Chapter 124
Chapter 124
basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*. *08032773332*. Sosai muke zamana lafiya da taka tsantsan kan abin da zai janyo mana rikici. Na fahimci yajin da na yi, ya sake sawa Tijjani tsoron mu yi fada. Duk da hakan kuma wani loakcin zai fitittke ya yi mini sababin na raina shi, ko akan abu kad'an sai ya tsiri fishi yana fad'in "Tunda Babah ta bani lasisin na dinga yi masa yaji shi ke nan nake yi masa abin da nake so. Dan na ga ba shi da yadda zai yi. Idan yana irin wannan fishin, wani zubin ya bani dariya. Wani lokacin ya bani mamaki. Idan na so sai na rarrashe shi tunda shi haka yake kamar su Hanif wajen son a ritata shi, a tarairaye shi. Wanii lokacin kuwa na share shi, na fi shi fishi. Idan ya lura da hakan sai ya yi maza ya hadiye nasa fishin ya hau lallaba ni. *Shekara daya a gaba* Kwanci tashi tagwaye suka yi shekaru uku. Haka muke gurgura rayuwa yadda ta zo. Wataran fari, wataran baki. Zuwa lokacin sosai harkokokin Bulkachuwa suka sake mike wa. Ni kaina ina siyar da dankalin turawa da su karas da atile a cikin gida. Ba kuma k'aramin alheri nake samu ba. Tunda shine yake siyo mini babu maganar kudin kawowa. Idan na siyar na cire riba na ba shi kudin sai ya sake siyo mini wasu. A hakan har na tara jarina ba tare da na zuba wani kudin ba. Dan haka na ware kudinsa na ba shi, tare da yi masa bayanin yadda kudaden suka haihu dan haka zan cigaba da yi da nawa. Yana bude baki sai ce wa ya yi wadananan din ma naki ne. Kin tuna bashin da kika yi ta ranta mini a lokacin da bani da shi?". Na girgiza lai na ce " A a tsakanina da kai babu bashi Baban 2. Ba ka dauke ni yadda na dauke ba Wallahi." Da azama ya ce "Na gode, na yarda babu bashi. To na ba ki kyauta. Na murmusa na ce "Ka dai biya ni kawai. Shike nan na gode, Allah ya kara budi da lafiya." Ya amsa da "Ameen maman 2." Ya kanne mini ido tare da ce wa "Na kosa a yiwa su twins Gambo fa". Na yi dariya na mike na bar shi dan yanzu sai ya fara tsokana ta akan abubuwan da na yi ta yi masa a baya. Muna cikin haka babu zato sai ga shi ya zo mini da takardar da take nuni na samu gurbin karatu a kwalejin ilimi ta jihar Bauchi. Ban yi murna ba, domin tun filazal na fi son na yi kasuwanci. Na kuma fahimci Ubangiji ya sanya mini nasibi a cikin juya kudi. To akan me zan damu kaina sai na yi karatun da babu garantin zan ci moriyarsa tunda kullum kasar sake lalace wa take yi. Aikin gwamnati siyar da shi ake yi da makuden kudade, sai kana da hanya ma da ka samu a siyar maka d'in. Bai yi fishi ba, ya zauna ya dinga zayyano mini tasirin ilimi a wajen mace ba dan ta yi aiki ta samu kudi ba ne kawai. Ilimin mace da gogewarta na taimaka mata k'warai wajen bawa yara tarbiya da sanin yadda zata yi cudanya da mutane daban daban. Ya sanyaya murya ya ce "Ki daure ki sawa zuciyar ki soyayyar karatun nan Asiya dan sai kin yi shi. Fata na ke yi ko na mutu a ce ke din kina da wata madagora da zaki rik'e mini y'aya'na. Duk duniya ke nake da tabbacin ba zaki gaza da hidimarsu ba. Daure ki bani hadin kai mana". Na dinga kuka domin idan yana irin wannan maganganun gabadaya kidime wa nake yi. Shi kuma baya fasa fada mini lokaci zuwa lokaci, tamkar mai son na yi haddarsu. Tare muka fara makaranta da su Hanif. Domin Nursery da take cikin college din ya snaya su. Da kansa yake kai mu. Sai ya wuce garin da zai je. Bama koma wa gida sai na gama daukar darussa. Komawa ta makaranta sai ta jawo takaddama mai yawa a cikin gidan Marina. Domin a tarihin gidan ni ce na kammala sakandire har na fara ta gaba da ita da kuma aurena. Dada ta dinga sababin ya rungumi BAK'AR TA'ADAR arna masu barin matansu suna cud'anya da mazaje kullum da sunan neman ilimi. Babu kishi babu komai. Alhalin ma'aiki ya ce wanda baya kishin iyalin sa babu shi babu jin kamshin aljanna. Yanzu gabadaya gidan Marina ni na tsole ido. Rufin asirin da muke ciki ya na matukar mintsinin ahalin gidan. Bana damuwa tunda ba a garin nake ba. Wani abin ma har a yi yamididinsa a gama bana ji bare raina ya baci a banza. Kwatsam sai ga Maijidda a gida, wai ta yi yaji. Al'amarin bai yiwa iyayenta dadi ba. Domin ni da ake son ganina ina cikin tasku da jele da sunan bacin rai ba a tab'a ganin na yi hakan ba. Kuma abin mamaki Jabir din ne ya kawota gidan da kansa. Domin ta k'ure hak'urinsa a yadda ya fada. Ya murje idonsa ya juya ya barta. Hakan ya kawo cece kuce da rashin jituwa a tsakanin Baban Tsakiya da na Kasuwa. Duk yadda suka so boye maganar kada mu ji. Sai da maganar ta fantsama domin aure zai k'ara ita kuwa ta ce bai isa ba, sai dai ya zaba ko ita ko amaryar. Ya so su fahimci juna amma ta tada balli domin da ta ga yarinyar da zai aura tunda dalibar kwalejin da yake koyarwa ce. Ai sai ta gigice domin haka take yar tsurut fara kal tamkar dai abokiyar tagwaitakar Yabi ce. Hankalinta ya rubanya tashi domin ta tabbatar ya sota ne a dalilin yadda suke yanayi da ex love dinsa. Ta kuwa ce ba dai ita ba. Shi kuwa ya ce bata da hurumin zaba masa wacce zai yi zaman aure da ita. Watanni biyu basa cikin zaman lafiya, gabadaya ya murde mata fiye da yadda ta murde. A karshe ya kawo ta gida ya ce ta zauna ta huta tukun. Da ya tafi ya kashe wayarsa da dukkan hanyar da za'a same shi. Baban Kasuwa ya dinga fad'a tare da fad'in tozarcin da Jabir ya yi, da shi yake. Kuma ubansa ya kasa tsawatar masa. Saboda yana jin tsoron sa. Rikici ya kaure a tsakaninsu Dada ta kasa shawo kan matsalar domin Baban kasuwa ya dauka da zafi, kuma dama tafi gudun zuciyarsa. Baban marinar da ba'a saka shi ba, shine ya tuntunbesu bayan Dada ta fad'a masa a dunkule ba a bude ba. Abin mamaki kowa ya ce masa babu komai, duk da Dada ta fad'a masa. Shi kuwa sai ya hak'ura ya zuba musu ido. Bai gane kan al'amarin ba sai da ta yi sati biyu. Da kanta ta je ta durkusa tana kuka ta fad'a masa yadda abubuwan suka kasance, sannan ta roki Baban Marina akan ya bawa Jabir hak'uri. Gabadaya ta shiga damuwa da tunani domin dukkan y'aya'nta uku suna can tare da shi.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161