kowa ya yi sallah ya yi wa Baban 2 addu'ar ya zama free". Suka had'a baki wurin ce wa zamu yi sosai ". A sanyaye muka rabu domin gobe za'a dawo da shi BAUCHI dan shiga kotu. A hanya Nasiba ta sake rasa kuzarin ta, dama kuwa bata iya sake wa a gabana na dade da fahimtar a takure take da ni. Abin da Bulkachuwa ya yi mata kuwa ya sake sanyaya mata jiki. Ina hankalce da ita, ina ganin yadda take son yi mini magana amma ta kasa. Cikin kundubala ta ce "Yabi!. Na amsa da "Na'am" murya babu amo. Ta kalli twins da suke barci a jikina. Ta ce "Idan na ce miki bana son Yaya Bulkachuwa na yi karya domin na girma da son sa, ke ma kin sani. Idan na ce miki a yanzu dole aka mini a kan aurensa zaki yarda?" Ban ce komai ba. Illah ido da na zuba mata. Ta numfasa ta zarce da ce wa "Ni da kaina bani da yadda zan yi ne. Domin kuwa mutane da yawa suna haduwa da kalubalen a hadasu da iyaye karkatattu. Sai dai duk da hakan ba zamu ki sonsu ko janye wa daga gare su ba. Na sani tun farko soyayyar sa gare ni ba mai yawa ba ce, bare yanzu da yake auren ki. Dan Allah ki yi hakuri kada ki datse mu'amala da ni Yabi. Al'amarin zumuncin yau ya shiga rudani mai yawa, amma idan aka yi hak'uri aka danne, aka yi

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161