Skip to content

Chapter 112

Chapter 112

Bakar Taada Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ba. Wani k'aramin gida da yake gabanmu ka'dan, Tijjani ya siya. Sabon gini ne, fenti ne kawai ba'a yi ba. Mai gidan ya d'aga gidan xai siyar a dalilin ya samu wnada ya fishi yalea zai siya. Da yamma muka je na ga gidan. Karamin guda ne ainun. Sai dai kuma an tsara shinda kyau. Kafin udan an shiga daga farkon akwai daki mai dauke da band'aki. Wanda tsarinsa yafi dace wa da na maigidan. Daga ciki kuwa k'aramin tsakar gida ne, sai falo mai dauke da dakuna biyu, ko wanne da bandakinsa. A tsakar gidan akwai kicin da kuma wani band'akin daga gefe. Gidan ya sake kawatuwa a dalilin an zuba masa tayal ta ko'ina. Ta bayan dakunan kuma akwai doguwar hanya, bata bille wa, amma dakuna zasu sami iska, sannan za'a iya daura igiyar shanya a wajen. Farin ciki ya mamaye ni. Yau ga ni zan yi d'aki mai dauke da band'aki a cikinsa. Lallai komai lokaci ne. Ya kalle ni da murmushi ya ce "Ya yi miki?" Na bu'de baki na ce "sosai ma kuwa Baban 2. Ubangiji ya k'ara arziki, yasa rabo ne." Da walwala ya ce "Ameen, tunda ya yi miki bari na je wajen dillalan, mu nemi shaidu a je a biya". Na fa'da jikinsa ina jin farin ciki na walagigi da ni. Na dinga jera masa fararen addu'oin da suke sanya shi farin ciki. Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, ciniki ya fa'da ya yi fentin da ba'a yi ba. Ya sayi katifa ya saka a d'akinsa. Dakina kuwa aka shirya kayan gadona bayan an musu kwaskwarima, katifar gadon muka bari a tsohon gidan kafin mu tare. D'akin yaran kuwa aka saka musu katifarsu da ya siya musu yun suna jarirai. Kujera ya canja mini, tawa ta tsufa da yawa, tunda ba mai tsada ba ce dama. Yanzun ma mai L ce amma mai daraja sosai. Aka makala tibinmu a bango shike nan, domin a kicin a saka firij tunda da fili. Gida ya fito ras. Na dan yi siyayyar kayan kicin wanda zan iya. Na sayi kafet da labule kalar kujerar. Muka ja gida muka rufe. Da kansa ya je Bulkachuwa ya taho da Babah da yara. Ta zo ta ga gidan da Ubangiji ya mallakawa Tijjani cikin sau'ki. Ta dinga hawayen farinciki, tare da addu'ar Ubangiji yasa likkafa ta cigaba. A fili ta ce "Da ikon Allah sai kun yi arzikin da kowa sai ya ci arzikinsa. Ina da yakinin Ubangiji ba zai juyar da addu'ar da nake yi muku ba". A ranar ta tafi, duk yadda muka so ta kwana tare da mu, amma fir ta ki. Ta bar yara, tare da zolayata wai gasu nan su mini sati biyu, zata turo Nasiru ya dauke su. Haka ya je Toro ya sanarwa da iyayenmu alherin da ya samemu, tare da basu Ihisani. Mota guda suka taho ganin gidan da su Baban Tsakiya nasu gasgata Tijjani ya siya ba. Tun wuri ya kawo mini kayan miya da nama ya ce "Ki yi abinci da yawa Asiya. Yau mutanan Toro sun taho ganin gidanmu. Nasiba ta ce mini har da Dada". Na dan ji babu da'din yadda ya ce Nasiba ta fa'da masa. To waya suke yi ko kuwa ya ya? Na daure na ha'diye ban tuhume shi ba. Na hau hidimar aikina. Shi kuma ya ri'ke hannun yara suka tafi siyo ruwa da lemo. Na kammala abincin na yi wanka. Ina cikin shiryawa na ji tsayuwar mota, a gaggauce na gama shirina. Na fito ina marabtasu. Na ri'ke hannun Dada ina yi mata maraba ta mussaman. Tuni su Baban Marina, da Baban