Skip to content

Chapter 117

Chapter 117

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

ce "Ko ba wajen ki na kawo su ba, har ta yi mini inkarin inda na kai su bare kuma wajen ki ne". Da azama ta ce "Wallahi ba zaka bar su ba, tunda kai ma ba da nufin su kwana ka taho da su ba. Kaya kala daya ka sako musu a leda. Nasan kuma idan sun bata na jikinsu a sauya musu ne iya yau. Ka bari idan ka shiryo su da kayansu sai su zo mini, amma ba haka kawai a shiga hakkin uwa da y'ay'an ta ba". Ya rasa yadda zai yi, a kan dole ya kwashe su suka juya. Ni da nake mak'ale a daki, zuciyata sai tsalle take yi a kan na ga yarana. Da k'yar na daure ban fito ba. Da suka tafi kuwa sai na ji tamkar na ruga a guje na ce "Ga ni nan". Na kwanta lamo. Ina kallon silin. Babah ta shigo yanayin da ta ganni a ciki sai ta yi turus. Ta iso ta zauna a gefen k'afafuwana. Ta sassauta murya ta ce "Nasan zaki so yaranki a tare da ke. Amma ki daure ba jimawa zaki yi ba. So nake ya rikice gaba'daya, ta yadda da kansa zai zo da bakinsa ya fa'da mini ba kya tare da su. Har da ce mini wai kina gida zazzabi kike yi". A hankali na ce "Idon Hamim ya yi ja?" Ta galla mini harara ta mik'e ta na ce wa "Ban sani ba. Idan kuwa haka zaki mini, ki kuntata kanki sai ki zo ki bi bayansu kawai". Ta fice tana ta sababin masifar son y'ay'a da iyayen yau suka mak'alawa zukatansu. Da gaske dai mace tana saurin yin afuwa ga namiji a dalilin yaranta. Domin tun yanzu na fara kewarsu. So nake na bu'de ido na ga suna wasan hawa da sauka a jikina. Na fesar da iskar damuwa. Na sani daga shi har yaran suna cikin kewata mai yawa. Barin ma sarkin kuka da k'ulafaci Hamim. Haka na zauna, ina jin wani irin abu na bina. ** Bulkachuwa kuwa da k'yar ya isa Bauchi domin ya shiga rudun inda zai ga Yabi. Ya kira wayarta yafi sau goma ana fa'da masa a kashe take. Amma ya kasa dainawa. Suna isa gida, dakinta ya dire. Yaran da suka waiwaya basu ganta ba, suka dinga kuka a tare. Shi kansa ji yake tamkar ya bare baki ya tayasu. Gaba'daya azanjinsa ya k'are. Da k'yar ya shawo kansu suka yi shiru. Kwanaki biyu yana tiritiri da su. Sa'ar da ya yi ma ya riga ya saba da hidimarsu. Jiya a Toro suka yini, yana bulayin yiwa gidajen mutane dirar mikiya ko zai ga Yabi. Amma shiru tamkar Malam ya ci shirwa. Komai ya tsaya masa cak. Kan dole ya sake komawa Bulkachuwa da su. Ya rasa ta yadda zai fa'dawa Babah Yabi ta gudu ta barsu. Ya gama kame kamensa ya fa'da mata gaskiya sun samu sabanin fahimta da Yabi ta yi yaji, ya kuma neme ta ya rasa tsawon kwanaki uku kenan. Ta dauki salati mai tsananin gaske. Ta dake ta ce "Yarinyar da ubanta ya damka mini amanarta a hannuna ka yiwa sanadin da ta gudu ta fantsama duniya?" Ya yi tsumu ya rasa me zai ce. Ta ce "Sai ka fa'da mini abin da ka shuka mata har ta kasa ha'diye wa ta bar maka wadannan yaran da suka shiga ranta. Ta tafa hannu tana skae kambaba girman lamarin. Fadi take yi "Duk uwar da tafi ta bar k'ananun y'ay'anta ai ba'kin cikin da take ha'diye wa ba ka'dan ba ne. Tura ce ta kai bango". Ya kasa