Chapter 44
Chapter 44
auren zumunci. Amma a yanzu yadda yake jin Yabi zai iya yin komai dan ya same ta. Ya gamsu tausayi da sonta sun masa rubdugu. Ya rufe littafin ya mayar da shi ma'adaninsa. Ya jima a zaune yana ta tunanin sana'ar da zai fara. Ya saki gauron numfashi! A fili kuma sai ya ce "Allah ka hana Tijjani sanya Yabi kuka! Allah ka hana ni zaluntar ta. A hore mini ita ya Ubangiji". Ya zabura ya mik'e yana ganin lokaci ya yi da zai daina buga buga ya samu tartibiyar sana'ar da zai dogara da ita tunda nauyi mai yawa ne zai hau kansa, wata'kila ma badi war hakan yana shirin zama Abba. Murmushi da kunya suka subuce masa ya dinga sosa k'eyarsa tamkar yana gaban manya ne. A fili ya furta wa ya ga "Yabi as uwa?" Sai dariya ta sosai ta kama shi, har bacin ran da Jabir da Dada suka cusa masa ya yi sauki. Ya fito ya nufi wajen Alh Tsoho magini dan ya ji ko zai masa hanyar samun aikin ginin. Yana tafe sanye da yadi na wando da riga bata kai guiwar sa ba. Kamar kullum a wanke suke amma fa babu guga. Sannan ya saka hular sanyi ya rufe gashin kansa. Domin tunda aka furta za'a bashi auren Yabi. Bai sake yarda an ganshi da gashin kansa ba, duk da ya ki aske wa. Ba wanda yake jin kunyar ya ganshi da sumar irin Baban Marina. Domin ya sani baya so, ya sha tisa shi a gaba ya saka a masa askin akan dole. A yanzu kuwa wata irin kunyarsa yake ji ta sosai domin bayan kawunsa ne da yake yi masa adalci, yanzu shirin zama surukinsa yake yi. Bulkachuwa da kansa ya yi amannar ba dan zuciyar Baban Marina irin ta daddako ba ce da ba za'a yi masa wannan k'arfin akan diyarsa ba. Ba dan alherinsa mai yawa ba ne, da ba zai ba shi aure ba, komai za'a yi kuwa. Amma ya yi shahadar ba shi, babu dogon turanci. Yana tafe yana fa'din "Allah ka fitar da Tijjani kunyar Baban Marina". Ya sha kwanar shiga cikin wani kwararo sai kawai ya fara jin k'amshin turaren da yake ji a jikin Yabi da kuma wanda yake shaka a jikin Jabir. Ya shiga sai kuwa ya hangosu kowannensu jingine a garu. Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi. Kishi mai tsananin gaske ya dabaibaye shi. Tamkar ya juya sai kuma ya tsinci kansa da tunkararsu. Ya zuba musu ido. Yabi na kuka sosai yayin da Jabir idonsa ya kad'a ainun. Sau d'aya za'a kallesu a gane suna cikin tsananin soyayya da kuma halin cankacakare. Ya kalli Jabir da yake tsab da shi cikin shadda ruwan toka ta sha guga. Farin gilass ya mak'ala. Ga k'amshi mai da'di na tashi a jikinsa domin komin hassada baka isa ka ga wani abu na rashin tsabta ko gayu a tare da Jabir ba. Yayin da Yabi take sanye da hijabanta har k'asa sai dai duk ya b'aci da hawaye har da ba'kin kwalli. Kishi sosai ya turnike Bulkachuwa. Har ji ya yi zukar numfashi na neman yi masa turjiya. Amma a hakan ya motsa k'wanjinsa ta hanyar cewa "Jabir na tabbatar babu jahilci a tare da kai tunda ka yi zurfi a ilimummuka daban daban. Sai dai abin mamaki sanin naka bai amfana maka komai ba, tunda zaka iya tsayawa da wacce kwanaki kadan ya rage a daura mata aure a cikin lungu inda babu sawu. Ni ba zan yi maka rashin adalci na yi maka kazafi irin yadda ka yi mini ba. Sai