Skip to content

Chapter 125

Chapter 125

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

Mai shan nono kawai ya bar mata. Bata tab'a zaton zai yi mata hakan ba. Duk kokarin Baban Marina ya amsa samun Jabir. Washagari ya tisa ta a gaba ya nufi Kaduna da ita. A ransa ya tabbatar dan tana son komawa dakinta ne. Ba dan hakan ba da bai isa ya yi irin wannan ikon ba. Jabir na ganin sa ya ware fuska ya marce shi da girmamawa. Baban ya dinga yi masa fada tare da tabbatar masa ya yi tsaurin ido. Cikin jin nauyi ya ce "Ka yi hak'uri Baba! Ta kai ni bango ne da yawa. Ni fa dama hak'uri nake yi domin ba hakan nake so ba, amma tunda kaddara da rabo ya ba ni ita, ban zalunce ta ba. Ga ta nan ta fada maka inda na kuskure domin nasan iyakar adalci ina yi mata. Aure kuwa bata isa hana ni yi ba, bata kuma da hurumin zaba mini wacce zan aura domin ni din ba makaho ba ba ne, bare ta ce zata zaba mini wacce zan aura". Baba dai ya yi masa fada tare ce wa "Ka dauke ta ka kai mana ita, ka yi tafiyar ka ai rainamu ka yi Jabiru. Duk cikinmu ka rasa wanda zai maka maganin matsalar sai ta hanyar mayar mana da ita? Ko a lahira wani na cin arzkin wani. Kada ka sake irin haka. Kishi kuma ai dole ta yi, ka rarrashe ta, ka kwantar mata da hankali ba wai ka ankara ta ba." Ya juya ga Maijidda take kuka sosai ya ce "Ke kuma ba ruwan ki da auren sa, matukar yana yi miki adalci, kawai ki yi hakuri ki yi addu'a. Ai kishiya yar uwa ce, ina ruwan ki da ita. Ban da ma sakarci me ya ka ki yin fitina akan wacce ma bata zo hannunsa ba? Kina ahalin gidan Marina ki ce ba kya son kishiya? To ko da kika ga gyatumar ki ita kad'ai ai mu kina ganin kofofinmu mata ne da yawa ba kuma wacce ta kori wata, ko ta hana ta samun arzikin ta." A ranar ya juyo ya dawo. Ba jimawa kuwa Jabir ya yi aurensa. Hakan ba k'aramin tasgado ya janyo a taskanin Baban kasuwa da na Tsakiya ba. Da k'yar aka samu suka fara gaisawa. Kunyar mutane da yadda aka san kansu a hade yake ya sanya suke gaisawa. Da kuma yadda Dada ta yi kuka sosai akan gabar da suke yi da juna. A zahiri sun shirya amma kasan zuciyoyi babu dad'i. Ba yadda zasu yi ne kowa yana ganin shine akan dai dai. Baban Marina dai bai ce kala ba. Domin yanzu da abubuwa suka fara warware masa a dalilin mafi yawa y'aya'nsa muna cikin rufin asiri. Muna had'a abin da za'a ci a k'ofarmu. Tijjani kuwa ya dauke masa cefanen kayan miya da kudin k'ananun bukatu. Hakan ya sake janyo masa bakin jinin da babu yadda za'a yi sai zunde a bayan ido. *** A hakan na cinye shekara d'aya da fara karatun. Na fara nisa a cikin ta biyu. Tun bai shiga jikina ba, har na sanya shi a raina na mayar da hankali, hakan ya faranta ran Tijjani tunda ban sami carry over a shekarar farko ba. A hankali sai nake ganin Tijjani na d'an sauyawa. Sauyin bai shafi mu'amalata da shi ba. Amma yana yawan zuwa Toro. Kusan kullum sai ya je ko da ba zai je Jos ba. Ina ta jin rade radin yadda yanzu yake zama ya yi hira da Nasiba da har yanzu bata yi aure ba. Sai ma kasuwanci da take yi sosai. Kayan gwanjo take siyowa a Jos masu kyau. Har ce mini