Chapter 60
Chapter 60
Hakan ya sanya na tashi na yi tamkar na je wajensa, nan kuwa dakina na shiga na zauna bakin gado. Tamkar mai jirana sai gashi ya shigo mini. Ya kaurara murya ya ce "Asiya Toro ba ki ji kashedin da na yi miki ba akan shigar mini daki da mata ba ko?" Na murguda baki na ce "Ban ji ba Tijjani! Ba kuma zan ji ba". Ya ce "Shike nan" Na riga shi barin dakin. Ina kallon yadda ta shirya masa abincin a tray, cikin flask mafi kyau a kicin din. Plate din na tangaran ta saka. Maimakon da ta kai ta fito, sai ta yi zamanta suna hirarsu. A daddafe na kammala lallen. Dan da wata ta zo ma ha'kuri na bata, na ce ina da ayyuka mai yawa ga kuma maigidan na nan. Wani irin makakin ba'kin ciki nake ji har cikin mak'oshina. Duk da bana son Tijjani amma na ji zafin kiran Rafi'a da ya yi. Mussaman umarnin yi masa girki da ya bata. Ina da eani irin kishi tun ina karama ta. Har ta kai Gwaggo kullum cikin yi mini addu'ar samun sassauci take yi. K'asan zuciyata kuma ban yarda kishinsa nake yi ba. Tunda ba wai ina sonsa ba ne. Kawai wula'kanta ni da ya yi ne ya mini ciwo.🤣 Sai da ya gama ta fito da kwanukan abincin. Da murmushi ta ce mini "Na gode sosai Amarya. Sai na sake shigo wa". Ga mamakina na kasa yi mata ko da yak'e ne. Murya a dakushe na ce "Madallah". Da daddare ina falo, ina kallo ya dawo. Sai da ya yi wanka, sannan ya shigo ya zauna. Cikin nutsuwa sosai ya ce "Asiya na ce kada ki kuma shiga mini daki da nufin yin lalle ko kitso amma baki ji ba ko?" Yana rufe baki na ce "Tijjani ban ji ba, ba kuma zan ji ba, ka yi abin da zaka yi marar tsoron Allah kawai". Ya yi mini k'uri ya ce "Me na yi miki na rashin tsoron Allah? Ni ban fa'di hakan akan ki ba, sai ke zaki fa'da mini hakan?" Babu fargaba na ce "Ina da tabbacin bana aikata kaba'ira, kai kuwa kaba'irori nawa kake aikata wa? Tsabar shaharar da ka yi a BAKAKEN TA'ADODI har gidan auren ka ma bai tsira da sharholiyar ka ba". Ransa ya baci. Amma da ya fahimci kishin Rafi'a ne ya k'ume ta, sai farin-ciki ya maye gurbin bakaken kalamanta. Da alamun da Rafi'a zai yi amfani ya dinga rama wula'kanta shi da take yi. Ya girgiza kai ya ce "Sharri dai dan aike ne. Mussaman wanda aka ginasu akan zato da jita jita." A kufule ainun na ce "Ba batun sharri a lamarinka. Iya karshen cuta an yi mini. Amma na barwa Allah al'amurana" Na fa'da hawaye na subuce mini". Ya kasa cevwa komai. Tsawon lokaci mun yi jigum jigum! Sai hawaye da suke tsere a kan fuskata. Babu kuzari ya taso ya dawo kusa da ni sosai ya sassauta murya ya ce "Kinsan bana son kukan ki Asiya! Na tari numfashin sa a zafafe na ce "A gidan uban waye baka son kukan nawa? Makaryaci, mugu, bunsuru..! Ai ban karasa ba, na ji wani irin gigitaccen mari a fuskata. Wanda ya sanya na zunduma ihu a matu'kar ki'dime. Cikin fishi mai yawa ya ce "Kin ci uwar karya kin kwana da yunwa Asiya. Kin yi ka'dan ki zagi ubana, ki wanye lafiya. Ashe togaciyar da na yi miki kwanaki a zauren gida baki ji ba? Wallahi ki mutunta ta kan ki, ki kame bakinki daga zagina. Ni zaki ce wa a gidan uban wa? Ubana zaki zaga? Baki