Chapter 19
Chapter 19
yanzu ma idan na tashi zan je na sami Yaya Sani na tabbatar masa babu maganar aure, mun gama magana da Iliya, Maijidda zai aura. Domin ba zan yadda ya dauko mini majuniniyar yarinyar nan ta zo ta tarwatsa mini zuri'a ba". Daidai lokacin na yi sallama na gaida Dada sannan na gaishe su a jamma'u. Babar Bulkachuwa ce ta amsa cikin karfin hali tana danne bacin ran da ya ke kutso mata. Nima na yi jarumtar cewa "Ashe kin zo Babah?" Ta ce " Na zo dazun nan kin san sammakon zuwa nake yi saboda motar Jos muke shigowa. Na yi yake na ce "Sannu da zuwa". Na mike da nufin tafiya sai kuwa Baban Tsakiya ya ce "Dawo ki zauna. Na zauna ina kallonsa k'ir domin ya riga ya wanke mini a zuciyata. Ya kausasa murya ya ce "ki hanzarta turo wanda kuka shirya domin kuwa watan jibi da saba'a zaku bar gidan nan". Cikin son nuna masa iyaka na ce "To ai Jabir naka muka daidaita da shi, wannan satin zai iso garin, wajenka zan turo shi, ko wajen Baban Kasuwa?" Ya zabura ya mini dakuwa ya ce "Marar kunya, marar mutunci ki zagi dan-uwana, ki mini tsaki a gabana ki yi zaton kuma zaki zama surukuta, ko dai bayan sharholiyar da kike yi har shayeshaye kike had'a wa da shi? To saurara ki ji! Jabir ba zai auri wanda zata zagi ubansa ba." Babu fargaba na ce "Na karbi wannan hukuncin da hannu biyu Baba, ban kuma saka ka cikin masu son rai ba, domin na yi laifin da na cancancin hakan. Alfarma d'aya nake ro'ko a wajenku tunda ni ce bani da tarbiya, to ku musanya wa Yaya Jabir ni da Nazira domin dukkanku nan ba wanda zai zargeta da rashin tarbiya ko sharholiyar da ni nake yi". Nan da nan Baban kasuwa ya ce "Anki a bashi ita din dan uwarki, makira, algunguma, Maijidda ce matarsa har a kiyama kuwa". Ga mamakina sai na mike na tsinci kaina da cewa "Gaskiya Baban Marina ne ba a so, shi kuma har yana kora ta saboda ku. Ba komai Ubangiji ya sanya alheri". Har na fice ba wanda ya iya bu'de baki ya ce mini kala tsabar kad'uwar da suka yi da furucina. Baban Tsakiya ne cikin fishi ya ce "Ba shakka dangin uwar yarinyar nan akwai majununai". Na so na tsaya na ce "ko wanne d'a yafi gadon dangin ubansa, dan ya gane sune majununai ba mutanan Kangire ba. Sai dai kuma duk iyashegena ai wata fuskar tafi gaban mari, kannen ubana ne, ta ko wacce fuska idan na yi musayar yawu da su ni ce bani da gaskiya. Sai kawai na had'iye. Ina fitowa na yi kicibus da Bulkachuwa yana tsaye da buta a hannunsa, tabbacin daga bayi ya fito. Na tabbatar kuma ya ji komai har maganganun da aka yi a kansa da Nasiba. Domin gaba'daya manyan idanuwansa sun kad'a, sun yi jajur. Na wuce shi ban sake kallonsa ba, kallonsa ka'dai ya sanya na ji tamkar na yi amai tsabar yadda na washe shi. Wannan abin da na yi ya sake ki'dima wadannan bayin Allah domin dukkansu ba wanda maganar bata shige shi ba. A ranar na koma gidan Yaya Salisu ban san wainar da ake toyawa a gidan Marina ba. Zama nake yi irin na taka tsantsan a gidan, ba dan komai ba sai togaciyar da aka yi ta yi mini a gida. Da safe zan yi wanke wanke da shara, na yiwa dansu wanka shi kenan sai na shige daki. Idan ta gama abinci zata mini zubin auki. Yadda nake gudun bata mata, hakan ita ma take kaffa kaffa dan kada na ga beken ta, ko idan na koma gida na bada ba'kin labari a kanta. Ranar da na yi kwanaki hudu sai ga Nazira da Iklima. Muka yi hira, sun kusa tafiya Nazira ta ce da Iklima ta fita ta jira ta a waje. Ba musu Iki ta fita. Ta sassauta murya tabbacin bata son a ji maganar ta ce "Kinsan me yake faruwa kuwa a gida?" Na girgiza kai ina fa'din a ina zan sani Adda Nazi?" Ta sake yin kasa da murya ta ce "wata yarinya ce ta yi cikin shege har ta kusa haihuwa fa, to ana ta shari'a, da ta lissafo wadanda suke mua'amalantar ta har da Yaya Bulkachuwa yanzu haka kullum sai sun je kotu". Zuciyata ta harba da tsananin gaske, na ce "Tijjani gaskiya baya kyauta mana, gaba'daya sai ya gama ruguza darajar gidanmu alhalin shi ba dan gidan ba ne". Nazira ta ce "Hmm abin sai ha'kuri ba ki ga yadda ya zama ba, ya kuma kafe akan ciki ba nasa ba ne ba zai kar'ba ba. Babah ta Bulkachuwa ita ma ta zama abin tausayi sosai tsabar ba'kin ciki." Hawaye ya balle mini wata irin damuwa ta shige ni, kishin zumunta ya murde ni, ko yaya ba zaka so ganin jininka a cikin tozarci ba. Mun jima a hakan kowa da k'wallarsa ta ce "Jiya Malam Yunus Econs ya aiko a bashi izinin neman aurena kinsan tunda matarsa ta rasu a wajen haihuwa har yanzu bai sake wani auren ba, ga yaron nan tuni ya shekara biyu." Na ru'ko ta ina fa'din "Kai na yi murna sosai Allah ya tabbatar da alheri mutumin kirki ne, na amince Adda Nazi ta so shi ta bashi dama, Allah sanya albarka a tafiyar". Muka fito ina musu rakiya tana ce wa "Abdul sau uku yana zuwa amma Baba bai bari an fa'da masa inda kike ba." *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. Na ce zai bari ne, domin ko Yaya Jabir ne autan maza na bar shi Nazira". Ta ru'ko hannuna ta ce "Madallah da zuciyar Yabin Marina! Ni nasan zuciyarta ba zata cigaba da son wanda zata yi kuka a hannun ahalinsa ba, ba zata so wanda ubansa yake k'yamarmu ba, in sha Allah sai kin auri wanda ya fishi komai, aurensa da Maijidda kuma bama adawa. Sai kuma kuka ya goce mata, nima hawaye ya sake zubo mini, domin idan na ce bana sonsa ko abin bai dame ni ba na yi k'arya. Amma zan nuna wa su Baban Tsakiya ni din yar halak ce ina kishin ubana, ina kuma kishin kaina. Babban rufin asirin da Allah ya yi mini shine dama ina da Abdulrashid. Su biyun duk ina sonsu amma nafi son Yaya J. Yafi daukar hankalina matu'ka da gaske sai dai zan iya rayuwa da Abdul ba tare da na takura ba. Sai da muka yi kukanmu son ranmu sannan muka je gidan Yaya Salamatu, muka bata labarin halin da ake ciki. A sanyaye ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161