Skip to content

Chapter 66

Chapter 66

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

take rataye. Ya yi baya, ya sanya. Ya dawo ba'kin kofar ya ce "Darajar wannan baiwar Allah kika ci, tana gidan. Na rantse miki da yau kin ga k'arshe taurin kai da tsiya." Ya kalli Hajiya ya ce "Na gode sosai, amma dan Allah kada ki sake ta'ba ta. Ki yi ha'kuri". Yasa kai ya bar gidan gaba'daya. Y'anmatan nan suka kasa ce wa komai amma dai gaba'daya sun shiga rud'anin al'amarin da ya faru. Ta tashi, ta fita tana fa'din "Zan je har gidanku na sanar wa Gwaggonki baki shirya zaman aure ba. Gara ta sani kada rana daya ta gan ki kamar jifa kin koma gabanta. Ke ko tunanin halin da take ciki ba kya yi? Tare da kanwar ki aka aurar da ku. Tana zaune k'alau, amma ke kin fitini kanki kin fitine shi." Na dinga kuka ina bata hakuri akan kada ta fa'da wa Gwaggo fishi zata yi da ni. Da k'yar ta yarda ba zata fa'da ba. Bayan ta ce na kira mata shi a waya. Akan dole na kira shi. Na danna speaker. Yana dauka sai ce wa ya yi "Bebina kin daina kukan? Ki yi ha'kuri kin ji. Ai da nasan mutumiyar kirki ce irin haka da bazan yi hakan a gabanta ba". Ba'kin cikinsa ya nemi kassara ni. Na mika mata wayar cikin b'acin rai. Jin muryarta ya sanya ya shiga cikin nutsuwa sosai. Bai bari ta ce komai ya fara bata ha'kurin abin da ya yi. Ta ce "Tambayar ka zan yi. Baka son ta yi k'unshin ne?" Da sauri ya ce "Ina so. Ai bazan hana ta sana'ar da ta kafu da ita ba. Amma dai dole ta bar abin da na ce mata. Na ce kada ta kuma yi mini lalle a d'akina, ta je ta yi a nata d'akin. Shine kawai rikicina da ita". Ta ce "To shike nan. Magana ta k'are." Ta kashe wayar ta murd'e mini kunne tare da ce wa "Dama can dakinsa ne, amma kike masa k'unshi a ciki? Saboda ke tabbataciyar marar kunya ce? Amma yanzu ai kin ga 'karshen tsageranci." Ta saki kunnena ta tashi ta bud'e wadrof d'ina ta ga dukka kayana ne babu nasa ko daya. Ta sake kai kallo ga d'akin ta ga babu alamun hula ko wani abu na miji a ciki. Ta daure fuska ta ce "kwanta na duba ki, wato har yanzu ke budurwa ce ko?" Na rushe da kuka wiwi. Ina fa'din Dan Allah ki yi ha'kuri sanin da na yi ita din mai zafi ce. Sannan ba mai wargi ba ce, y'ay'anta ma shakkarta suke yi ainun. Ta cije ta ce "Kin san Allah sai na ga ni. Ko kuma yanzu na saka Salisu ya dauko mini Gwaggonki tunda ni ba ni da mutunci a wajen ki." Na sake tsananta kukana ina fa'din "Dan Allah Hajiya ki rufa mini asiri. Dama fushi suke yi da ni. Mussaman Babanmu, ki yi hakuri. Kuma ni akan wannan ba laifina ba ne. Na yarda na yi kuskure akan maganar d'akinsa, ba kuma zan sake maimaita wa ba.". Ta saki ajiyar zuciya ta ce "Shikenan na hakura. Amma na baki daga nan zuwa kwanaki uku ki kwaso kayansa ki dawo masa da su nan. Sannan ki kwantar da kai, ki roke shi ya baki iznin zama a d'akin tunda gidan naku babu bishiya ko rumfa. Ba sai na fa'da miki muhimmanci sana'ar ki ba. Komin wadatar miji neman na kai da'di ne da shi. Zaka yi harkokinka kai-tsaye ba sai ka jira an yi maka ba. Bare ke da kika saba yiwa