Chapter 92
Chapter 92
ga Yaya Ummi da alamu tare suka fito da yaranta yan makaranta su suka wuce ita ta taho nan. A falo muka zauna. Ita ta fara ce wa Yaya Bulkachuwa ka ga yadda ka koma kuwa me yake faruwa ne?" Ga mamakina yana bu'de baki sai ce wa ya yi "Ba'kin cikin Asiya ne yake neman kassara ni". Gabana ya takarkare ya fadi. Me nake yi masa ni Yabi?" Yaya Ummi ta ce "me ya faru haka Yaya Bulkachuwa?" Na kasa kunne sosai dan na fahimci abin da zai ce da kyau. Sai ji na yi ya fara rattabo laifukan da nake yi. Cikin nutsuwa ya ce "Ummi tunda aka rufe gidan burodi da nake zuwa na shiga yanayin rashin ku'di. Har ta kai bana iya yin abin da ya kamata. A farko rimi rimi Asiya ta ke ha'kuri da duk abin da zan kawo. Tare zata sarrafa mu ci, ko da garin kwakai ne. Amma tafiyar bata yi nisa ba sai ta fara gazawa. Ta fara raina kokarina saboda an riga an cusa mata akidar watarana ita ce zata rike mini gidan. Komai zan siyo na bata ba zata yi amfani da shi ba. Kwanaki na siyo sabulun wanka Gif har yau bata ta'ba ba, ta bayar an siyo mata wanda ya dace da ita. Duk ban ce komai ba. Sai shekaranjiya kuma ta ce mini zata fita, ban zaci wai gida gida zata dinga bi tamkar dilalliya ba. Tun safe da ta fita sai yamma lis ta dawo wai ashe gida je ta dinga bi tana yin k'unshi ana biyanta saboda kawai ta fahimtar da kowa ita ce take ri'ke da ni! Ya nisa ya zarce da fa'din tana shigo wa ta tarar na yi komai Kamar yadda ta sani tun farko ni aikin gida bai zame mini komai ba, amma kinsan me ta ce mini?" Yaya Ummi ta girgiza kai cikin sanyin jiki. "Tana bude baki sai ce mini ta yi wai na zama Yabi. Wato na zama mace mai zaman gida, ita kuma ta zama namiji mai fita ya yi gwagwarmaya. Duk yadda maganar ta buge ni hakan na daure na ha'diye maganar na kawar mata da kai! Ya fa'da yana hucin b'acin rai. Gaba'daya jikina ya mutu, zufa sai keto mini take yi. Na tabbatar duk abubuwan da ya lissafo ina yinsu tabbas. Amma ko ka'dan a zuciyata ban daukesu zasu b'ata masa rai ba. Domin ko ka'dan ban yi da nufin wula'kanci ko na muzanci ba. Asalima ni na yi ne da nufin kyautatawa. Kafin Yaya Ummi ta ce komai sai ya cigaba da fa'din "Jiya kuma ta ce mini zata fita ban amsa mata ba. Sai kawai na dawo na tarar bata gidan, tun azahar nake zaman jiranta bata dawo ba sai tara saura. Fa'da mini Ummi me ta mayar da ni, me kuma take nufi da ni ne?" Yaya Ummi ta yi shiru ta rasa abin fa'da domin ta fahimci ransa ba k'aramin baci ya yi ba. Sai kawai ta buge da ba shi hakuri tare da ce wa"Tabbas ta yi kurakure, amma ka yi hakuri zata kiyaye." Ya girgiza kai ya ce "Ba fa zan yi hakuri ba tunda ba zan dauki wadannan BAK'AK'EN TA'ADODIN da ta fara tsirarsu tun daga yanzu ba. Gara manyammu su san halin da muke ciki kada abu marar da'di ya faru ace na bawa marar d'a kunya." Yaya Ummi ta yi maza ta ce haba dai, haba dai Yaya Bulkachuwa ba abin da zai faru sai alheri. Ai gata nan duk ta ji abin da ka fa'da, za kuma ta kiyaye." Ya girgiza kai ya ce "Kin