ce wa komai. Illah zufa da take yanko masa tamkar mai hadiyar kunama. Cikin bacin rai ta ce "Ya ya ina magana ka mini shiru sai zare ido ka ke yi irin na rashin gaskiya". Murya babu amo ya ce "Wallahi ba komai na yi mata ba. Nasiba ce ta zo shike nan ta kwarzabi kanta." "Ta kwarzabi kanta kamar ya ya?" Ta tambaya cikin wani irin yanayi na bacin rai mai yawa. Ya numfasa ya ce "Ce wa ta yi sai na kore ta. Ni kuma na ce bazan kore ta ba. Shi kenan na dawo na tarar ta bar gidan". Ta rausayar da kai ta ce "To ai Yabi ta yi adalci. Sai da ta fa'da maka bata son zamanta. Kai kuma ka nuna kana da bu'katar ta zauna a gidan tunda naka ne. To mene ne kuma dan ta fita ta bar muku gidan ku tabbata a ciki?". Ransa ya baci ainun. Ita ma bata fahimce shi ba. Su duk haka mata su ke da kishi ne?. Basa fahimtar komai matu'kar akan kishi ne. A hankali ya ce "Yanzu dan Nasiba ta zo shi kenan sai ya zama masifa? Ta ce sai ta bar gidan? Duk zamanmu da ita bata gasgata ni ba ke nan? Ni ba kula ta nake yi ba, bare ta ce ta fahimci wani abu a tsakaninmu. Wallahi saboda sababin Yabi ko kallon inda ta ke bana yi. Amma hakan bai yi mata. Shin Nasiba ba zata zo gidana ba, ba yar'uwa ta ba ce?". Babah ta girgiza kai ta ce "K'warai yar'uwar ka ce ta gaske tunda har ka zabi fishin matarka akan ta. Madallah da Yabi bata za'bi zaman muzanci ba. Ta daga hannuwanta sama ta ce "Allah kasa yarinyar nan tana hannu na gari. Allah kasa tana Kangire ko kaduna gidan Jabir". Nan da nan ya muzanta. Ya kasa yin shiru ya ce "Kaduna! Ya fa'da cikin takaici mai yawa. Ya kasa yin shiru da rawar murya ya ce "Na rantse idan aka same ta a Kaduna duk masifarta sai ta ga ne bata iya komai ba". Ta galla masa harara ta ce "To me zaka yi ne? K'arshe dai ka sake ta. Ni kuwa Wallahi tana gama idda zan bada aurenta ga saurayi ma, don bazan yarda ta fita daga ahalina ba." Idonsa ya kad'a ya yi jawur. Da rawar murya ya ce "Babah a gabana kike nuna zaki bawa k'anina auren matata?" Ta bu'de murya ta ce "Na fa'da na ji ruruf!". A matu'kar ki'dime ya ce "Allah ya huci zuciyarki. Allah ya tsare ni aikata irin wannan BAK'AR TA'ADA din". Ya bata tausayi ainun. Amma ta cije ta ce "Akan idona uwar Nasiba ba abin da bata fa'da akan ka ba. Ita ta hana a baka aurenta saboda suna ganin ka baka da mamora. Amma Yaya Sani ya juyawa dukkan nak'asunka ya tursasawa Yabi auren ka sai kuma dan ka fara samun dama, ka fara shiga sahun mutane sai a yi maka shunen ta har cikin gidan Yabi! Ta yi shiru. Saboda yadda zuciyarta take jin tsananin zafin yadda aka tado mata tsumin bacin rai na tsawon lokaci. Ta zuba masa ido wanda rabon da ta yi masa haka ya manta. A kaurare ta ce "Nasiba ba matarka ba ce, ko bayan raina ba zata zama matarka ba. Shari'a ta halasta ka aure ta babu aibu a cikin hakan. Amma kuma shariar da kanta ta ce "ku girmama ra'ayin iyayenku sama da naku. Matu'kar ina da hak'ki akan ka Wallahi na haramta maka ita. Soko marar tunani. Har ka manta tozarcin da uwarta ta yi mini

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161