Tsakiya har da Baban kasuwa suka isa falo. Baba Maryo na cikinsu. Tare da Tijjani muke ta ajiye musu kwanukan abinci da abin sha. Yadda muke shige da fice muna hidimarsu tare, abin ya yi matu'kar burge Dada da Baban Marina. Domin sai addu'ar alheri suke bin mu da ita. Su kuwa ragowar wani irin kallo suke bin mu da shi wanda na rasa gane inda suka dosa. Domin ba wanda ya taya Dada da Baban Marina albarkar da suke sanya mana. Sai da suka ci, suka gyatse. Suka je masallaci suka yi azahar. Sannan muka d'unguma ganin sabon gida. Dada sai hamdala take yi, yau Ubangiji ya gwada mata ta ga gidan mai sunan manya. Baba Maryo kuwa da ta shiga falon ta leka ta ga dakuna biyu, ko wanne da bayi a ciki. Tana bude baki sai ce wa ta yi "Gida kuwa a yalwace. Ban da wuyar zama irin ta y'ay'an yau. Mace biyu ma sai su yi zamansu wata bata takura wata ba. Tunda akwai turakar maigidan". Zuciyata ta yi matu'kar bugawa, domin na fahimci akwai k'ulli a zuciyarta game da ni, tunda muka je biki na ga tana rawar jiki wajen Babah tare da bagarar da ni, nasan akwai abin da take nufi da ni. Maganar da Tijjani ya fa'da mini dazu na ce wa Nasiba ta ce tare da Dada suka taho, ta sake dawo wa ta rib'anya zullumin da na shiga. Na daure ban ce komai ba illah yak'e da nake yi. Gaba'daya Dada da Baban Marina ne suke yin murna ta fisabidillahi a cikinsu. Baban kasuwa da ya bu'de baki sai ce wa ya yi "To Tijjani gida ya yi kyau. Amma ku shiga a hankalinku, ku dinga jin tsoron Allah. Harkar nan ta neman maza ta zama ruwan dare a tsakanin matasa. Kada ku bari manyanku su rude ku su dinga baku kudade kuna b'ata gobenku". Na kalli Tijjani na ga ya yi kasa da kansa yana fa'din"Da ikon Ubangiji zamu kiyaye iyakokon Ubangiji." Zuciyata ta dinga tsallen na mayar masa da martani. Amma idon Baban Marina, da na Tijjani suka mini cikas. Domin na sani dukkansu baza su mini ta da'di ba, idan na yi masa rashin kunya a gabansu. Ban gama jimamin isgilancin Baban kasuwa ba, sai kuwa Baban Tsakiya ya ce "Haka KUMA a kiyaye cin riba, da shiga kungiyar masu daukar bindiga suna kwace wa jama'a rayukansu da dukiyoyinsu suna azurta kansu. Wannan zamani da wuya ya ke." Dada ta ce "Ina addu'a akan duk rintsi kada a jarrabi iyalina da aikata kaba'ira. Ban san me ya hana Baba Maryo sakin nata bakaken ba. Tunda ita ma bata nufinmu da alheri. Shi dai Baban Marina bai ce musu kala kanzil ba. Sai da suka gama. Ya nisa ya ce "Ubangiji ya yiwa neman ka albarka, ya tsare ka, ya baka arzikin halali mai yawa. Ubangiji ya saukar da farinciki a kanka da iyalinka. Allah ya tsareku gaba'daya, ya shirya muku zuri'a." Na daddage da k'arfi na ce "Ameen Babanmu. Ameen dattijon arziki, uban marayu, har masu uban ma.." Baban Marina ya faki idonsu ya galla mini harara. Gane nufinsa ya sanya na ha'diye sauran maganar da na yi nufin zubarwa. Baban Tsakiya ya kalle ni cikin fishi ya ce "Shi ka'dai ne Ubanku?' Da azama na ce "Duk nan ina da uban da ya fika ne Baba? Kai ne ka d'aura mini aure fa". Ya furzar da iskar baki ya ce "Na dauka kin manta saboda kina ganin kun fara shigo wa gari ai" Kan dole na yi shiru. Ban sake ce wa komai ba. Amma

Table of Contents

Chapters

161 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161