Skip to content

Chapter 128

Chapter 128

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

nutsuwar da ta dace da mu ba. Na dauka bandakin da na samar miki a cikin daki zai sa ki yi farincikin ki gane komai kike so sannu a hankali zan yi miki shi " Ido cikin ido na kalle shi duk da bai sake ni ba, na ce "Duk wadananan abubuwan da ka lissafa hakkina ne da ya zama wajibi ka yi mini su, ba wai taimakona ka yi ba. Idan kuma yinsu alfarma ce to ka daina bana so. Daki mai bandaki kuma bana sonsa, nafi son wanccan gidan da yake fallen falle mai bandaki a tsakar gida, domin nafi samun gamsuwa da mutuntawa a cikin sa. Ya sake ni yana fad'in "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Asiya sai yaushe mata zaku gane hidimar da take kan namiji ba zata bar shi kullum ya mu'amalance ku yadda kuke so ba? Da din da kike marari ba ni da abin yi ne, ina rayuwa ne a takure saboda bana iya samar miki abubuwan da suka dace da ke. Yanzu kuma da na samu hanyar daukan nuyinmu sai ya zama tashin hankalin? Shi kenan sai ya zama laifin da zaki janye soyayyar da kike yi mini?" Na ce ",Eh dama ai ba son ka nake yi ba. Kirki da ririta ni da kake yi ne ya janyo maka soyayyata. Amma tunda ka janye su, nima na fasa son naka sai ya ya kuma? Har kana kumfar bakin ka kai ni Kano ka mini siyayya to ga kayan can bana so. Tunda har zaka yi waya a cikin dakin da kasan ina ciki kana fad'in baka tsorona, zaka bayar da mamaki akan lamarina. To ina ce sai na damu da kai ko kuma idan na zauna da kai? Sannan zaka tozarta ta ni ta hanyar nunawa duniya ni din ba komai ba ce a wajen ka. Ni kuwa me zaka yi mini na ga farin ka Tijjani?" Ya sake ni a matukar sanyaye. Domin ya gane da dukkan zuciyata na shirya wa ko wacce irin fitina. Ya zauna kawai ya jingina da bango sama da awa bai iya ce wa komai ba. Sallah ta fitar da shi. Ya dawo ya zauna a inda ya tashi, gabadaya ya zube tamkar mai amai da gudawa. A sanyaye ya kalle ni ya ce "Ba ni shayi na sha. Yau ko ruwa ban kai bakina ba. Ban yi masa musu ba na hado na kawo masa. Yaran namu su kansu sai suka zama babu walwala a dalilin sun ganmu a birkice. Yana dawowa daga sallar isha ya rufe gida. Da yake da yaran ya je. Suna dawowa Hamim ya yi barci. Hanif ne ya dan jima yana kallon cartoon kafin shi ma barcin ya sure shi bai sani ba. Har lokacin muna zaune jigum jigum tamkar masu zaman makoki. Ya numfasa ya ce "Asiya mu fahimci juna mana. Ko motsi ban yi ba. Bare na tanka masa. Ya ce "Na rasa gane halin da nake ciki. Gabadaya jina nake yi a juye. Amma mu fahimci juna. Kin ga Babah ta yi fishi da mu mai tsanani. Mu shirya kanmu, gobe sai mu je mu bata hak'uri." Na ce "To". Ya ce "Ban gane to ba Asiya". "Allah wahidun! Me zan ce maka to? Na ce a,a?" Ya kalle ni kawai. Ya mik'e ya sure ni tamkar yar tsana ya yi dakinsa da ni. Yana fad'in "Mu je kan katifa na rarrashe ki, domin na gane rarrashi akan katifa yafi na kan gado ratsa jiki". Na dinga mutsu mutsu tare da son na kwace amma ina. Ya mini kamun kazar kuku. Duk fizge fizgen da nake yi bai kula