Chapter 96
Chapter 96
ce. Amma haka kawai nake jin fargabar zakewarta a wajena domin na riga da na sani mijina yana son yan lukataye irin ta. Ni kuma yar firit ce. Sannan bazan yaudari kaina ba, zai iya sha'awarta tunda jikinta rugu rugu ne, kuma bayltw damu ta saka mayafi ba. Tunda tana ganin ba sai ta fita waje da ta shigo ba. Bugu da kari ba Hausawa ba ne. Wasu abubuwan nasu da namu akwai banbanci. Haka dai nake ta daure wa ina ta k'ok'arin ban bar shi da kewa ba. Komai yake so sai na yi masa. Ba kuma na tab'a k'osawa da al'amarinsa duk da nima ina son harkar. Amma bana ja masa rai saboda kada ya ga ni a waje ya yi sha'awa. Ba kuma na nunawa ya gundure ni. Ana cikin haka aka tashi bikin. Ihsan k'anwarsa. Tun saura sati biki na tafi, saboda a fara komai da ni, sannan ni ce zan mata k'unshi da kitso. Babah sai ina ka saka take yi da ni. Yadda ta ga na murje na yi kyau ba karamin da'di ta ji ba. Na sani kuma da a ce da goyo na je mata da tafi haka murna. Shi da kansa ya kai ni. Washagari ya tafi akan sai nan da kwanaki ka'dan zai juyo. Komai sai da na bar masa, hatta miya sai da na soya masa, na yi masa cincin. Kawai tafasa farar taliya ko shinkafa zai yi sai kuwa shayi. Ana gobe biki y'an Toro suka iso. Aka yi hidima cikin rufin asiri taro ya tashi lafiya. Kwanaki biyu a tsakani ya zo muka tafi shake da kayan biki masu yawa. Tunda muka yi aure bamu ta'ba nisa da juna ba sai wannan karon. Duk da dai a Bulkachuwan ma ranar biki sai da ya faki ido ya jani muka je wani waje ya yi abin da zai yi sannan ya dawo da ni. Amma muna isa gida ko hutawa bamu yi ba. Daki ya ja ni bamu fito ba sai da ya samu nutsuwa. Da daddare ina zaune a cinyarsa sai ce mini ya yi "Little baki da nauyi, shafal ban ji kin danne ni ba". Na zabura na kalle shi, gabana ya fa'di sosai. Da rawar murya na ce "Sai yau ka fahimci haka? Wa ka d'ora a cinyar da yanzu baka ji yadda kake so ba?" *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Ya daburce ya ce "Wallahi babu kowa Yabi". Fa'din Yabi da rudun da ya shiga sai yasa na kasa gasgata shi amma kuma na danne na ha'diye saboda babu kyau zargi. Duk yadda na so na bar maganar amma a zuciyata sai wasi-wasi nake yi. Na kasa samun nutsuwa. Hakan ya fara shafar walwalata. Ban sauya masa ba, ba kuma na bijire masa amma kuma babu shiriritar da nake yi masa a baya. Rannan na ce masa ina son na je gida na yini. Da rawar baki ya ce "To, yaushe zaki je?" Domin ya takura da rashin walwalata. Na ce "Duk ranar da ka ce". Ya ce "To gobe sai na kai ki" Haka kuwa da kansa ya kai ni, muka fara isa k'ofar Dada muka gaisa. Tana ta barkwancinta da karatunta. Ban wani jima ba na tashi na nufi k'ofarmu." Ya shigo suka gaisa ya ce mini zai tafi da yaushe zai zo ya d'auke ni? Na ce "ko yaushe ma". A k'ok"arinsa na son ya kyautata mini sai ya ce "Tom idan an idar da Isha zan zo". Na ce "Allah ya kai mu". Ya tafi. Na yini cikin iyayena cikin nutsuwa da walwala. Da yamma lis Gwaggo da Inna zasu je duba yar kanwar Mama da ta haihu kusa da unguwarmu ne. Dan haka Baban Marina ya ce "Asiya sai ku je tare ki rakasu idan kin dawo sai ki shige gidanki". Na amsa da ce wa "To Babanmu, domin idam Gwaggo ta fita ba jin da'din zaman zan yi a dakin ni ka'dai ba, tunda Ikilima ta tafi Islamiya, shima kuma Baban fita zai yi. Mama kuwa babu wata ma'amala mai yawa a tsakaninmu. Dan haka muka tafi tare. Da muka dawo na yi lungun da zai sada ni da gidana, su kuwa suka mik'e suka koma nasu gidan. Haka kawai nake jin nauyin jiki na saukar mini. Wani irin b'acin rai ya ziyar ce ni da na karyo kwanar da na fara hangen gidanmu. Haka nake tafe ina ta jin fargaba. Ina kuma ayyana abubuwa marasa da'di a zuciyata. Nan da nan na fara ta'awizi ina kore shaid'anin da yake son yin wasan kura da zuciyata. Har cikin zuciyata ina son Tijjani, ina son na rayu da shi. Domin a zaman da muka yi na shekara daya da kusan rabi na tabbatar yana da kyawawan dabi'u. Na farko shi mutum ne mai mutunta sallar farillah. Sannan mai yawan tsayuwar dare ne na shaida hakan. Domin duk lokacin da zai shafe yana tiritiri da ni da daddare, to da zarar k'arfe uku ta yi kuma zai tashi ya yi wanka. Ya yi ta yin munajati da Ubangijinsa, wani lokacin ya matsa mini na tashi, wani zubin kuma ya k'yale ni na yi barcina. Sau tari kuma idan ban tashi ba, da asuba idan ya tashe ni sai ya ce "Tashi ki yi sallar farillah akan lokaci, na raba dare ina roka miki alherin duniya da lahira my little". Bayan hakan na karance shi yana da matu'kar son ya kiyaye ka'idojin da shari'a ta d'ora masa mussaman na ri'ke gida da kula da tarbiyata. Sannan ba shi da mugunta ko ka'dan har yau din nan Tijjani bai ta'ba saka mini ido akan ku'dina ba. Asalima kullum cikin k'ara k'auwame kansa yake yi da abin hannuna. Sannan ya iya Soyayyar da duk taurin zuciyar mace sai ya dargaza ta. Ga kuma girmama iyaye, yana mutuntata manya kwarai da gaske. Wadannan dabi'un da ya siffantu da su ya sanya nake hakuri da inda yake kuskure mini, hakan ne kuma dalilin da yasa na k'i yarda na k'arfafa wa kaina zargin ko ya koma Bak'ar Ta'adar sa ta baya. Na shiga zauren na ga kofar tamu a rufe ruf. Na fara tunanin ai ban fito da mukulli ba, tunda mun yi shi zai zo ya dauke ni. Na zaro waya da nufin na k'ira shi ya zo ya bu'de mini, sannan na wuce k'ofar Maman Safiyanu na jira shi. Sai na jingina da k'yauren k'ofar ga mamakina sai na ga ta bud'u. Na tura a hankali na ga sakata a ture tabbacin an saka bata shiga ba ne. Na shigo a hankali. Amma sai na ci birki na tsaya cikin tsananin tu'ajjibi da mastanancin mamaki mai yawa. Jikina ya d'auki b'ari, zuciyata ta yi nauyi ainun. Amma idona
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161