san kafiyarta, ba ji zata yi ba, ni kuma ba zan yarda ba. Kin ga gara komai a yi shi a bayyane ba sai abu ya yi tsananin da rayuka zasu baci da yawa ba". Ni gaba'daya ma mamaki ya ba ni, ya fitittike akan sai na tafi, ita kuma Yaya Ummi sai wani lallab'a shi ta ke yi. Yo ni ban da ina jin tsoron al'amarin da zan fuskanta a gidnman Marina ma zunde da dariya, da ba'kin cikin da zan jefa iyayena da na girgije na bar masa gidansa. Ta kallo ni tare da mini signal din na ba shi hakuri. Na dauke kai na juyar da fuskata. Domin nima na hauro ai komai nake yi dominsa ne. Amma tunda shi ba zan yi masa alheri ya yaba ba, sai dai ya bini da sarhutu to shi kenan na daina yin komai. Fita k'unshi da sunan Home service kuwa na soke sai ya nemo wani laifin kuma. A k'asa zuciyata kuma sai hirji nake yi tare da fatan Yaya Ummi ta kashe wannan matsalar domin duk yadda na hauro nake kurarin zan iya tafiya din, zuciyata tafi son zaman, nafo son ya huce ko ba dan ahalin Marina ba. A karan kaina na damu da fishinsa. Da k'yar Yaya Ummi ta shawo kansa ya ha'kura da maganar sai mun je gaban Baban Marina. Ta bu'de murya ta ce "Ki ba shi hakuri". Fuska a daure, amma cikin azama na ce "Allah ya baka hakuri". Daga haka na tsuke fuskata da bakina. Tare muka karya da ita. Sai da zai fita suka tafi tare ya sauke ta a gidanta. Ban zauna ba sai da na yi abinci na zuba a flask. Na gyara ko ina, sannan na fara yiwa wata da ta zo k'unshi. Bai dawo ba sai yamma, kafin lokacin kuwa na yiwa mutum hudu duk sun tafi. Budurwa d'aya ce ta rage da yake ita zan mata bak'i da kuma kitso. Da azama na saki kitson na fita ina yi masa barka da dawo wa, domin ya tsani ya dawo ban bar abin da nake yi, na je gare shi ba. Idan wani ne ya fa'da mini Bulkachuwa zai dinga yi mini irin wannan mulkin mallakar zan k'arya ta shi kai tsaye. Ni da kaina mamakin kaina na ke yi. Na yadda nake rawar jiki a kansa. Wata'kila kuma yadda yake sarrafa ni ne sirrin. Gabadaya tsoron fishinsa nake yi tamkar me. Ya mik'o mini ledar hannunsa mai dauke da karas da atile. Hannu biyu nasa na kar'ba na dinga fa'din "Na gode, Allah ya k'ara budi.". Na wanke hannuna, na yi kicin na ha'da abincinsa na kai masa. Na debo pure water masu sanyi guda biyu na saka a plate. Na ajiye a gabansa. Na fita na debo masa karas da atilen na zuba a bowl na wanke na kai gabansa. Na dan yi jim na kalle shi yana cin abincinsa cikin nutsuwa. A hankali na ce "zan je na k'arisa kitso." Da walwala ya ce "To". Na fita, a raina kuwa sai fa'din nake yi sarkin son mulkin tsiya. Kai Tijjani baka bai ni haka ba, Yasin" Da daddare ya dinga laluba ta, na maze ban yi masa abin da nake yi masa ba. Ya fara ce wa "Amma dai kin san bana son haka, sannan kuma kin san kin ci bashina jiya". Da sauri na ce "Ba wani bashin ka da na ci. Kai ne ka kawar da kai, alhalin ka ce ko mun yi fa'da kada mu saka aurenmu a ciki. Amma jiya sai da ka saka su tsundum." Cikin kwantar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161