Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

Murya ba amo ya ce "Madallah da Dada da y'anmatantanta". Duk suka hau rige rigen gaishe shi Amma ban da ni. Ya amsa hankalinsa na kaina. Ya kasa ha'kuri ya ce "Asiya Toro how far?". Na yi banza da shi. Domin dai na tsani yadda yake gatsa ainihin sunana, dan kuturun wula'kanci har sai ya ha'da da Toro. Kusan kowa Yaya Bulkachuwa yake ce masa, ni da bama shiri bana ce masa Yaya Bulkachuwa. Amma sai nake mutuntunta shi wajen kiransa da Yaya Tijjani amma bai yaba ba, bare ya gode. Yabin da zai ce ne yake ganin asara saboda an cika zuciyarsa da k'yashi. Shi yasa nima na janye yayan tuntuni nake gatsa Tijjani gatsal wanda na lura shi ko oho. Ina nan, ina kallon wadanda basa ce mini Yabi, duk ranar da Ubangiji ya sanya na je Saudi akan girma da hankalina ko tsarabar abin da ba'a so ba zan basu ba. Tijjani na cikin sahun farko. Yaya Ummi ce mutumiyarsa, baya zuwa gidan kowa amma yana zuwa gidanta, har idan da ku'di a tare da shi ya yi wa ya'yanta alheri. Sosai suke d'asawa, mutimiyarsa ce ta sosai. Dada ta fusata ta ce "Mugun nufi ya k'are miki Yabi! Ko wacce ta gaishe da dan- uwanku amma ban da ke, bai yi fishin wula'kanta shi da kika yi ba, ya sake bu'de baki ya yi miki magana amma kina ji sarai kin k'yale shi, saboda ke din kina gaji nunkufurci da ba'kin hali ko?" Raina ya baci domin a kullum kalaman Dada a kaina kenan, bansan me Goggo ta tsare mata da a kullum sai ta jingina mata munafurci da ba'kin hali ba, ko da yake na taba jin labarin cewar tun haihuwar Yaya Ummi da dangin Goggo suka zo suna daga garinsu na Kangire cikin k'aramar hukumar Birin Kudu suka fuskanci wulakanci daga wajen Mama. Shikenan duk haihuwar da take yi basu sake yin gayya sun zo ba. Sai dai a samu mutum biyu su zo su ganta washagari su juya sassafe. Wannan matakin da suka dauka shine ya zama laifin da yak'i wuce wa a wajen Dada da take ta musguna mata da gorin ba y'ar babbar haula ba ce, sannan yan'uwanta masu k'ullaci ne, duk kuma cikin matan gidan mahaifiyarmu ce kawai bata da kowa a garin Toro shi yasa ma wani abin ake yi mata da gan gan. Duk da ba jin dadin zaman take yi ba, ta jure dukkan kalubale dan kawai ta zauna da mu yaranta, amma bata tsira ba tunda Babanmu ma haka siddan sai ya dauke mata wuta na tsawon lokaci mai yawa. Mama kuwa bata fasa yi mata yankan baya a duk inda ta zauna ko ta samu damar yin hakan ba. Ko yaushe Gwaggo a cikin mutuntunta Dada take hatta wankin kayanta har yau bata daina yi mata ba, amma babu gwaninta bare yabawa. Nan da nan na tunzura na ce "Da yake shi kina jin tsoron kada ya keta ki shiyasa kike fa'din hakan. Amma ni kin bu'de baki kina niyyar tozarta ni. Tunda ban gaishe shi ba, ya yi mini magana ban amsa ba, ba sai ya rabu da ni ba? Bana son harka da shi ne, a duniya na tsani sunan da yake kirana da shi. Sannan idan zai mini magana sai ya lanjare murya, kuma kinsan dai ba sosai nake ji ba, bare na ji shi da kyau". K'wafa ta yi tare da cewa "Kowa ya yi na gari ai dan kansa Yabi". Basira ta ce "Yi ha'kuri Dada d'ora mana karatun kawai". Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Kayya Basira zuciyata ta jagula ainun karatun nan sai gobe kuma". Firdausi ta ce "Yaya Bulkachuwa saka baki Dada ta d'ora mana karatun, bata ha'kuri mana". Ya kalle ta ya ce "Dadarmu share kawai, nima na ha'kura ai. Kinsan hankalin Asiyan Toro a k'auri yake". Na sake hauro wa na ce "Tijjani ka bari, ka ga dai bana shiga harkarka akan me zaka nemi takure ni ne? Gaskiya bana son haka". Dada ta sake yin k'wafa tare da cewa "Yabi kin janyo muku, domin na lura tashen balaga kike ji, zan kuwa yi maganinki." Kafin wani ya yi magana sai ga Ikilima k'anwata da a yanzu take shekaru tara. Ta shigo cikin nutsuwa ta kalle ni ta ce "Adda Yabi ki zo". Da azama na mike domin nasan Yaya Jabir ne. Saurayin da yake gigita zuciyata da ruhina. Ban ce komai ba, na mike ina cewa "Sai da safenku". Dada ta bimu da ido tana cewa "Jabiru ne ko kuwa wani ne?" Ban kula ba, ba kuma wacce ta tanka. Domin dai na fi su farin jinin mane ma duk kuwa da ba finsu kyau na yi ba, asalima wasu sun fini kyau, sun kuma fini cikar mace. A bakin kofar Shashenmu ya jingina. Matashin saurayi mai cike da nutsuwa da kamala. Wankan tarwada ne, siriri mai matsakaicin tsayi, mai sanyi a halayya da kuma dabi'a. Bashi da kwaramniya tun tashinmu, mai hakuri ne na gaske, da wahalar gaske ka ga fa'dan Yaya Jabir. Sosai muke shiri da shi, duk kuwa da ni din mai tsiwa ce, mai kuma hayaniya ce. Amma jininmu ya ha'du sosai. Kusan tun soyayyar kuruciya ce ta rikide ta zama ta gaske. Dalibi ne a jami'ar tarayya ta Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Ajinsa uku sawess yake yi a cikin Jos. Sannan ya yi sa'a ma'aikaci ne a karamar hukuma da aka dauke shi aiki da sakandire a lokacin kawunsa kanin mahaifiyarsa kansila ne a yankin gundumar Toro. Na isa gare shi, yana sanye cikin farin yadi fari k'al. Wato duk samarin gidanmu babu mai tsabtar Yaya J. Ina jin da'din k'iransa da Yaya J. Na lura shima ba karamin son sunan yake yi ba. Ni ka'dai ce nake fa'da masa hakan kuma. Kusan halayyarmu daya ni da shi, domin nima tsabta ce da ni, har fa'di ake yi aljanun tsabta ne da ni. Baya ga haka muna da son y'anuwanmu, bama jin k'yashi wajen salwantar da duk abi da yake namu ne akan d'an-uwanmu, har rashin girman jikinmu iri d'aya ne. Shine d'a na farko a bangaren Baban Tsakiya. Mutane da yawa suna fa'din kama muke yi ni da shi, ni kuma bana ganin kamar kawia dai yanayinmu ne daya tunda shi din ba wani girma ne da shi ba, haka yake dan madaidaici avarage height ne. Haka nima duk cikin y'anmatan da muka taso ko wacce ta fini tsayi, bani da tsayi, nafi kusa da gajerta. Ina da gashi sosai, sannan ina da manyan idanuwa baya ga hakan fara ce sosai. Yadda nake yar cif cif sai nake matu'kar daukar hankalin mutane. Kullum idan zan fita sai Gwaggo ta ce ban da wulakanci Yabi, domin al'adar gidanmu ne yarinya bata kammala karatun sakandire. Shekaru sha biyar ake aurar wa, amma mu da alamu za'a bari mu kammala duk da dai Dada ta fara fa'din mu shirya dama kuma ita ce take matsa lambar sai an yi aure. Ya zuba mini ido babu walwala jikina ya yi sanyi na yi kasa da kaina ina fa'din "wannan kallon tuhumar fa Yaya J?" Ya saki gauron numfashi ya ce "kin kama kanki da kanki Yabi. Jiya ma

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161