isa ba, rashin kunyar ki ya tsaya a kaina. Ni da kike ganina nasan mutuncin iyayena da gaske, ba wai yaudarar ina sonsu a baki ba, amma na kasa kare musu martabarsu a bayan idonsu ba." Ya mike tsaye ya ri'ke kunnensa alamun gargadi. Da kumfar baki ya ce "Billahillazi kika kuma yi mini lalle a daki sai na wula'kanta ki, ke da gayyar ta ki. Sannan yau ne rana ta karshe da zaki yi gigin zagin iyayena. Ki bari, bana so! Idan kuma kin ki ji, lah shakka ba zaki k'i ga ni ba". Ya tafi ya bar ni ina kuka mai tsananin gaske, domin ba k'aramin shigata marin ya yi ba. Tunda ga wannan lokacin gaba ta k'ullu a tsakaninmu mai tsananin gaske. Ya fita daga al'amarina gaba'daya. Baya bin ta kaina, yana dawowa daga sallar asuba zai fice tun gari bai yi haske ba. Ba zai dawo ba sai wajen Tara. Nan ma yana gama uzzirinsa zai sa kai ya fice. Ba zai dawo ba sai dare. A hakan na fuskanci wajen gini yake zuwa. Fitar asubar ne bansan me yake yi ba. Zuciyata har kissima mini take yi lalata yake fita yi. Dan haka na sake wasarsa, na sake jin haushinsa. Bana girki sai dai na saka almajiri ya siyo mini, abincin siyar wa tunda ana yi a makwabta. Ina samun lalle da kitso. Ban kuma fasa yi a dakin nasa ba. Sai dai kafin ya dawo sun tafi, ni kuma zan gyara masa dakin, sai dai k'amshin muhallabiya ya kama dakin. Bai ta'ba magana ba. Ban sani ba, ko dan bai dawo ya tarar da mu a ciki ba. Ko kuwa ya hakura ne?. Cikin wannan yanayin da muke ciki na yi matu'kar rame wa. Na yi baki. Kullum cikin kuka da b'acin rai na ke. A ranar da na cika wata guda a ranar Dada ta zo ganin dakina. Bulkachuwa da kansa ya dauko ta a mashin ya kawo ta. Ta dinga yaba tsarin dakunan. Amma ta kasa gamsuwa da yanayinmu. A sanyaye ta ce "Mai sunan manya Yabi ta sake kankace wa, ta yi duhu, duk da ita fara ce kal. Kai ma dube ka, babu wani annurin angwanci tare da kai." Ga mamakina sai ya sassauta murya ya ce "Kowa da yadda yake fuskantar kalubalen duniyar nan ai. Me nake da shi da zan jiyar da Asiya da'di bare na samu nutsuwa da ita. Na barwa Allah komai. Idan na mutu Dada na yafe miki wannan ha'din da kika jagoranci aka yi. Cike nake da fargabar kada auren namu ya sake d'aid'aita zumuncin gidan Marina." Dada ta dauki salati tana fa'din "Ashe har yau baku shirya ba? Ashe ba kalau kuke zaune ba, shi yasa ka dinga zille wa idan na ce ka kawo ni gidan ka?". A hankali ya ce "k'alau muke Dada." Ta kalle shi ta ce "Tashi ka bamu wuri." Bai yi musu ba, ya fita din. Ta kalle ni ta ce "Haba Hajja Yabi. Me yasa ba zaki kwantar da hankalin ki ba? Mai sunan manya son ki yake irin son nan mai tsananin gaske. Ban ta'ba ganin abin da ya sanyaya shi irin lamarin ki ba. Tun wanccan satin na je gidan Ubaida tana zaune k'alau da mijinta. Sai ke ce zaki kunyatamu?" Na rushe da kuka sosai na ce "Ita mijinta ai baya wula'kanta ta, baya yi mata sanadin da zata kwana ta yini da yunwa. Mijinta mai kamun kai ne. Amma ni kuwa fa?" Kuka ya ci k'arfina sosai. Duk son kan da Dada ta wanzu tana yi a tsakaninmu da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161