Skip to content

Chapter 89

Chapter 89

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

na kai kicin na shiryasu. Na ba shi gudar dubu akan ya siyo mini gawayi rabin buhu, da kuma danyar kubewa. Domin na tsani siyan abu dan tsurut a leda kullum. Ina da gas amma na bar shi sai iya da safe zamu dinga amfani da shi. Ya siyo mini bushasshe kuma manya dan jos haka ma kubewar. Na ce "To je ka dawo anjima ka'dan." A lokacin kuwa yammaci ne sosai. Dan haka na ha'da wuta na dora tuwon garin masara wanda yana cikin siyayyar da na yi d'azun. Na gama na kwashe na mayar da miya. Magariba tana yi ina kammala wa. Sai da na yi sallah, na yi wanka sannan almajirin ya dawo. Na zuba masa ya tafi. Sai ga Tijjani ya dawo. Ya kalle ni na ci kwalliya ko'ina kamshi ke tashi. Ya kalle ni da alamun tausayi ya ce "Sannu da gida. Ya mik'o mini ledar hannunsa wacce awara ce. Na kar'ba tare da godiya. Na tashi na gabatar mana da abinci, na zuba mana a plate guda. Na ce "Bismillah". Ya girgiza kai ya ce "Na gode". Na zuba masa ido murya na rawa na ce "Ba zaka ci ba, bayan na tabbatar da yunwa a tare da kai! Da rauni sosai ya ce "Ni ni ne mai ciyar da ke, ba wai na zauna ki ciyar da mu ba". Na tashi na koma kusa da shi na ru'ko dukkan hannuwansa na sassauta murya na ce "Ba ciyar da mu zan yi ba. Ubangiji zai buda maka k'ofofin da zaka samu ka sauke nauyin rik'on iyali tunda shi ya wajaba maka. Kana kuma da niyyar yi d'in. Abin da nake so ka fahimta ko aure bai ha'da mu ba, ai jini ya ha'damu. Ko ina wani gidan idan ina da ikon kula wa da iyalinka ai zan yi, bare kuma ni ce iyalin naka, to mene ne amfanin sana'ar da ka bar ni nake yi alhalin ba zata yi maka rana ba?" Ya yi shiru bai ce komai ba, na sake sassauta murya na ce "Dan Allah ka yarje mini na yi iya abin da zan iya yi". Ya saki gauron numfashi ya ce "Idan na amince ya tabbata dai da aka ce ke ce zaki ciyar da mu Asiya. Shike nan zan rasa yancina na mai gida, shike nan zan zama mata, ke ki zama mijin". Ya fa'da murya na rawa ainun. Na durk'ushe a gabansa na ce "Wallahi ba zaka zama ba. Yadda muke hakan zamu cigaba da tafiya kai ne miji. Ni ce mata, zan dinga karban umarni daga gare ka, abin da kake so hakan za'a yi.". Ya yi shiru yana nazari bai ce komai ba. Na matse hannunsa na ce "Pls mana" cikin sigar shagwaba. Ya zuba mini idonsa da ya kad'a sosai ya ce "Asiya zuciyata ba zata nutsu ace kina siya mini abinci a gidan nan ba. Gara dai ki bari na dinga baki abin da aka yassare mini, idan ma zaki kara da abin da kike so to bazan hana ki ba, tunda ban wadatar da ke ba. Amma ni kada ki yi da ni. In sha Allah ko da bashi ne dai bazan kasa baki abin da zaki saka wa ba'kin salatinki ba. Sai idan kin raina". Na kalle shi na gane da gaske yake yi. Na yi k'asa da murya na ce "Anya kasan kalubalen da yake tare da cin bashi kuwa mussaman a waje? Kawai ka yi hakuri tunda dai Ubangiji ya baka matar da ya bata sana'ar hannu mai k'arfi. Ina fatan Ubangiji ya kawo maka aiki ko sana'ar da zaka dogara da ita." Ya