aka yi yana karbo mata sakon kayan. Tun ina daure wa ina dauke kai daga abubuwan da nake ji har na fara sike wa. A dalilin kullum dare sai ya fita k'ofar gida ya shafe lokaci mai yawa yana waya. Haka nan kaffa kaffa yake da wayarsa abin da baya yi a da. Da na yi masa magana sai ya balbale ni da fad'an na saka masa ido ne. Ban da hakan me yake yi mini? Dan ya yi wayar da bata shafe ni ba a waje shine laifi? Na kasa bude baki na ce komai domin ba ni da hujja. A hankali muka fara samun tazara a tsakaninmu. Na sani bai canja daga kawo mini abubuwan abincin ko na bukata ba. Bai canja a hidimar makaranta ta ko hidimar y'aya'nsa ba. Sannan bai canja mini a mu'amalarmu ta auratayya ba. Har yau din nan a cikin mararina ya ke. Duk da ni din ma kullum a cikin gyara kaina nake da ingantattun kayan Surayya da basu da illah ga lafiya. Sannan ina amfani da kayan g.h.t na FASEELAT. Amma yawan wayar da yake yi da sintirin zuwa Toro, da sabunta mu'amalarsa da Nasiba da nake ta jin rade radinta, tana matukar ci mini tuwo a k'warya. Na rasa wa zan fad'awa ya fahimce ni. Domin da na fadawa Gwaggo ce wa ta yi "Ina ruwan ki da jita jita? Sannan ai bai zai yi aure bai fada ba. Ki rage kishi mussaman kan abin da baki gani ba, zato ne da shati fadi kawai. Haka na hak'ura na cigaba da zuba ido tare da hak'uri. Amma sai nake ta d'ad'are wa da shi. Ko a shimfida bana wani katabus shi zai yi kidansa da rawar sa. Wani lokacin ya tambayi dalilin sauyin nawa cikin kwanciyar hankali. Bana iya ce masa komai sai dai na ce "Ban canja ba, babu komai". Wani lokacin ya ce "Allah ya sauwake. Wani lokacin ya yi tsuka ya juya mini baya tare da fad'in "Zan yi maganin wulakanta ni da kike haka siddan Asiya." Gabadaya mun koma muna ganin laifin junanmu a dalilin kowa bai gamsu da kokarin d'an-uwansa ba. A haka na kammala aji biyu. Twins sun yi wayo sosai tunda sun shiga shekaru biyar. Wani irin wayo da fikira a cikinsu tamkar wanda suke siyo dabara a kasuwa. Gabadaya sun juye ubansu sak. Ga shi suna girma suna sake zama iri d'aya. Ni da kaina ina gane su ne ta halayyarsu. Domin har yau din nan Hanif mai hakuri ne, magana bata dame shi ba. Sabanin Hamim d'an hayaniya kuma mafadaci irina. Har yanzu bai bar kuka ba. Sau biyu ina yin bari. A yanzu haka ina zuwa ganin likita a dalilin hakan. Na karshen nan da na yi Bulkachuwa ce mini ya yi "Ina sane nake bararwa tunda na saka masifa a raina. Ya rasa me yake mini da nake gana masa azaba haka. Kallon sa na yi kawai. Ba tare da na tanka masa ba. Domin na riga da na saka a raina ce wa hakurin da aka yi ta jaddada mini na yi a lokacin aurena. Yanzu ne zan fara shi. Dan haka na rungumi addu'a, y'aya'na da karatuna hadi da sana'ata. Na tattara shi na zuba masa ido yana yin almuransa yadda yake so. Muna cikin wannan zaman na fallasa tafi yabon yawa. Kamfani suka sake biyansa kudin hayar filinsa tunda shekaru uku ta cika. A wannan karon har da kari akan wanccan. Duk yadda muke jin haushin juna sai da ya zauna ya mini bayanin komai. Ya kwashe mu

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161