dai na sha fa'da kai din azzalumi ne, ba masoyi ba. Ta ya ya an baka aure ka karba, dan kwadayin albarkar iyaye ita kuma ka dinga hure mata kunne da ga yiwa nata tsohon biyayya? Ban da ita din sakara ce har wanne kalami ne a bakinka da zaka tsara mata da yafi na ubanta da kannensa tasiri?". Jabir ya sandare ya zuba wa Bulkachuwa ido, yana jin wata irin fargaba from no where tana shigarsa. Yayin da ni kuma na dago ido jage jage da hawaye na watsa masa kallon kiyayya da raini na ce "Ba ruwan ka da ni Tijjani! Na saurare shi din, domin shi nake so, nake fatan kasance wa da shi". Ga mamakina sai kawai ya ja kakkuran tsaki tare da ce wa "Ai ke din shasha ce! Kuma kin ji na saka maganata da ke? Da shi na ke wanda na gamsu da hankalinsa da iliminsa, kawai adalcinsa ne bai gamshe ni ba. Amma ke da baki da hankali ina ruwana da ke? Jiyan nan na gan shi da matarsa a asibiti yana ri'ke da ita. Yana faman tattalinta. Wai matar da ya aure ta ba dan yana so ba yake yiwa irin wannan son da adalcin, amma ke kullum yana cikin dama miki lissafi. Da yake ya mayar da ke shargalle marar tunani." Ai kuwa yana rufe baki kuka ya k'wace mini sosai. Jabir ya kasa magana domin ya tabbatar Bulkachuwa ya gansu a asibiti ba k'arya ya yi masa ba. Bulkachuwa ya sake yin k'uta tare da nuna Jabir da yatsa ya ce "Neman aure cikin aure haram ne in ji ma'aiki (S.A.W). Da ku'din aurena akan ta, ko ba zaka yi mini kawaici irin na zumunci ba, to ka yiwa ka'idojin shari'a biyayya. Ka fita mini a harkar Asiya! Ubangiji ya baka Maijidda wacce ita ce mafi alheri a gare ka. Amma bar mini Asiya Toro domin ina da yakinin akwai babban al'amari a tsakanina da ita. Daga ranar da aka tabbatar mini an ba ni ita, na fara addu'ar na yi nisan kwana mai yawa dan na tabbatar ni kad'ai na mallake ta". Still Jabir ya kasa magana domin gaba'daya almarin ba k'aramin bugunsa yake yi ba. Kishin Bulkachuwa ya shak'e shi k'warai da gaske. Domin idan gaskiya zai fa'da ya ga son Yabi a idonsa irin wanda bai yi zaton Tijjani zai yi mata ba. Mussaman yadda bai dauki soyayya da muhimmanci ba. Mace tana bata masa rai zai juya mata baya duk yarda yake da ita kuwa. Ina kuka, ina kallon Yaya J. Na sani dan na yi ba'kin ciki ya sanya Bulkachuwa sako maganar Maijidda. Ban da haka mene ne dan ya nuna kulawa akan matarsa ta aure? Nan da nan zuciyata ta hassala cikin rawar murya na ce "Mene ne dan ya kula da lafiyar Iyalinsa? Tabbacin nima zai kula da ni ke nan tunda har ya yiwa wacce baya so adalci to ina kuma a ce ni ce da yake so? Kai sau nawa ana ganinka da tambadaddun matan banza?" Take jikin Yaya J ya yi k'wari domin yasan yadda nake da kishi na gaske, maganar Bulkachuwa na iya tunzura ni na yi masa fishi. Dan haka ya dan murmusa. Sannan ya ce "Ko yanzu na mutu a sanadin rashinki ba ni da kaico tunda kin mini kyakkawar shaida Yabin J". Da rawar murya na ce "Idan ka mutu, kuma ka bar ni da wa? Wanne irin ba'kin fata ne, akan me zaka mini fatan irin wannan asarar haka?" Tijjani ya harzuka ya ce "Ba zaka mutu ba ka ga yadda Asiya Toro zata manta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161