Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

sha'aninki tamkar baki da wata damuwa." Na ce "Abin ne yake neman fin k'arfina". Na fa'da, kuka na sake kwace mini. Ta dinga bubbuga bayana tana fa'din "yadda aka yi din ne akwai tozarci a ciki, amma ni dama bana son wannan ha'din domin tsananin da zaki fuskanta mai girma ne. Allah ya sa haka ne mafi alheri. Share hawayenki ki d'oro alwallah ki yi ta nafila tunda hantsi ne yanzu." Na kuwa mike ina share idon nawa, na fita da zummar yin alwallah. Na dawo na tarar da ita, tana ganin kayan da suke cikin ledar. Leshi mai kyau, da mayafin da ya dace da shi, da doguwar riga abaya, da takalmi da jakarsa, sai tarkacen sark'a da abin hannu ga kayan kwalliya da turaruka. Da envelope mai dauke da wasika da kudin dinki. Gwaggo ta ce "Wannan kaya masu daraja haka? Ajiye wa za'a yi sai Babanku ya ga ni". Na tayar da sallah ban ce komai ba. Mama da zata dafawa Nazira kazar aure har da Maijidda ta hada ta dafawa. Ina kallo yadda ta samo tattabaru ta hada da saiwowi ta sake dafa musu. Haka Gwaggo ta maze kamar bata gane ba. *Mai bukatar saiwowin dahuwar kaza ko na tattabaru da sauran kaya na mussaman ta mini magana akan lambata 08032773332*. Ina ji, ina ga ni aka daura auren Yaya J d'ina, da Maijidda. A ranar kam buya na yi, a makwabta na yi kukan da ban ta'ba yin irinsa ba. Na dinga jin wani irin abu tamkar zai fasa mini zuciya gaba'daya. Fa'di nake "Ya Allah! Ya Allah". Idan na tuna nagarta da sanyin halinsa sai na ga ba karamar asara na tafka ba, wacce na saddakar ba zan mayar da irinta ba. Har dare ba wanda yasan inda nake, sai da na ji dirin isowar motar daukan amare sannan na fito. Dan ba zai yiwu ace ban raka Nazira d'akinta ba. Da na fahimci Nazira za'a fara kai wa domin motocin kai ta ne suka fara iso wa sai kawai na fa'da daya daga cikin motocin. Sai a dakinta muka ha'du. Duk yadda ta ke lullube a cikin mayafi said da ta riko hannuna ta ri'ke gam tana sake kankame shi tabbacin farin-cikin da take ciki bai sa ta manta tawa damuwar ba. Sai da kowa ya watse aka bar ni da ita, domin dai bamu da wasu kawayen da zasu kai mana dogon dare. Ta kalle ni ta ce "Mu yi ha'kuri Yabi, kara daure wa, idan muna ganin ki a hakan ba wanda zai samu sukuni. Kinga ma yunwa nake ji, tun jiya da muka ci abinci ban sake saka komai a bakina ba, ba wanda hankalinsa ya kai a bawa amarya abinci, na sani da kina kusa da ni da kin bani". Na ce "Afuwan Adda Nazi, amma ai yanzun nan Malam Yunus zai shayar da ke nama da madara". Ta galla mini harara tare da fa'din aku sarkin magana". Na mike domin na ji ana fa'din mai motar ya dawo. Da k'yar ta bar ni na tafi, tana kuka, ina yi. Kwanaki ukun da suka biyo bayan bikinsu Yaya J sun fi ko wanne tsauri a gare ni. Sa'ar da na yi ma ba a gidan aka yi masa gini ba, a can bayan gari ne da kansa ya gina abinsa sai dai da tallafin Baban Tsakiya. K'aramin gida mai fasali na ban sha'awa, ba burin da banci akan wannan gidan ba. Ko bandakin gidanmu da yake sani takaici, da zarar na tuno bandakina a cikin daki yake a gidan Yaya J sai komai ya wanke mini, na yi ta zumudin