Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

dawo gidanmu a takure nake jin kaina, domin ban ji da'din yadda Nazira bata sake mini kamar yadda nake so ba. Na iso gida na tarar da Yaya J gurfane a gaban Baban Tsakiya kansa a k'asa da alamun kuka yake yana fa'din yayi masa alfarma ya bar shi ya yi abin da Allah ya hallata masa. Ba sassauci ko nauyin ganina ya ce "Na gama magana idan baka gamsu ba, ka je ka nemi wanda zai shige maka gaba, babu damuwa, amma fa babu albarkata a ciki". Na shige da sauri, ina ambaton "Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun". Ina shiga gida sallar almuru kawai na gabatar na dauki waya na k'ira kwamishina na ce "Baba ya ce ka turo waliyyainka". Ya dinga murna yana sanya alheri da albarka, tare da addu'ar Allah ya sanya yadda na aminta da shi, kada ya kunya ta a idona. Na ajiye wayar ina mamakin ni kuwa a duniya me na tsare wa Baban Tsakiya ne? Na dinga Jin haushin kaina yadda na makance ina son Jabir! A yau na yarda na gamsu tazarar da take tsakaninmu tamkar tazarar sama da kasa ne . Ba zan ce bana son Yaya J ba, domin kuwa ikon zuciyata ba'a hannuna yake ba. Amma na yarda da maganar Nazira ko shi ka'dai ne namiji a duniya to haramun ne a gare ni. Bayan Baban Marina ya dawo gida bayan sallar isha a tsakar gida Inna ta shimfida masa tabarma a dalilin zafi da ake fama da shi. Ya kammala cin abincin da ta gabatar masa kenan. Ya kalli ni duk da muna da tazara ya ce "Yabi zo nan". Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Na matsa kusa da shi kamar yadda ya yi mini umarni. Babu sukuni ya ce "Ya ya maganar Alhaji?" Kaina a kasa na ce "Na isar da sakon na ka". Ina rufe baki ya ce "Madallah da Yabi! Ubangiji ya tsare ki, ya sanya albarka a dukkan sha'aninki". Farin-ciki ya mamaye ni, na amsa da ameen da karsashi. Ya sallame Ni. Na shiga dakinmu na tarar da Gwaggo tana ta kulla siganta hankali kwance. A zuciyata ina ta jinjina mata na yadda bata raina riba duk kanknatar ta. Domin sigan nan mafi yawa sai ta yi ciko duk sadda za'a auno mata. Idan na ce ta bari, sai ta ce da bata siyar wa, da ba zamu sha yadda muke so ba. A hankali na ce "Sannu da kokari Gwaggo! Allah dai ya nuna mini ranar da zan hutar da ke zaman kullin sigan nan dan kawai mu saka siga a koko ya ji". Ta yi murmushi tana fa'din Yabi da dogon buri kike, dama ana wuce yin sana'a ne? Na ce "Indai bata kawo ku'di ba. Ta yi murmushi ba tare da ta ce komai ba. Na bu'de baki zan yi maganar sai kawai muka ji sallamar Yaya Jabir a tsakar gidan. Baba ya amsa masa tare da cewa "iso mana Jabiru". Ya zauna a tabarmar ya gaishe shi cikin nutsuwa. Baba ya amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa iyali da karatunsa. Tsawon lokaci Yaya J bai iya cewa Baban komai ba. Sai Baban ne ya ce "Akwai matsala ne Jabiru?". Cikin rauni sosai ya ce "Baba so nake ka bani Yabi na aura". Zuciyata ta buga, na yi matu'kar kasa kunne a kansu, ko kwakkwaran motsi bana son yi. Hatta Gwaggo tsaya wa ta yi tana saurare. Murya da walwala Baba ya ce "Jabiru ka zo inda za'a yi maka komai, ina tabbatar maka da a ce a wani wajen kake son auren da na je na nemo