girgiza kai tabbacin bai gamsu ba. Na ce "To shike nan ka dinga karban bashin a wajena." Ya gyara zama ya ce "Nawa kika kashe a hidimar tuwon?" Na ce "mu je kicin a lissafa. Ya mike muka je. Na nuna masa komai da aka siyo wanda a k'alla zamu kai wata muna ci a talau ce. "Nawa kika kashe a wannan siyayyar? Na ce dubu sha bakwai da dari shida na. Sai gawayi na dubu daya." Ya ce "To kub'ewar fa?" Na ce "A bar wannan". Ya girgiza kai. Da sauri na ce "Ta naira dari ce." Ya ce "Sha takwas da dari bakwai ke nan ko?" Na ce "Eh" ya ce "In sha Allah zan biya ki, matu'kar ina shakar numfashi." Muka koma falon muka ci abinci ina ta yi masa hira dan ya ware sosai. Wannan kayan abincin da muke da shi sai ya rage masa damuwa mai yawa. Duk da hakan kuma bai yarda ya zauna a gida ba. Kullum sai ya fita. Rannan ya yi sa'a ya samu hada saltelite har gida uku. Da k'arfinsa ya dawo ya mik'o mini dubu biyar ya ce "Ga shi, na rage miki bashin ki. Ya fita ya dawo da leda mai d'auke da soyayyen kifi. Na kar'ba tare da addu'ar Allah ya kara budi. A wannan tsukun gaba'daya a takure nake domin maimakon na samu ninkin tattalin da yake yi mini kafin mu shiga tsananin da muke ciki. Sai ya zamana ni ce nafi rawar kai a kansa domin dai na samar masa nutsuwar shine mijin. Tunda na lura yana kame wa ne dan kada na samu dama a kansa. Na dinga mamakinsa domin gaba'daya ban yi zaton zai mini kallon zan raina shi dan ya shiga halin babu ba. Ya takura kansa sosai, komai kaffa kaffa yake yi. Idan na yi kamar zan yi masa magana sai na ha'diye. Na dinga hakuri ina lallabawa ina binsa a hankali. Hidimar da ta karu a kaina sai ya zama ina ta kokarin fa'dada kasuwancina. A dalilin an kawo wa Tijjani takardar biyan ku'din gida tun kwanakin baya. Na fara tunanin yin Home service domin na samu na tara masa ku'din kafin lokacin da suka diba mana ya cika. Na kalli yatsun hannuna guda biyu gold ne. Daya na wajen kwamishina ne, dayan kuwa da sana'ar tawa na siya. Jiya na bashi daya na ce ya siyar ya biya ku'din ya ce "Ba ya so, kada na sake na siyar da kadarata akan al'amarin da ba hakkina ba ne. Idan kuma na siyar to ba zai karba ba. Da zai fita na tambaye shi zan fita, zan je bayan layinmu. Bai hana ba. Tunda na fita da hantsi ban dawo ba sai yamma lis tunda asabar ce ban cika samun k'unshi a ranar ba sai kitso. Na dawo na tarar da shi a gida. Ya gyara ko ina. A falo na tarar da shi yana kallo. Na yi masa murmushi ya mayar mini a gajarce. Ya kalle ni ya ce "Daga ina kike na ji sai k'amshin muhallibiya kike yi" Zuciyata daya na ce "Wallahi lalle na yiwa wata babbar mace da ahalinta zasu je biki Abuja. Na fito da kudina dubu sha biyar na ajiye masa na ce "Idan Allah ya yarda a satin nan zamu ha'da ku'din da zaka biya gidan". Ya zuba mini ido galala sai kuma ya kad'a kansa ya ce "Babu laifi". Ni ban kawo komai ba. Na tashi na yi kicin da nufin dora girki. Sai na tarar da ya girka ya juye a flask. Ga shi ya mayar da ruwan

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161