zuwan lokacin da zamu yi aure, ashe dai wasikar jaki nake tsara wa. Tayals a ko ina, ga furanni har da fasadabir ya shuka mini, ga bishiyar mangawaro da ni na bayar da kwallon ya shuka, ita ma ta kama sosai. Amma tashi guda aka ruguza mini komai, Maijidda na cikinsa an kuma sake kawata mata gidan da kayan alfarma domin takanas aka tafi Jos aka siyo mata furnitures, ko yaran Baban Tsakiya su Firdausi basu samu gatan ta ba. Haka na dinga rama tamkar ku'din guzuri. Ban samu sassauci ba sai da aka doshi kwanaki ashirin da auren a dalilin na koma zuwa makarantar boko mun shiga aji shida. Da k'yar Dada ta bari muka koma. Gaba'daya na zama shiru shiru, idan ba kure ni aka yi ba, na daina fa'da, ko yara na gani sai dai na rabasu na yi musu sulhu. Amma na daina rama wa wani duka, bare ni na doku da kaina. Duk da yadda na canja ba yaron da yake kuka sabo da ni, ban tsira a wajen mutan Gidanmu ba. Gaisuwata da kyar Baffanina suke amsa wa. Na rasa laifina, zamu gansu tare da Nasiba mu gaishe su, su amsa ta ta gaisuwar cikin walwala har suna ambaton sunan ta amma ban da ni. Na fa'dawa Gwaggo ta ce "Na cigaba da gaishe su kada na gaji suna da hakkin na mutuntatasu. A sanyaye na ce "Gwaggo ni bani da hakkin su sakar mini fuska su mua'amalance ni da mutunci tunda jininsu ce ba agola ba? Nasiba fa ba yar gidan nan ba ce, amma ace ta fini a wajensu?" A duk sadda na yi mata wannan k'orafin dauke kai take yi ta ce "To ai laifukan da kika yi musu ne, da yawa, sannan ita Nasiba ko ba y'ar gidan ba ce amma tana da wata alfarma tunda a ko ina ana son y'ay'an da yar'uwa mace ta haifa, ke ma ai har da halin ki ya sanya suke yi miki hakan". Idan ta fa'di hakan sai kawai na kalle ta na yi shiru, domin na sani ta fa'da ne dan kawai na fahimci girmansu. Ba dan suna yi mini adalci ba. Har sati uku sannan na warware na rungumi zuwa makaranta duk da karatun ma sai a hankali saboda kewar Nazira na damuna. Dada kuwa fa'di take na fito da miji domin wanda za'a bawa Nasiba ya ce "Kowanne lokaci zai iya gama gidansa ba sai bad'i ba, ita kuwa ranar auren Nasiba ita ce rana ta, ko na fito da miji, ko a bani Malam Nata'ala shine damo sarkin ha'kurin da zai jure wa dukkan iya shegena. Malam Nata'ala dattijo ne da yake zaune a unguwarmu mutumin kirki ne kwarai da gaske matansa biyu da yara da dama, tsanagaya ce da shi ma'ana Malami ne mai almajirai. Ban wani dauki maganarsa da Dada ta ambata da muhimmanci ba, illah k'anzon kurege. Kwanci tashi asarar mai rai har aka cinye kwanakin wata da auren su Nazira. Har lokacin kuma ban yarda na je gidanta ba duk nacin aikar da take akan tana nema na. Ikilima ce take zuwa akai akai duk sadda ta je kuma akwai abin da zata bata ta kawo mini na ci ko na sha. Ga wasiku birjik tunda bani da waya duk da an kawo mini har uku amma Baban Marina ya ce "Baya son mu ri'ke waya. Duk yadda Yaya J yake nacin mu hadu gaba'daya na tsike zuciyata, domin yanzu haushinsa nake ji ba ka'dan ba. Kan dole ya koma makaranta tunda ya kammala sawes din da yake yi a Jos. Ina cikin wannan

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161