Chapter 11
Chapter 11
marubuciyar akan lambarta 08167768704 domin samun free pages na labarin kai tsaye, kafin ku kai ga yin payment.Kar ku manta it's a true life story,don haka ku hanzarta shiga cikin tafiyar da babu ✍🏻 danasanin bin alƙaminsa.... * *Shafin nan kyauta ne sukutum ga mamana* *Hajiya Hadiza Sodangi* *Na gode sosai Ubangiji ya shirya zuria* 7&8. Maganar Baban Marina ta dawo da ni tunanin da nake yi. Kamar a sama na ji ya ce "Na gode miki Asiya! Duk yadda nake jan kunnenki akan b'atawa Dada rai, da kuma dukan yaran gidan nan ba kya ji, saboda kin riga kin zama y'ar kuka. Uwarki kullum cikin yi miki kashedi akan shiga fa'dan yara da kuma tsokanar Dada, amma duk a iska ko? Na gode sosai da wannan bacin rai da kika sanya ni, Allah ya shirye ki". Ya tsugunna gaban Dada ya ce "Ki yi ha'kuri! Halin Asiya ni kaina ha'kuri nake yi da ita, amma zan dauki mataki akan ta'ba ki da take yi". Ta kyabe baki ta ce "To ka fara dan takidin aurensu. Jiya mun tattauna da kannenka sun ce su babu matsala ko yaushe auren ya zo a shirye suke, kai dai za'a fa'dawa ka fara tanadin tunda yaran ka har biyu ne". Ya yi gyara murya cikin k'arfin hali ya ce "Babu damuwa Dada ina saka rai Ubangiji zai kawo mini hanyar da zan samu na yi musu iya abin da zan iya." Ta murmusa tamkar ba ita ce mai kuka tana face majina ba. Ta ce "To babu laifi Allah ya basu na gari, masu kuma ha'kuri, domin mai yakana ne zai iya zama da Yabi dan wuyar zamanta ya kai inda ya kai, ba inda ta baro uwarta". Cikin sanyin jiki Baba ya mike yana cewa"Dada sai da safe mu kwana lafiya". Ta amsa masa da fa'din "Allah ya tashe mu lafiya". Na mike, Nazira ma ta biyo ni muka fice, ba tare da mun ce uffan ba. Domin na sake fusata da ta ce sun tattauna da kannensa amma shi ba'a saka shi cikin zaman ba. Muna jin ta tana fa'din "Wanda Allah ya bashi tsawon rai zai yi kallon tak'ama a wajen ki Yabi. Yarinya da ke amma kusan ke kike juya shashinku gaba'daya. Kina tashi Yayarki ta biki zungui zungui ko sallama ta kasa yi mini saboda tana rarrashin zuciyarki?". Ban juya ba, bare na tanka mata, balle kuma Nazira da take da sau'kin hali. Muna shiga shashinmu muka yi turus a dalilin halin da muka ga mahaifinmu a ciki, zaune yake akan tabarma a tsakargida. Sai fifita Gwaggo take yi masa, gumi na yanko masa babu kakkautawa. Muka isa gabansa, muka tsugunna, baki na rawa na ce "Sannu Babanmu! Abin mamaki sai ya daga mini hannu tabbacin ya amsa gaisuwar tawa. Nazira ma ta yi masa sannu ya amsa ta hanyar gyada mata kai. Mama ta fito daga bandaki ta kalle ni ta ce "Wannan ja'irar yarinyar sai kin zama sanadin mayar da kananun ya'yansa marayu, fitananniya tabtacciya. Ai duk gwanin na iya a rana ya ke" Ta ja tsaki mai tsanani ta wuce d'akinta. Bata jima da shiga ba ta k'walawa Nazira kira, ta mike a hanzarce ta nufi dakin nasu. Daidai lokacin Baba ya dan samu sau'kin zufar da take karyo masa. Ya yafito ni, jiki na rawa na isa gabansa. Ga mamakina sai ya mik'o mini hannunsa na dama. Hannu bibbiyu na ri'ke hannun nasa, cikin barin jiki gaba'daya. A sanyaye ya ce "Ina alfahari da ke Yabi! Kafatalin ya'yana ke nake da tabbaci akan ba zaki cigaba da yin mini *Bak'ar Ta'ada* ta y'an ubanci