Chapter 10
Chapter 10
muka ce zamu shiga shirgin ya'yanka ai sai dai su rufe mu da duka tunda a cikin idonsu muke ganin bakincikin da suke yi da mu, tamkar dai mune muka hanaka ka sake tara arziki, ko muka hanasu yin zuciyar tallafa maka. Ban da lalace wa Musa ka'dai bai isa ya ri'ke kofarka ba? Ya'yanka wajen hudu ko biyar ne a daki amma duk wula'kantattu ne, basa taimaka maka da komai, amma abin kaico sun raina kokarinmu akan ka." Baban Marina ya sunkuyar da kai kasa gwanin tausayi yana fa'din sai ha'kuri da yaran yau, ni kuma har yau din nan basu fiye mini ku ba". Na kalli Nazira na ga hawaye na tsere akan fuskarta, na sake kallon ragowar, su Firdausi kowa idonta a bushe tabbacin basu da kaico akan cin mutuncin da iyayensu suke yiwa ubanmu. Na kasa hawaye a dalilin ba'kin cikin da yake cina yafi gaban hawaye. Ba abu mai ciwo irin wanda ba za'a barka ka keta shi ba, ya tisa iyayenka a gabanka da cin mutunci akan idonka. Na sake kai idona kan Dada da take matsar hawaye, na dinga mamakin yadda ta tara mini jama'a haka. Na gama yarda kafatalin jikokinta ba wacce take jiran kiris akanta iri na. Duk yadda Nasiba take zage wa suna yin sa in sa, hakanan kowa a cikinmu tana mayar mata da magana amma ba wanda take mayar da laifinta garma sai ni. Tausayin mahaifina ya yi matu'kar kama ni ta yadda kannensa suka tsaya a gabansa suke fa'da masa maganganun da komin sanyin halinsa sai sun mintsine shi. Kirjina ya sake nauyi akan wanda ya yi dazu da naga Baban Tsakiya yana cin da'di a kofarsu amma mu muna cin abinci irin na yan fursuna, kuma suna da halin tallafa wa. Amma sun runtse idonsu. Haka Baban Marina ya dinga bawa Dada da sauran y'ay'anta ha'kurin katobarar da na yi tamkar dai shi din ba uwarsa ba ce. Sai lokacin hawaye mai ciwo ya goce mini, ina jin tsanar mutanan da a baki Baffanina ne. Maganar gaskiya kuma na fi jin ciwon Baban kasuwa. Haka suka fice suna kumfar bakin na fitine su, na fitini y'ay'ensu, tunda ba'a sati ba a doku da ni ba a cikin gidan. Rainin da aka yi mana ne ya sanya dukkan mutanan gidan suke ganin zasu mayar da mu gidadawa, shiyasa ni kuma na lashi takobin duk wanda ya nemi ta'ba ni, ko taba wani cikin yan k'ofarmu la shakka ni ya ta'ba domin zan siyi fa'dan ne ya dawo kaina, duk yadda nake yar shafal amma Ubangiji ya hore mini wani irin karfi tamkar shari'a, ko dan da dukkan zuciyata nake yin fa'dan ne oho. Yadda nake tare wa kannena fa'da da muke daki d'aya haka nake tarewa na yaran Inna amaryar Babanmu babu banbanci. Hatta Nazira da take yayata ni nake tare mata fa'da domin duk wanda ya fa'da mata maganar banza zan yi ruwa na yi tsaki na shiga na dinga yarfa bak'ar magana har sai abin ya juye kaina. Duk yadda nake jin haushin Mama bai shafi son da nake yiwa Nazira ba. Domin yar-uwata ce da uba ya ha'damu, idan da abin da na tsana ban kuma yarda da shi ba shine yan'ubanci. Ina matu'kar takaicin yadda wai gidanku daya da mutum, cikinku daya, gadonku daya amma babu yarda da amana a tsakaninku. Duk wani alherinka baka son dan-uba ya ji, zaka iya fa'dawa bare matsalarka amma ban da dan-uwanka da uba daya ya hada ku. Kuma mafi yawa iyaye mata ne suke bari yaransu su shiga cikin rikicin da ba nasu ba. Da ace Nazira tana biye hudubar Mama da tuni ta gurbata mana zumunci da soyayyarmu, mun koma muna adawa da junanmu. Wai uwa ce zaka ji tana zayyane wa y'ay'anta laifin kishiyarta, ko kuma laifin y'a ko d'an da ba nata ba. Da ace iyaye mata zasu dinga ha'diye rikicin kishi a tsakaninsu, suna boye rashin jituwarsu a gaban yaransu, sannan idan matsala ta faru suna barinta a tsakaninsu da an samu sassauci wajen yan ubancin da ake yi a yau. Idan d'an kishiya ya yi miki laifi ko ta yi miki, daure ki ha'diye ba sai kin baza wa yaranki da basu sani ba, gudun haddasa gabar da baki san iyakacinta ba. Ko wanne d'a a duniya gaibu ne, ba wanda yasan me gobe zata zo da shi, ba lallai d'an da kika haifa ya samu daukaka ba, wata'kila sai d'an miji ya samu daukaka fiye da yaranki, adalcin ki ne zai sa Ubangiji ya sarrafa zuciyarsa ya ji k'anki, haka nan ke ma babu jin kunya ko nauyin kin yi abubuwa a baya marasa da'di. Na sani mutanan yau bamu cika gode wa da yaba kokarin abokan zamanmu ba, muhimmi dai mu yi adalci a tsakanin zaman kishi da yaranmu, ko ba a shiri ya zama akwai sassauci da ha'diye bacin rai, shi adalci yana haifar da farin-ciki da yalwar arziki da hadin kai a cikin gida. Addinin musulunci cewa ya yi ko wanne musulmi dan-uwan musulmi ne, bare kuma wanda jini mai k'arfi ya ratsa a tsakaninku. Daga shakiki sai li-Abbi a duniyar musulunci da zumunci amma mutanan yau mun dauki wata irin *Bak'ar Ta'ada* ta mayar da dan-uba abokin gaba kuma makiyi. Da kaina na jinjina wa kaina da duk wacce bata da wannan mummunar manufar a ranta. Madallah da mutanan da suka yarda Ubangiji ne yake zaba mana mutanan da zasu zama iyayenmu da yan'uwanmu. Alhamdulillah, Allah ka bamu ha'kuri da juriya wajen mua'amalantar mutanan da ka d'ora mana hakk'in zumunta da su. *Kafin lokacin zaku iya fara payment ta yadda idan an kammala free pages babu dogon jinkiri.* *Madallah da masoyan RUBUTUNMU*. *Madallah masu sauke hakki komin kankantar sa, madallah da masu k'arfafa guiwarmu*. *Fatan alheri ga masu kiyaye hakkin sana'ar y'anuwansu*. *500 for regular* *1k for VIP* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *ZENITH BANK* ✍️ *BAK'AR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)*. *Marubuciyar* *Halin Yau* *Sabo da kaza*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KO DIYAR DA ZAKI AURAR. TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S ONLY* *Ina makaranta labaran Books ɗin Ayshat Ɗansabo lemu, marubuciyar TAIMIYYAH DA NUFIN ALLAH kai har ma da sauran daɗaɗan littafanta? Marubuciyar na muku albishir da cewa sabon littafinta mai suna ƘADDARAR ZOYA ya fara sauka da zafinsa,labarin ƘADDARAR ZOYA labari ne da ya faru a gaske ba ƙageggen labari bane.Don haka kar ku bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta,labarin zai zo muku akan 500 Whatsapp group sai VIP group on Telegram 1k.Ku tuntuɓi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161