iyayenki hidima a cikin sana'arki". Ina kuka na ce"To. Domin dai na gamsu da maganganunta. Ta sake ce wa "Ki ajiye komai ki rungumi auren ki, kowa da kaddararsa Yabi. Ke taki ma da kyua. Tunda mijin na ki yana son ki da alama kuma yasan me yake yi tunda soyayyar bata rufe masa ido ya sarayar da yancinsa na miji ba. Ki shiga taitayinki. Wadanccan y'anmatan zarata kallon so da fatan ace nasu ne suke binsa da shi. Ki ribaci damarki. Ki rike darajarki tun baki tankwabar da ita ba. Idan a yanzu da yake neman zaman lafiya da ke, kika yarda kuka zauna, to har tsufanku ya dinga kaffa kaffa da ke. Ban ce ba zai bata miki ba, ban ce ba zai kuntata miki ba. Amma dai zaki samu sau'ki, zai kuma din ga shakkar ki botsare masa. Kada ki yarda ki koya masa jure wa fishin ki Yabi". Cikin kuka na sake ce wa "To" Wanda ban san dalilin da ya sanya na kasa daina wa ba. Ta nisa ta sake ce wa "Ban da ma ke din sakarya ce ai cikin hikima zaki gaje can din. Da kin nuna masa nan ne dakinsa ai shike nan. Yanzu kuwa can din da kika raina sai ki ga ya samu wacce zata yarda ta zauna a cikinsa. Sai dai ki ji an kawo masa amarya." Ba k'aramin dukana wannan maganar ta yi ba. Na k'ara sautin kukan da nake yi. Ta ce "Sha sha a haka kamar wayayyiya amma bagidajiya ce. Baki iya komai ba sai kishi. To wai wannan kishin na mene ne tunda ba sonsa kike yi ba? Ya auro uku mana me zai dame ki? Na so bana gidan yau, ya tub'e ya zauna cikin mata na ga yadda zaki yi. Kin san kuma duk masu hankali baza su sake zuwa miki ba. Marasa tunani kuwa sun dinga zuwa, dan su k'ulla alaka da shi". Bata bar gidan ba sai yamma lis, bayan y'an matan sun cire nasu sun tafi. Sai bayan Isha ya dawo. Ya same ni a dakina ina kan abin sallah duk na takura tsabar takaicinsa da yake dafa ni. Ya zauna a kasa kusa da ni. Ya ce "Barka da gida Asiya Toro". Na kasa bu'de baki na ce masa uffan. Domin yadda zuciyata take tafasa sai na ji tamkar na yi ta k'unduma masa ashariya. Yasa dukkan hannunsa ya ru'ko ni yana fa'din "Ba kya gajiya da kuka ne Asiyata?" Ai kuwa ba zato na fara kai masa duka a ko'ina. Ya dinga fa'din"ki yi a hankali kada siraran hannuwan ki su ji ciwo." Na bar dukan domin tabbas hannuwana ne suke mini zafi tunda jikinsa a murd'e yake k'warai da gaske. Kawai sai na fashe da kuka tare da ce wa "Sai Allah ya bi mini hakkina da ka keta a gaban jama'a. Baka da buri irin ace an kai k'arata gaban iyayena. Ka je na barka da Allah ya bi mini kadin zaluncin da kake yi mini. Ban da ka mayar da ni banza ka yi mini hakan? Bayan kwanaki akan idona ka saka aka yi maka girki. Idan tak'amar kicin da kayan abincin naka ne. To kwanukan da tukwanen fa? Ai da sai ka siyo ka kawo mata, ko ta debo na uwarta." Da sauri ya ce "Amma Dada ai ta kashe wannan maganar. Na baki hakuri kuma." Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Ri'ke ha'kurin ka bana so. Tunda ka nuna ba ni da iko a cikin gidan da ake ce wa wai nawa ne, sai ka fa'da mini inda zan dinga zama da jama'ata, tunda ka

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161