Chapter 54
Chapter 54
abinci ko ban ci ba. To bazan ci ba, idan na mutu ma ai baka da asara." Ya harzuka ya ce "Botsarriyar yarinya kawai! Ana taro ki, kina sake nausawa, to kar ki ci din. Allah ne shaidar na yi bakin kokarina". Ai kuwa na zunduma ihu tamkar gaske. Na katse wayar. Ya dinga kira amma naki d'agawa. Ya kira ya kai sau biyar ina gani ban dauka ba. Daga can sai ga text message. Kamar bazan bu'de, sai kuma na bu'de din. "Asiya Toro ki ji tausayina! Ki daina mini irin haka. Kinsan yadda zuciyata take bugawa a dalilin kukanki da kin daukar kirana? Ki yi ha'kuri bazan sake yin tafiya na barki hakan ba. Kuma indai na iso lafiya da kaina zan dafa miki komai kike so". Jikina ya yi sanyi. Tsawon lokaci na kasa gane yanayina, tausayi ya bani ko kuwa mene ne? Na bu'de what'sapp na ga anan ma ya turo mini sakonni. Na kasa bu'de wa domin bana son na sake jin fiye da kasalar da nake ciki. Da yamma lis sai ga shi ya dawo. Na bu'de masa kofa ya shigo dukkan hannuwansa ri'ke da ledoji. Ban yi yun'kurin kar'ba ba. Da walwala ya ce "Asiya Toro babu oyoyo sai kallo mai kama da harara?" Na gintse fuska na yi gaba, na bar shi. Ya biyo ni falon dana shiga. Ya ajiye mini a gabana. Ya fita da sauri sai gashi ya kinkimo kwanon satellite ya ajiye a tsakar gidan ina hango shi ta windo. Da'di ya yi matu'kar kama ni. Domin na kagu na fara kallo. Ya sake fita ya dawo rungume da kwali a kirjinsa da na yi zaton receiver ce. Dayan hannun kuma leda ne. Na yi maza na gyara zamana na yi kamar harkokina kawai nake yi. Ya shigo da sallama na amsa a hankali. Ina mamakin yadda Tijjani yake da yawan sallamah. Ya zauna a kasa a gabana tamkar uwargida da yaronta. Amma girmansa da cikar haibarsa ya sanya bai yi kama da yaron gida a gabana ba. Tunda ni din yar mitsil ce. Yanayinsa yafi kama da na wadda yake neman a amince masa, a gamsu da lamarinsa. Da barin jiki ya tashi ya dauko roba a kicin, da yar wuka hadi da bowl karami irin plastic din nan mai k'wari. Ya debo ruwa a cikin robar. Ya shigo, ya bu'de ledar da tafi kusa da ni. Apple ya ciro guda biyu ya wanke a cikin ruwan, ya saka su a bowl din tare da yar wuk'ar ya miko mini ya ce "Fara da wannan Asiya. Ki rage yunwa kafin na gama miki abincin. Maghariba ta kawo kai sai na dawo daga sallah zan d'ora miki. Me kike son ci?" Ban kar'ba ba, ban kuma tanka ba. Ya ce "Ki kar'ba mana, me yasa kike yi mini haka ne?" Yadda ya yi maganar a dan tunzure, bansan ya aka yi ba, na tsinci kaina da mika hannu na kar'ba. Ya sassauta ya ce "ko na yanka miki?" Ban amsa ba, illah hannu da na saka a cikin robar na wanke. Sannan na dauki Apple din na fara gutsura da bakina. Ya zuba mini ido yana kallon yadda nake cinsa cikin yanga tamkar me cin magani. Ya murmusa ya ce "Yabi yanga". Karon farko da kunne ya ji ya kira ki da Yabi. Na dauke kai na ce "Tsabar adawa da kake yi da hajjina shine ba zaka ce Yabi ba. Yau kuma da bakinka ya subuce ka fa'da din sai da ka ha'da da bita da k'ullin yanga?" Ya fashe da dariya sosai ya ce "Kamar kinsan subutul kalam na yi. Tun fil'azal nafi son ce miki Asiya domin sunan na matu'kar burge ni. Yanzu kuma tunda Jabir haka yake ce miki, na sake kauracewa sunan. Bana adawa da hajjinki, amma fa bazan kira ki da Yabi ba. Ina fatan na samu damar da zan kai ki sauke faralli Asiya. Sai ki zama Hajiya ta sosai tunda hakan shine burinki." Na dauke kai, na gutsuri apple na ce "Da wanne ku'din zaka kai ni Makkah? Ai indai ina tare da kai babu wani alherin da zai same ni, bare alheri irin na zuwa Saudiyyah". Tsawon lokaci ban ji ya ce mini komai ba. Na juyo da kallona gare shi. Na ga jikinsa ya mutu. Duk kuzarin da ya zo da shi ya gudu. Gaba'daya ya zama tamkar an kwara masa ruwan sanyi. Ni kaina sai na ji jikina y mutu lakwas. Tsawon lokaci muna haka tamkar masu zaman makoki. Da k'yar ya yun'kura ya mike ya ce "Na tafi masallaci". Na bishi da ido, ina jin abin da nake ji a kansa na sake mamaya ta. Na kasa gane tausayi yake bani ko kuwa menene? Nasan dai ko ka'dan babu digon sonsa a raina. Da zai dawo ya shigo da k'aramin gas (3kg). Daga bakin kofar falon ya tsaya bayan ya daga labule ya ce "Me zaki ci Asiya?" A hankali na ce "Ni na koshi, akwai macaronin nan a kicin". Bai ce komai ba. Ya saki labulen. Da kansa ya zubo abincin. Sai dai wannan karon a kujerar nesa da ni ya zauna. Bayan ya dauko ruwa da lemun coke. Na kalle shi tamkar wani mai wadata ya hakince ya saka ruwa da lemu a gaba. Ya kammala, ya dube ni bayan ya ha'diye fishins ya ce "Ki dinga jin tsoron Allah Asiya. Yanzu abin da kika yi ya yi daidai kenan? Ki saka na k'ira Ummi na balbale ta da sababin bata yi mini aikin da na saka ta da kyau ba. Ashe ma kin ci kin cika cikin ki, tsabar fitina, da son ki tayar mini da hankali shine ya sanya kike kuka da fa'din abincin bai yi da'di ba?". Na zum'bura baki, na kasa cewa komai. Ya yi k'wafa, bai ce komai ba. Ya sauko ya zauna kan kafet din ya bu'de reciver ya ce "Gashi na siyo miki." Ganin ban amsa ba ya sanya ya cigaba da bude ledojin da ya shigo da su. Kusan duk kayan abinci ne dangisu shinkafa, taliya da macaroni. Sai katon din indomie da kayan shayi. Sai kuma leda mai dauke da sabulun wanki da su omo, makilin da maganin sauro na kunnawa. A hankali ya ce "Ku'din da abokaina suka ha'da mini ne na siyo miki settlite da gas, shine na karo kayan abinci dan mu dan tura sosai kafin su kare." Na juyar da fuskata na ce"Madallah". Ya yi sororo murya a dakushe ya ce "Ba zan yi wani abu da niyyar na sanya ki farin- ciki ki nuna mini kin ji da'di ba Asiya?" Cike da iyashege na fara wage baki, dukkan hakorana a waje, ga idona na zazzarosu tamkar mai motsi a k'wak'walwa. Ina yin hakan, ina cewa "Na yi murna Tijjani. Ka burge ni Tijjani, na ji da'di Tijjani". Sannan na dawo yanayina na zuba masa ido na ce "shike nan?". *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161