ba. Sai da ya dangana ni da katifar. Ya bini ya mini rumfa da jikinsa. Karshe ma ya sakar mini nauyinsa ta hanyar danne ni. Na daure na ki na nuna na kosa. Ya bini da kisses da sauran al-amura masu nauyi. Tun ina dauriyar kin karbar rarrashin nasa har na kasa jure wa na fara karba ta hanyar sakar masa jiki da daina ture shi. Sai da ya gama jagwalgwala ni, sannan ya kankance murya ya ce "Da gaske ba kya sona Asiyaty?" Na dauke kai ina jin kunya na kama ni. Domin ni kad'ai nasan yadda nake jin sa a zuciyata. Kawai wulakancinsa ne yake neman kwantar da ni. Sai da yasan yadda ya yi muka shirya, ya zangwanyar da fishin da na yi. Bayan ya jaddada mini, ba abin da yake so nan duniya sama da ni. Cikin saa'a bai mini zancen mutuwa ba. Bamu yi barci ba, a wannan dare, domin ko da muka samu nutsuwa. Maganganu muka cigaba da tattauna wa. Haka ya dinga bani hak'uri tare da rokon na daina yi masa irin wannan fishin mai tsanani. Na daina damun kaina ta hanyar kaurace wa abinci da kuma walwala. Sai da muka karya, muka shirya sannan muka dauki hanyar Bulkachuwa. Da k'yar Babah ta sauraremu. Mun shafe fiye da awa ban da sallamarmu bata sake kallon inda muke ba. Harkokokin ta take yi ita da su Hanif. Su kawai ta bawa ruwa da abinci, mu kuwa ko kallon inda muke bata sake yi ba. Ni na fara yin kundubalar bin ta daki. Yayin da ya biyo bayana, amma ya toge a bakin k'ofar tabbacin jiya bai ji da dad'i a hannunta ba. Na zauna a gefenta. Na lankwasa harshe na ce ",Dan Allah Babah ki yafe mana. Idan ba ki huce ba, ba zamu ga haske ba. Kuma tun jiyan ma mun sasanta kanmu." Sai lokacin ta bude baki ta ce "To ni kuma ina ruwana da al'amarinku? Ni da kika ganni bana shiga kasafin da babu mutunci a cikinsa. A gabana ki zagi mijin ki Yabi?" A sanyaye na ce "Ban zage shi ba Babah". Ta ce "Kalmar da kika fada masa ai zagi ne Na yi shiru. Ta dinga yi mini fad'a tamkar zata doke ni. Ganin ta tsananta ya sanya na ce ",Babah Wallahi ni kad'ai nasan kuttun da yake cusa mini. Yanzu ba dama ya dawo ya zauna mu yi hira, sai dai ya yi da wayarsa, na sani kuma da y'anmata yake yin hirar ni ya bar ni gaho. A Kano kuwa da kunnena na ji yana zancen zai tura gidansu". Ta ce "Akan me ba zai yi aure ba? Akan ki zata zauna, me ce a cikin kishiya ne da kika tsananta wa kanki k'in ta. Allah ya ce su yi mataye sama da d'aya idan zasu iya adalci. An janye ayar ne, ko kuwa rushe ta zaki yi, ki kafirta?" Tana rufe baki na rushe da kuka ina fad'in "Kin bi bayansa ya yi mini kishiya ko Babah?" Ta janyo mafici ta shiga kwada mini tana fad'in "Na bi bayan nasa sakarya. To hakan da kike yi masa ne zai hana shi k'ara auren. Tun yanzu kin tattara kin bar shi, idan ta zo ba sai ta karbe shi gabad'aya ba." Cikin kuka sosai na ce "Babah na rantse da Nasiba yake soyayya. Ya auro kowa amma ban da ita. Ni Wallahi bazan yi kishi da ita ba. Mutuwa zan yi, idan kuwa ban mutu ba, daga ranar da ya aure ta. Billahi a ranar na haramta gare shi!" Na fada cikin matsanancin kuka.

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161