Chapter 47
Chapter 47
ni. Na ce zuciyar waye din zata tsumu?" Ya make kafa'da ya ce ta "Asiya Toro". Na yi kwafa na ce "Ai na gane zuciyarka babu alheri ne shi yasa kake k'yashin ce mini Yabi. Da'din abin ma dubun ka suna fa'da mini cikin girma da arziki". Ya ce"Nan da lokaci ka'dan komai zai zama tarihi. Kin ga dai na nemi arzikin ki, ban kuma mayar miki da martanin bakaken maganganun da kika yi ta yab'a mini ba. Ina sake ro'kon ki idan abokina ya kira ki, ki taimake ni kada ki bayar da ni." Ban amsa ba. Ya sake cewa dan Allah Asiya Toro". Cikin fishi na ce "Na ji". Da'di ya kama shi ya dinga fa'din "Na gode sosai. Ina fatan na ga ranar da zaki fahimci irin tarin alkhairorin da suke zuciyata mussaman akan lamarin ki". A hanzarce na ce "Ai kuwa dai ba zaka ga ranar ba". Ya girgiza kai tare da ce wa "Babu damuwa time will tell". Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ina son na tambaye ki, zaki iya zama a wanccan daya bangaren na Dada?" Maimakon na yi masa magana da baki, ai sai kawai na d'ora hannu aka na fashe da wani irin kuka na tashin hankali. Murya na rawa na ce "wato dai a cikin masifar gidan nan zan tabbata? Idan kuwa har a cikin gidan nan ake nufin na zauna da sunan zaman aure Allah ya dauki raina kafin hakan ya tabbata. Na shiga uku ni Yabi". Ya rikice ya hau fa'din yi shirun ki dama na fa'da mata wajen ya miki local da yawa, sannan baki samu sauyin muhalli ba. Yau din nan duk inda gida yake zan nemo kafin dare. Da ku'di a hannuna. Yi hakuri ki daina irin wannan kukan. Kin ga yadda kika koma kuwa Asiya?" Da k'yar ya lallaba ni, na yi shiru. Ya zura hannunsa a aljihu ya ciro cakulet manya masu da'di da tsada k'waya biyu ya mik'o mini. Bansan ya aka yi ba na fashe da dariya ga kuma hawayen ba'kin ciki na ziraro mini. Da yake d'an duniya ne sai kawai shima ya fashe da dariyar yana cewa "Ni nasan Ubangiji zai cusa miki soyayyata dan yasan yadda ya gina ki a tawa zuciyar. " Da k'yar na samu dariyar ta tsaya. Da hawaye a idona na ce "me zan yi da wannan abar?" Ya zuba mini ido yana wani lumshe su ya ce "Wai fa dan kada na zo hannu na dukan cinya ya sanya na taho miki da su" Na rasa me zance masa tsabar takaicinsa da ya d'ada makure ni. Na ce "To ajiye idan ka ga Yarinya k'arama ka bata amma ba ni ba". Ya waske ya ce "Asiya Toro maraina ka'dan fa barawo ne. Kowa ba iya karfinsa zai yi kyauta ba? Kin san wahalar da na sha kafin na samo miki wannan cakulet din a garin nan? Saboda nasan kina son ta ne. Amma ban burge ki ba? Idan kin yi hakuri wataran katon zan siyo na ajiye miki." Da sauri na ce "da dai ace ba hannun jinjirai ne da kai ba tsabar rowa." Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Ni ne mai hannun jarirai? Lallai kuwa zan baki mamaki Asiya Toro local government. Bauchi state of Nigeria". Ko kula shi ban yi ba na wuce shi na tafi na bar shi a tsaye. Tsabar takaicinsa da ya sake kular da ni. Ya d'aga murya ya ce "Sai gobe zan dawo, ko da anjima ma na dawo?" Da kansa ya bawa kansa amsa da ce wa "To zan dawo da daddaren ran ki ya da'de." Har na isa k'ofarmu mamakin Bulkachuwa kawai nake yi. Ban da dai ya riga ya same ni a araha ya rasa me zai kawo mini sai cakulet k'waya biyu. Shi ko kunya bai ji ba? Amma da na tuna halin rowarsa sai kawai na janye mamakinsa. Na shiga tambayar kaina wanne irin zama zamu yi ne da shi? Na tabbatar sassaucin da ya yi dan baya son na yarfa shi ne. Amma da tuni ya baje mini kalolin rashin mutuncinsa. Na zauna na fara kokarin cigaba da k'ullin sigan. Zuciyata ta shiga hakaito mini kayan jikinsa. Shadda ce a jikin sa kalar ganye wato kore sosai. Ya d'ora hular sanyi mai tambarin kungiyar Manchester United. Na sani kuma d'an ya boye wa Baba curarriyar sumarsa ne tunda zafi ake yi ba sanyi ba. Daga ni tun farar safiya ya sanya kayan a hakan kuma shi ya k'ure malejin kwalliya ne. Na ja tsaki tare da ce wa "Idona ya saba ganin samari ma'abota wanka da gayu. Irinsu Yaya J da Nuru Tanim. Ta ya ya Bulkachuwa zai burge ni?." Gwaggo ta shigo ta ce "me ya faru da kika je?" Na yi kasa da kai na ce "Ba Dada ba ce ashe". Ta ce "To waye?" Na bata rai duk da kan nawa yana kasa na ce "Tijjani ne". Daga hakan bata kara ce wa komai ba ta dauki abin da zata dauka ta fice tsakar gida. Washa gari da azahar ina kwance a tsakar daki sai ga Nazira ta zo. Karon farko da ta zo gida tunda aka yi mata aure. Duk rud'anin da nake ciki sai da na tashi da azama na rungume ta. Muka haye k'aramin gadon Gwaggo da muke kwana a kansa ni da ita tun fil'azal. Da murmushi a fukskata na ce "Yau Adda Nazira ce a gidanmu?" Ta d'aka mini duka tare da cewa"oh har kin cire ni a cikinsa, to kema kwana nawa ya rage miki mu yi kunnen doki?" Na bata fuska sosai. Ta ce "daga wajen Dada nake suna can, suna artabu da Yaya Bulkachuwa akan inda zaku zauna. Wai akan me zai je ya kama haya tamkar ba shi da kowa a Toro? Shi kuma ya kafe ba zai zauna a cikin gidan nan ba.". Na bata rai na ce "Ai Wallahi na fa'da masa indai ya yarda da tsarinsu to kuwa sai dai a tsine mini dan bazan zauna a gidan nan ba'kin ciki ya karasa ni tun ajalina bai zo ba" Adda Nazira ta ce "Haba ashe tirjiya ya samu daga gare ki, kin ga yadda ya fitittike akan ba zai zauna a wajen ba? Dada har da kukanta wai sai da ya bari su Baban Tsakiya sun gama gyara masa wajen sannan ya ce zai fita ya kama haya tamkar wanda bashi da galihu a Toro? Shi kuma kinsan shi ya ce "Salisu da yake hayar rashin galihu ne ke nan? Ashe ashe Gimbiya Yabi ce ta saka ya rikice ya turje. Ya kama miki gida mai kyau a bayan sakatariya. Ba ki ga gidan ba. Yanzu muka dawo a mashin dinsa ya goye ni muka je ya nuna mini gidan. Ni Wlh har na ji na daina k'insa. Kin ga rawar jikin da yake yi. Sai fa'di yake ya kika ga wajen Nazira? Nasan idan ya burge ki to zai burge kanwar ta ki ma. Gaskiya Yabi ke d'in mai sa'a ce. Gaba'daya kin rikita namiji irin Yaya Bulkachuwa. Murna nake yi, da dukkan zuciyata nake jin addu'armu ta karbu. Da ikon Ubangiji sai kowa ya yi mamakin alherin da zai biyo bayan wannan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161