Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

duniya shine Gwaggo ta ce mini aurena da Yaya J ba zai yiwu ba. Na yi k'asa da kaina a hankali na ce "Gwaggo fa'da mini dame ya fini da kike ganin yafi k'arfina?" Ta murmusa ka'dan ta ce "Saboda Babanki ba shi da arziki, sun tsere mana, sannan uwarsa tana da buri a kansa, bayan haka ga Mama k'ut take da uwarsa, dan haka zata yi dukkan mai yiwuwa ta sake b'ata lamarin tunda akwai haske a tare da shi, ba zata so wannan hasken a tare da ke ba. Sanin kanki ne kuma mutanen gidan nan baza su dauke ki su ba shi ba, tunda kuna da yawa, zasu yi kwarya tabi kwarya ne a tsakani. Da ace ke din diyar Baban kasuwa ce to, da ba fargabar da zan yi". Na numfasa k'irjina ya daure ainun. Na dinga tambayar kaina shin zan iya rabuwa da Yaya J? Da gaske har lalacewar zumunci ya kai za a iya hanamu aure ba tare da wani dalili gamshasshe ba? Ashe har za'a iya ture karfin jini saboda kawai dan-uwanka ba shi da wadatar abin duniya? Na sauke nannauyan numfashi na ce "Ki daina damuwa Gwaggo! Ban tsananta ba, ban kuma dage sai shi ba. Ki cigaba da yi mini addu'a". Ta sake kafe ni da ido ta ce " Ina yi miki addu'a sosai Yabi, amma zata yi tasiri ka'dai idan kin barwa Allah ya yi miki zabi, kin kuma yak'i zuciyarki akan Jabiru. Ina nufin ki rage zurfafa a al'amariinsa." A sanyaye na ce "To Gwaggo". Sai kuma na zauna ina taya ta k'ulla sigan ina bata labarin yadda ta kaya a tsakanina da Dada. Ta nisa ta ce "Ba kya jin magana ne, ban da hakan mene ne zaki dinga janyo wa tana yi miki mugun fata? Kinsan kuwa bakinta zai kama ki domin ita ma uwa ce a wajen ki". Jikina ya sake yin sanyi, na dinga yin addu'ar Allah yasa na daina tanka mata akan Shehu tunda mafi yawa saboda hakan take fusata. Ta ke tsanata mini, har take yi mini mummunar addu'a. Washagari takwas saura muka d'unguma zuwa makarantarmu ta jeka ka dawo ta gwamnatin jahar Bauchi. Ajin mu hudu wato ss1. Ko wacce tana cikin tsafta, duk inda muka wuce sai an kallemu wataran akan kunnenmu mu ke jiyo yadda ake fadin "y'an Marina ne, kasan yawa ne dasu tamkar tsaki." Ko muji an ce "kai wato gidan Marina akwai zuka zukan zaratan y'anmata fa." Muna tafe ina tambayar Basira da Nazira jiya Dada ta d'ora musu karatun kuwa bayan na tafi?. Nasiba ta ce "Bayan kin bata mata rai yaushe zata iya yin karatu? Kin san kullum sai ta ce haramun ne yin karatun addini a cikin fishi ko a cikin rashin tsarki". Muka k'yal-k'yalale da dariya gaba'daya. Muka isa makaranta hatta Malamai kwarjini muke yi musu saboda yawanmu da kuma yadda muke kama da juna baya ga hakan tare ake ganinmu tamkar kashin awaki alhalin a gidajenmu babu wannan soyayyar da jin kai da ake gani a tare da mu. Lokacin tashi yayi muka dawo a jiga ce a dalilin rana ake yi duk da zafin ranarmu da sau'ki akan ta Bauchi da Jigawa. Wajibi ne idan zamu tafi sai mun shiga mun gaida Dada, haka nan idan mun dawo. Tsabar saka ido da kwakkafin baiwar Allan nan duk wacce bata je ba sai ta ga ne, hakan kuma na iya zama sanadin rikici a gidan, domin bai zame mata komai ba, ta kira uwar yarinya ta yi mata