ba, na tabbatar da hakan. Ina saka rai ta dalilinki yarana zasu dawo tsintsiya. Na so ace da wuri na haife ki Yabi. Da al'amuran da suka dame ni basu yi mini tsananin da nake ciki ba. Amma Alhamdulillah! Ubangijinmu baya kuskure na gode masa, ina kuma tuba a gare shi." Hawaye tuni ya goce mini dukkan zuciyata a jagule take da tsananin tausayin Mahaifina da a yau nake ganin wani irin tashin hankali da raunin da ban ta'ba ganinsa a ciki ba. Gwaggo tana fifita, tana kuma share k'walla.y Ya numfasa ya ce "Idan na mutu Yabi, duk runtsi ku gaisa da yan'uwana, ko ba zasu taimakeku ba, to lallai ku dinga saka su a cikin al'muranku, idan kina yi, sannu a hankali zaki samu wanda zasu yi koyi da ke, tunda tun yanzu al'amura sun haska ke ce mai tsayayyen ra'ayi wanda yafi kusa da kyau da kuma dace wa." Murya na rawa na ce "Mu sasu a alamuranmu ko da ba zasu taimakemu ba, ko da idan mun fa'da musun ba zasu dauki al'amarin namu da girma ba?" Ya sake damk'e hannuna ya ce "Haka nake so Yabi". Da karfin zuciya na ce "Da Ikon Ubangiji zan yi yak'i da dukkan zuciyata na yi hakan. Amma ina ro'kon arziki ka mini afuwa, ka yafe mini muzancin da na janyo maka dazu". Ya girgiza kai ya ce "Baki yi laifi ba, na sani. Sannan su d'in ma bana son ki d'auki abin da suka yi mini a matsayin muzanci ko tozarci, na sani baki da sauki, kina da ru'ko, dan haka na umarce ki, ki manta komai". Na murmusa hawaye na kwaranyo wa na ce "Shi kenan Babanmu! Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, yadda a ke mini habaicin tunda aka haife ni ka tsiyace, ina ro'kon Ubangiji kullum, ya saka idan na girma na samu sanadin da arzikinka zai dawo ta dalilina fiye da wadda ka rasa a shekarar da na iso duniya". Ya ce "Rabu da maganar jahilai, ko iya hakan na ga ni ai na gode, sanadin sana'arki na daina fargabar a tambaye ni ku'din sabulu a gidana. Alherin da kika janyo mini mai yawa ne, mafi farin-ciki a ciki shine wanda kike yarda ya'yan da na haifa duka daya ne a wajenki ta fuskantar mua'amala ta zahiri." Da'di ya tsirga mini ban ta'ba zaton Baba ya fahimci yadda nake da ra'ayin rikau akan kannena ba, bansan ya fahimci ina tare musu fa'da ba, hakanan ban san hakan yana yi masa da'di ba, tunda kullum a cikin kirarin bani da hakuri yake. Sannan kuma baya ta'ba nuna mini ina abin a yaba, sai dai ya ce ai duka yan'uwane tunda ragowar ma y'ay'ansa ne da yan'uwansa suka haifa masa. Cikin son na sake k'arfafa nasa guiwa na ce "Duk d'an da ka haifa ina jin sonsa har cikin zuciyata Baba". Idonsa ya ciko da k'wallah cikin k'arfin hali ya ce "Allah ka shirya mini yarana, ka saukaka musu, ka basu lafiya, ka cika zuciyarsu da tsoronka, ka jefa soyayya da tausayin juna a tsakaninsu. Allah ya yi miki albarka Yabi". Daga ni har Gwaggo muka hau fa'din "Ameen ameen". Na kalli Gwaggo na ga hawaye ya goce mata, jikina ya sake yin sanyi, domin ita din wata irin mace ce mai k'arfin zuciya k'warai da gaske, abin da zai saka ta yi kuka to kuwa ya girgiza ta ba ka'dan ba, duk tsananin da take fuskanta a rayuwar gidanmu ban ta'ba ganin ta yi kuka ba. Na yi kasa da kaina cikin rauni mai yawa na ce "Ameen Baba! Allah ya kara maka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161