maka. Sai dai da yake y'ar tawa ce shiyasa bazan iya komai ba. Kana da siffar da za'a baka aure babu haufi. Amma akwai mishkiloli da baza su bari na baka Yabi ba. Farko matarka da take hannunka itama y'ata ce da kanina ya haifa. Kasan kuma matan yau basu dauki lamarin kishi da sassauci ba. Ha'dasu kishi zai iya ruguza komai ya mayar dasu abokan gaba, sannan zuri'armu zata dare ne, wasu na bawa Yabi kariya, wasu na bawa Maijidda. Da ace Yabi ka fara aura, ka zo kana son Maijidda daga baya to ina tabbatar maka da sai inda karfina ya kare, domin ina da tasirin da zan lank'awasa ta a zauna lafiya. Amma tunda ka riga ka auri Maijidda a farko, dole a ha'kura da maganar Yabi dan a samu a cigaba da lallaba zumuncin da ya dan yi saura." Tsawon lokaci ban ji Yaya J ya ce komai ba tabbacin ba haka ya so ji ba. Murya ba amo ya ce "Baba kai ne tsanin da nake ganin zan taka dan na samu cikar burina." Baba ya numfasa ya ce "Ai kuwa a wannan karon ba zan zame maka tsanin ba Jabiru. Domin ina sane da yadda Mahaifinka bai amince maka ba, ka yi kankanta da yawa ka jefa kanka a cikin manyan matsaloli, domin auren da kake son yi ba zaka samu nutsuwa da shi ba tunda babu albarkar iyaye, sannan su kansu matan naka ba gode wa kokarinka zasu yi ba, kullum zaka zauna ne cikin zullumin zarge zargensu." Yana dasa aya Yaya J ya ce "Zan jure Baba, zan iya, da sannu Ubangiji zai hore mini su gaba'daya. Sannan ina fatan sanadin wannan auren ya zama silar daidaita al'amura a gidan nan". Ga mamakina sai jin muryar Baban Marina na yi cikin kaushi ya ce "Jabiru ba zan baka ba, na rok'e ka, kar ka kuma dosa ta da wannan tatsuniyar domin ko mak'oshina bata je ba, bare ta shiga zuciyata. Bana son na yi maka abin da zaka mini kallon marar kirki, ko na rashin inganta zumunci, amma idan ka cigaba da dagewa to ba shakka zaka sha mamaki, domin kuwa na riga na haramta soyayyarku a zuciyata, dan haka kai ma ka shafe ta domin ba rayayya bace". Bamu gama fita da mamakin maganganun Baba ba, Yaya J ya sake shayar da mu wani sabon mamakin ta hanyar cewa "To Baba idan kuma Allah bai shafe ta ba, ya raya ta fa?" Takaicinsa ya k'ume Baba ya kasa ce masa komai domin bai ta'ba zaton Yaya J zai iya fada masa hakan ba tunda mutum ne mai biyayya, mai kuma gudun zuciya. A sanyaye ya ce "Kowa ya ki fahimtar halin da nake ciki, me yasa zaka biyesu wajen yin watsi da zumunci Baba? Annabi cewa ya yi mu yiwa wanda basu yi mana ba". A matu'kar zafafe Baban Marina ya ce "To dai ni ne uban Yabi! Ni kuma shari'a ta girmama ta mayar a hakku ya za'ba mata miji, idan kuwa hakane, ko mutuwa ce ta riske ni gabannin na aurar da ita da kaina. To waliyyinta baza su baka ita ba, bare kuma ina fatan a ara mini dama na aurar da ita da kaina. Ka je ka yiwa Mahaifinka biyayya, na gode sosai da soyayyarka. Mu cigaba da addu'a da sannu komai zai dai- daita mana. Amma Yabi kam ba matarka ba ce". Tsawon lokaci bai amsa ba. Ni dai daga sama na ji muryarsa yana cewa "Sai da safe Baba". Ajiyar zuciya mai nauyi na ji Gwaggo ta yi tare da cewa "Alhamdulillah! Ubangiji ka sake nisanta

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161