tass, ta ce da sa hannunta y'arta ta raina ta. Kuma abin mamakin idan baka kama sunanta ba, to da kai da wacce bata je ba daidai kuke. Ina tsaye suka dinga shiga suna fitobwa ba abin da ake ji sai "Dada mun dawo, sannu da gida" . Yayin da ita kuma take kama sunan kowa tana cewa "Sannunku da dawowa, lale da y'anmata Dada". Sanin da na yi garina da tsakuwa da ita, ya sanya nake jingirta wa sai na je gabanta sosai ta yadda zata shaida ni da kyau. Tunda kullum sai na je, amma idan ta so ci mana mutunci ni da Gwaggo sai ta ce ban je ba, ko kuma na yi mata gaisuwar gadara da wulakanci daga bakin k'ofa Dan haka da na k'ara wayo sai nake isa gabanta mu hada ido sosai sannan na yi gaisuwar. A gajiye na k'arisa k'ofarmu na tarar da bacin rai domin tsagwaya na tarar an yi a matsayin abincin rana, wani irin nau'in abinci ne da ake sirfa dawa sai a dafa a ci da manja. Na tsani abincin ba dan babu da'di ba, sai dan kawai bana so. Na zauna a tsakar d'akin Gwaggo ina kunci sosai. Ta shigo ta kalle ni ta ce "ban ga kin cire inifom din naki, kin yi sallah kin zuba abinci ba?" Na tumbatsa da fishi ban tanka ba. Ta kafe ni da ido ta ce "Yabi kullum aka yi tsagwaya sai kin tayar mini da hankali? Sanin kan ki ne mahaifinku ya saka takunkunmin siyo abinci a waje ko a ro'ko a wani waje. Me yasa ba zaki rufe ido ki ci dan ta yi miki maganin yunwa ba? Idan kin yi ha'kuri ai wataran barin gidan zaki yi, ranar da Allah ya kai ki dakinki komai kike so sai ki yi wanda bai wuce wadatar mijinki ba". Cikin bacin rai na ce "Ki taimake ni ki bar ni na jika gari na sha, Allah ya sani yunwa nake ji kamar na mutu". A sanyaye ta ce "To ki jika amma nafi son ki dinga ci tunda idan kin ci din ba illah take miki ba." Haka na jika gari na bu'de jakar makaranta na dauko gyada maro na bushe na zuba, ina sha, ina fa'din "ba dan na k'osa ba, da Iklima ta siyo mini madara, to aikenta bana me sauri bane ko wanda yake a matse irina, domin shad'arta ta yi yawa". Gwaggo ta girgiza kai ta ce "Ke dai duk salon k'wadayi kin san shi, ki dinga bin duniya a sannu sannu Yabi". Na yi dariya na ce "Gwaggo tuni aka daina bin duniya a sannu. Saboda gaggawar mutanen cikinta ba zasu bar mai binta a sannu ya kai ga gaci ba, yanzu da nake yin kitso na ha'da da lalle ba gashi muna d'an samun taro da k'wabo ba, da sannu nake bi iya kitson kawai zan yi Gwaggo. Yanzun ma so nake na koyi wata sana'ar na sake ha'da wa domin ina da burin na samu ku'di masu nauyi na jiyar da ke da'di, na jiyar da su Iklima". Ta girgiza kai ta murmusa ta ce "Na gode sosai Yabina! Allah ya ida nufi, amma dai ki bi a sannu da ikon Ubangiji komai zai saukaka a gareki, kullum sai na rokar muku kada a jarrabe ku da rashin abincin a gidan aurenku kamar yadda aka jarrabi Yayarku, ita ma ina fatan da'di ya biyo bayan wannan wahalar da take ciki". A sanyaye na ce "Allah ya amsa bakinki Gwaggo". Ina kammala wa na yi haramar sallar azahar, sannan na shiga wanka dan shirin tafiya Islamiya. Dai-dai lokacin Babanmu ya dawo daga wajen sana'arsa. Gwaggo ce mai girki

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161